← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 184

Sashe 86

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta bud'e k'ofar parlon su ta shiga gabanta yana fad'uwa,sanda ta tuna abunda Waleed yace wai zai sanar ma Daddy,gaba d'aya ta tashi hankalinta ta hana ma kanta nutsuwa,though ta san ma bazai tab'a fad'a ba kawai dan ya tsorata ta ne ya fad'a mata hakan ta sauke wani ajiyar zuciya a hankali,Mother kad'ai ta tarar a parlon tana zaune da Hafsat a hannunta tana bacci,ta tsuguna a hankali ta gaisheta,Mother tana kallonta tace "how are u feeling?" A hankali tace "I'm feeling better" mother tace "Allah ya k'ara lafiya,have u taken ur drugs?" Kai ta gyad'a mata a hankali tace "ehh" ta gyad'a kai tace "alright! But me ya fito dake yanzu da daren nan?" A sanyaye kwalla tana kawowa idanunta tace "a nan zan kwana" daga haka ta mik'e ta nufi d'akinta,mother bata ce komai ba ta bita da kallo,tana shiga d'akinta ta cire hijab d'inta ta haye kan gadon gabanta har lokacin bai daina fad'uwa ba,ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta kunna wayarta za ta cire daga flight mode,taga already ma ba'a kai yake ba kawai dai wayar yana silent,tana kallon screen d'in taga turutun missed calls da message guda kusan biyar,call log ta fara shiga taga kiran Azaan ne mafi yawa daga ciki sai wasu na Waleed,tayi wani ajiyar zuciya har ranta taji sanyi dan ko fuskarta ma sai da ya nuna tace "yau Yaya ya cire ni daga blacklist" ganin few minutes ago ya kirata,na Azaan ne dai tun yamma,ta bud'e text d'in tana dubawa taga duk sak'on nuna damuwa ne da rashin jinta daga Azaan,sai wani guda d'aya da ta gani daga Waleed,sanda ta bud'e kamar idanuwanta za su fad'o tsabar mamakin kalaman da ta gani ya rubuta mata,ta maimaita text d'in ya fi a k'irga,can kamar za tayi kuka ta ajiye wayar tana hararta,almost ten minutes tana zaune ta yi shiru tana tunani sai kuma ta d'auko wayar ta masa reply tana tura masa ta kashe wayar gaba d'aya tana sakin murmushi,ta mik'e ta shiga bathroom tayi wanka ta canja pad d'in jikinta ta d'auro alwala ta fito bayan ta gama shirin bacci ta kashe wutar d'akin ta haye gadon taja bargo ta rufe half d'in jikinta. Washe gari ya kasance Monday sosai ta ji sauk'i hakan yasa tayi shirin zuwa school da safe,tana cikin k'arasa assignment da bata samu ta yi ba sai lokacin,taga wayarta dake saman study table d'inta ya yi haske,k'arasawa tayi ta d'auki wayar taga text d'in friend d'inta Nusy ne ya shigo tana requesting tayi online yanzu za su yi magana,tayi mata reply da cewa su had'u skul kawai yanzu za ta shigo,ta ajiye wayar ta d'auki backpack d'inta na makaranta ta fita daga d'akin,ta yiwa mother sallama ta fita gidan,a hankali take tafiya kamar tana counting steps d'inta,ta k'arasa parking space lokacin duk sauran yaran gidan sun fito suka shiga motarsu driver yaja suka wuce skul,suna kan hanya Ameerah take tambayarta "sis ya jikinki?" Tace "da sauk'i" Ameerah tace "Allah k'ara lafiya,kin yi assignment kuwa?" Ta gyad'a mata kai tace "sure" suna ta hira tsakaninsu har driver ya sauke su get d'in makaranta ya juya,tun shigarsu premises d'in makarantar ta hango Nusy tsaye a jikin window ta zubawa hanya ido,tayi d'an