Sashe 58
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba?" Tashi tayi za ta shige bathroom ya fizgota da k'arfi sai da tayi k'ara ta turesa cikin b'acin rai tace "ni ka sake min hannu,ina ruwanka da ni?" Wani kallo ya mata yace "stay still.. Magana za muyi" da muryan kuka tace "ni bazan yi magana da kai ba" sosai yake kallonta da mamaki yace "me yasa baza kiyi magana da ni ba?" Cikin kuka tace "ba dan ka ga za kayi aure shi ne ka daina kula ni ba,kuma ko ganinka ma ba ka bari nayi" yayi still yana kallon yadda take kuka bil'hak'k'i ya zuba mata idanunsa jikinsa duk ya yi sanyi,sanda ya gaji da sauraron kukanta ya kai hannunsa ya mata whipping tears d'in a hankali yace "shhhiii! It's ok.. Kukan ya isa haka" duka ta kai masa a k'irji tace "ni ka kyale ni,kayi tafiyarka ba ruwana da kai" yace "i said ki bari haka,ko kina so muyi fad'a?" Ta girgiza masa kai da sauri,ya matso kusa da ita a hankali yace "Oyah! D'auko hijab muje,idan mun dawo sai ki fad'amin laifin da na miki kika ce baza ki kulaki ba" ta kallesa da sauri tace "ina?" Yace "kin manta?" Ta gyad'a masa kai,yace "kayanku fa a gurin tailor" zaro ido tayi tace "Yaya na manta" yace "ni ban manta ba,maza yi sauri muje" k'aton hijab ta d'auko har k'asa tasa akan riga da wandon uniform d'inta gudun kada ta b'ata masa lokaci suka fito,a hanya suna tafiya shi da ita yace "Uhn! Me ya faru kika ce kin daina kula ni?" Ta zumb'uro masa baki cike da shagwab'a tace "ba ka ce nice babban k'awarka ba?" Yace "yeah!" Tace "to kuma shi ne za ka daina zuwa na ganka?" Yayi shiru yana sakin murmushinsa ta kalleshi fuskarta a tsuke tace "dariya ma kake yi ko?" Yayi saurin had'e fuskarsa ya girgiza mata kai yace "nope! Ba dariya nayi ba" tace "ai na ganka kana yi" ya sake girgiza mata kai yace "no! Ni banyi dariya ba kece dai kika ga kamar na yi dariya" k'wafa tayi ta d'auke kanta,ya d'an kalleta ta gefen idonsa yace "to wai ba shi kenan ba yanzun na zo kin ganni,ko akwai wani abu kuma?" Ta girgiza masa kai,yace "mene ne? Fad'i naji" ta d'aure fuskarta tace "Yaya ni dai ka fasa yin auren nan ka ji?" Saurin kallonta yayi yana tsayawa,ya juyo yana kallonta yace "me yasa?" Tace "ni dai ba na so kayi" d'an murmushi yayi yace "no way Baby" ta tsaya kallonsa cikin jin haushi tace "to ai sai kai tayi,kuma wallahi ba zanje gidan ba" dariya sosai ta bashi yace "saboda me baza ki ba?" Tace "to ba matar ta fini matsayi a gurinka ba,kuma ita ai baka mata rowan ganinka ba sai ni" yace "waye ya fad'a miki haka?" Tace "ai haka ne" ya girgiza mata kansa yana kallonta yace "ba haka bane" kamar za tayi kuka tace "ni dai bazan yarda ba ko me za ka fad'a" duk yadda yaso ya mata bayani k'in saurarensa tayi dole ya hak'ura ya kyaleta ya fita ya karb'o musu kayan ya dawo ya tada motar suka juya gida,har suka k'arasa gidan bata sake masa magana,yayi parking bakin get yace "Uhn!" Ta juya da sauri ta kallesa tace "me yasa ka tsaya a nan?" Yace "magana za muyi" wani had'e rai tayi tace "ni fa bazan yi magana da kai ba" yace "why?" Kai tsaye tace masa "Z" yayi murmushi yace "alright! Duk sanda kika shirya magana da ni ma yi" ya bud'e motar ya fita,ganin ba ta da niyyar fitowa ya lek'a kad'an yace "get down" ta wani had'e ranta tace "me yasa?" Yace "akwai inda zanje" tayi sauri ta kallesa fuskarta a d'aure tace "gurinta za kaje ko?" Yana mata wani kallo k'asa² yace "ehh! Ko kada naje?" Haushi ne ya kuma kamata a fusace ta bud'e motar ta fita,ko rufewa bata tsaya yi ba tayi gaba,yana kiranta ta d'auki kayan bata ko tsaya ba tayi shigewarta ranta duk babu dad'i,ya girgiza kansa cike da farin ciki ya d'auki kayan ya biyota,dai² tana shiga part d'in Dadda taji muryoyi da yawa a parlon ta k'arasa da sauri hango Waleed yana biyota and a time d'in an fara kiran sallah a masjeed,da fuskar Azaan ta fara karo sanda ta shiga ta gwalo idanu so excited tace "Yaya!" Ya mata murmushinsa yace "daga ina kike ne?" Tace "dinki muja je amsowa da Yaya" ya gyad'a kai,cikin wani irin farin cikin ganinsa tayi gurinsa,maganar Mommella da tace "Ohhh! My kid.. Kun dawo?" Da wani irin speed ta kalli inda take tace "Mommella!" Ta fad'a jikinta da sauri tana dariya,Mommella ta rungumeta tana sakin murmushi itama,Waleed ya shigo da kayan yana ganin Mommella ya bud'a idanunsa yana murmusawa yace "sannu da zuwa" ta amsa tana tsokanarsa sai aurensa kawai suka ji lokaci d'aya babu sanarwa,shi dai murmushi kawai yake yi bai ce komai ba,bayan sun gaisa ya mik'awa Azaan hannu suka yi musabaha fuskarsu duka babu yabo bare fallasa,Azaan ya masa fatan alkhairi,jin ana tada sallah ya masa godiya ya tashi da sauri yayi hanyar fita yana kallon Manar,ita kam bata ma san yana yi ba duk ta kwanta jikin Mommella tana mata surutu,da za ta tafi b'angaren mother suka tattara duka suka fice suka bayan sun gama d'ad'd'aga kayan da suka karb'o tare da Waleed. Washe gari dinner Mama ta sa Waleed kama musu guri mafi tsada a event center,tun safe Manar suka fice ita da Ameerah suka tafi gyaran kai da k'unshi,ba su suka dawo ba sai kusan 4pm,lokacin suna shigowa gidan wanka suka fara yi kafin su gama abunda za su yi suka ji ana maganar masu make-up sun zo,cikin sauri suka yi abunds za suyi suka saka kayansu suka fita zuwa gidan su Ameerah,sun shiga lokacin an yiwa Deejah da Diyanah,nan fa shigowarsu yada aka fara neman yin rikici tsakaninsu da su Deejah,da suke cewa sai an gama yiwa k'awayen su,haushi yasa Manar kama hannun Ameerah tace "let's go sis" Ameerah tace "mu jira a fara musun sis" a fusace Manar tace "Allah ba na so,kwalliyan sai kace na zuwa k'iyama" ta fizgeta suka fita cikin fushi,suna fita balcony lokacin har an fara tafiya gurin dinner,Manar sai mita take dai² parking space suka ga Amaar da Azaan suna magana,Azaan da yaga fitowarsu ya kallesu ya dakata da yiwa Amaar magana because lokacin suna shirin tafiya ne suma yace "ya akayi ne Guddi?" Hawaye har sun fara taruwa idanunta da muryar kuka ta kalleshi tace "kawai dan munje a mana make-up shi ne wannan Deejan za su raina mana hankali" d'an murmushi yayi yace "shi ne yasa kike fushi?" Ta gyad'a masa kai,murmushi ya sake yi yace ma Amaar "bro let's take them.. Sai mu k'arasa gurin daga can" Amaar ya gyad'a masa kai yace "okay!" Ya kalli Ameerah yace "a ina ake yi?" Ta fara lissafa masa gurin da ta sani,yace "wanne suka fi iyawa?" Ta fad'a masa,yace "alright! Muje ko" suka fita a motar Amaar,suna tafiya suna hira,Manar dai ta yi shiru haushi ne fal ranta,sai da taga sun tsaya wani make-up and beatification bar,Azaan ya fita motar tare da su suka k'arasa gurin,abunka da aikin kud'i nan da nan aka gama musu,Azaan ya biya suka fito cikin kayansu iri d'aya maroon d'in lace an musu d'auri iri d'aya,tunda suka fito Azaan yake kallon Manar saboda azababben kyaun da tayi ta tsaya jikin mota tana masa murmushi tace "Yaya!" Ya lumshe idanunsa ya bud'e yace "wai da gaske kene kika zama haka?" A shagwab'e tace "me nayi?" Yace "u look prettier" tayi murmushi tace "thank u" back seat suka shiga Ameerah tace "sis wallahi gwanda da bamu tsaya ba,da yanzun ma fa ba'a zo kanmu ba ko,kuma ma ba lallai muyi kyau ba kamar haka" Manar ta harareta tace "ke kika sani" kusan 8:pm suka k'arasa gurin,hall d'in ya mugun cika da mutane kamar ba'a mutuwa,amma kuma hakan bai hana gurin tsaruwa ba kowa yana zaune seat d'insa masu video kam camera ne yake yawo yana d'auka babu wanda yake tsaye,table d'aya suka zauna da su Amaar suna hira da d'aukan pics,tun shigowarsu gurin kallo ya koma sama dan sosai Manar squad suka hargitsawa y'an mata da samari lissafi,gurin ya haska sosai saboda bayyanar su,sanda Mc ya b'ukaci fitowan ango da amarya su Manar fa anje skul an gamu da kilallu wayayyun friends tafiya ma kamar ba ta son takawa suka mik'e ita da Ameerah suka nufi stage d'in,tunda suka shigo gurin idanun Waleed yake kanta,har suka zauna da duk abunda suke yi,seeing her ita da Azaan suna pics abun ya mugun b'ata masa rai dama kuma zaman kawai yake a gurin amma jinsa yake kamar ya zauna a kan k'aya,fuskarsa kamar za ta tsage ya dunga kallonta yana fatan ta d'ago kanta ta kallesa. Sanda suka tashi za suje masa lik'i ita da Amaar da Ameerah dan Azaan kam ya hard'e yace babu inda za shi suje kawai,ya bawa Manar da Ameerah sabon rapper na kud'in lik'i,duk akan idon Waleed suka haura stage d'in lokacin su Deejah duk sun gama rawar k'afansu su masu wa da yake aure sai wani iyayi ake yi suka gama suka sauka,Manar dai sai magana suke da Ameerah suna k'us² suka k'arasa kusa da Waleed da ransa yake a mugun b'ace sai kallonta yake,cikin sa'a ta d'aga kanta ta kalleshi taga ya had'e rai,ta tab'e baki bata k'ara kallonsa ba ta ciro kud'inta za ta masa lik'i,wani kallo ya mata da yasa gabanta fad'uwa ta dunga kallonsa jikinta yana rawa ta kasa d'aga hannunta..