murmurshi suka k'arasa class lokacin few mutane ne suka zo,can k'arshen class suka koma da Nusy wanda idanunta suka nuna damuwa k'arara,tace "sis kin san me ya faru?" Manar ta girgirza mata kai tace "nope!" Nusy tace "i want an advice from u" Manar ta zaro ido tace "ni kuma?" Nusy ta gyad'a mata kai idanunta sunyi rau²,a hankali tace "okay! Allah sa zan iya,what happened?" Nusy tace "wani cousin d'ina ke sona ni kuma banji ina sonsa ba gaskiya,yanzu ga shi ya fad'awa Daddy na,har ya basa damar zuwa wai mu had'a kanmu" zaro ido Manar tayi kamar eye ball d'inta za su fad'o tace "nima fa ban gaya maku bane kawai amma abunda yake shirin faruwa da ni kenan" here ta sanar musu kaf alak'arta da Waleed da kuma tsakaninta da Azaan,kallonta Nusy ta dunga yi kafin tace "to ke wa kike so a cikin su?" Manar tace "ni dai Yaya Azaan nake so" Nusy tace "shi kuma Yaya Waleed fa?" Manar tace "shima ai ina sonsa,amma Yaya yana auren k'anwarsa ne?" Kafin Nusy tayi magana,kawai sai ji suka yi Ameerah dake zaune tare da su ta fashe da wani dariya,suka kalleta tare Manar tace "mene abun dariya ke kuma?" Tana had'e rai,Ameerah tayi mai isarta kafin ta tsaya tace "kun san me ya faru?" Suka ce "a'a" suna had'a baki,Ameerah ta kalli Nusy tace "kefa na ki duk mai sauk'i ne,tunda ba ki da wanda kike so,why not baza ki amshi cousin d'in naki ba? Yana da wani aibu ne da baki so?" Nusy ta girgiza mata kai tace "nope! Ba shi fa da wani matsala nice dai kawai banji ina sonsa ba" itama ta sanar musu irin shak'uwar da suka yi da Abdoul d'in,Ameerah ta dunga b'ab'b'aka musu dariya,sai da taga duk sunji haushinta kafin tace "ba fa sonsa ne ba kya yi ba kema,kawai dai dan bai tab'a zuwa miki da irin maganar nan bane shisa kike ganin kamar ba kya sonsa" ta kalli Manar tana sakin wani murmurshi tace "sis nifa na jima ina zargin Yaya yana sonki kawai bai tab'a fad'a miki bane" kallonta Manar ta yi da sauri tace "wa yace maki haka?" Tace "i just sit and think" wani murmurshi Manar tayi tace "to ni dai Allah ina da wanda nake so" Ameerah ta fara dariya tace "shi kuma Yayan fa?" Manar ta d'aure fuskarta tace "shi ai Yaya na ne,besides kuma yana da mata,nima aure na zanyi" ta k'are maganar tana murgud'a baki,wani dariya Ameerah ta sake fashewa da shi tace "wait please.. Kina nufin ba kya sonsa wai?" Manar ta gyad'a mata kai tana b'ata rai,Ameerah tace "but idan ba kya sonsa me yasa ranar da kika ce ya yi kissing d'inki baki ji haushi ba? And me yasa kike zuwa jikinsa? Kina tunanin zuciyarki ba ta sonsa ne?" Manar ta sake gyad'a mata kai,wani kallo Ameerah ta mata tace "Wallahi k'arya kike yi kice ba kya sonsa na yarda,kawai dai akwai wani abu tsakaninki da shi da yasa kika kasa fahimtarsa,but billah Yaya yana sonki,so ba na wasa ba.." Wani kallo Manar ta dunga yi ma Ameerah idanunta sun cicciko da hawaye a fusace tace "ni dai ba shi nake so ba,kuma ai kema kin sani" Ameerah tace "ai ke na jima da raina tunaninki,har yanzun baki san meye kalmar so ya k'unsa ba,ki samu lokaci kiyi tunanin maganata maybe ki iya fahimtar wanda zuciyarki take so.." Dai² nan teacher su na physics ya shigo,suka koma seat d'insu. K'arfe hud'u sun fito school tare da Nusy suna sake tattaunawa kan maganar da suka fara da safen,Nusy ta hango cousin d'inta da take bawa su Manar labarinsa tsaye jikin motarsa ya rungume hannu idanunsa sanye da glasses,sosai gabanta ya fad'i ta bud'a idanunta tana kallonsa,a hankali ta tab'a Manar tace "friend kin ga Yaah Abdoul can tsaye,wanda nake baku labari" Manar ta d'an waiga suka had'a ido da shi yana sakin lallausan murmurshi,a hankali tace "kai friend yanzu meye laifin wannan guy d'in ke kuwa?" Ameerah tace "barta dai tayi wasa,tana zaune za taga wata ta kawo masa tallan kanta" wani kallo Nusy tayi ma Aneerah mai kama da harara,Ameerah ta fashe da dariya tace "ai gaskiya na fad'a kike hararata" d'an murmurshi Nusy tayi tace "muje ku gaisa" suka k'arasa inda yake tsaye,Manar tace "ina wuni" ya gyad'a kai yace "lafiya lau k'awarmu ya skul?" Tace "alhamdulillah" suka gaisa a mutunce,Nusy ta gabatar masa da su as manyan friends d'inta da ba ta da kamarsu,sai murmurshi yake musu har da basu sak'on su kular masa da ita ya basu amana,and su tayasa campaign,suka yi dariya then suka yi musu sallama saboda driver da yazo d'aukan su,daga haka ya zaga ya bud'e mata ta shiga ya rufe,then ya zagaya mazaunin driver ya shiga ya tada motar suka wuce. Manar tana dawowa skul that same day taga miss call d'in Azaan,kasa kiransa tayi da farko don bata san me zata ce masa ba,can dai tayi dialing number a hankali ta kai kunne,wayar yana fara ring ya katse ya kirata,tayi gathering courage tayi picking,murya can k'asa² tayi masa sallama ya amsa yace "why are u ignoring my calls?" Zaro idanunta tayi a shagwab'e tace "nooo! Yaya ba fa ina sane nayi haka ba,ba na kusa da wayar ne,na bama Hjy ajiya tun ranar Saturday" yace "okay! I thought u where ignoring it shi sa ma ban zo ba da daren munyi hira,ya jikin?" Ta langwab'ar da kai a shagwab'e tace "na ji sauk'i" yace "maa sha Allah" shiru ya biyo baya can tace "me yasa to baka zo ba da ban picking call d'in ba?" Yace "me yasa zan zo?" Turo baki tayi tak'i cewa komai,yayi murmushi dan ya fahimci me tayi yace "i'll call u idan na sauka flight d'inmu zai tashi" wani zaro idanu tayi cikin damuwa tace "tafiya kayi baka bari na dawo ba?" Yayi murmushi yace "yeah! There's something important da ya sa ni tafiya ban miki sallama ba,but zan dawo soon saboda qur'anic grad d'inki" fuskarta a d'aure ta amsa masa ba don ta so ba,da ya fahimci ta ji haushi yace "I'm sorry Guddi na ce fa zan dawo" kuka ta fashe da shi ta katse wayar,ya dunga kiranta tana kallo ta k'i d'auka,ya tura mata text shima dai bata yi masa reply ba. Tun daga ranar da ya tafi bata k'ara kiransa ba,sai dai shi ya kirata,ko chat ma kafin tayi masa magana sai shi ya fara mata,tsakaninta da Waleed kuwa tun ranar da ya mareta bata k'ara saka shi a idanunta ba,gaba d'aya ya yiwa gidan yaji. Ranan thursday da yamma sun taso islamiyya lokacin saura 2 day's saukarsu,suna zaune parlon Dadda suna ta shirin sauka Waleed ya shigo,ta d'aga kai ta kallesa ta b'ata rai,ya zauna kan kujera suka gaisa da Dadda dake ba su sak'o gurin aminiyarta Tasallah,bayan sun gama karb'an aiken Manar ta kalli Dadda tayi k'asa da muryarta tace "Hjy ko za kice Yaya ya kaimu please,driver ba ya nan wai" wani
Chapter 86 · 0% Book details