Sashe 87
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kallo Waleed ya mata saboda ya ji me take cewa yace "i'm not a driver of anyone,kuje ku samu napep ya kaiku" Dadda ta kallesa ta marairaice murya tace "hava kai kuwa Mamman,ka taimaka ka kai min su mana,sa fi dawowa da wuri ma akan idan motar kasuwa suka shiga" mik'ewa yayi saurin yi ya d'auki keys d'insa zai fita fuskarsa a d'aure yace "sai su jira driver ya dawo ya kaisu,ni ba hanyar zanyi ba bare ki sani na rage musu hanya" yayi ficewarsa ya bar Dadda da bud'ad'd'en baki,cikin jin haushi kamar jira take yana barin parlon ta fara mita "jeka d'an kwal uba,idan ka kaisu baka haifu cikin Asama'u ba.. Da wasu shegun mitsil² d'in leb'unansa da suka zurma ciki,tsabar tsotson masifa,tun kana k'wailiyinka dama ba mutunci kake da shi ba.. Ni ce dai za ka dawo ka tarar da ni ai.." Dariya Ameerah da Manar suka kwashe da shi har da kwanciya,can Manar tayi saurin tashi tace "ina zuwa bari naje naga idan Yaa Amaar yana nan ya kaimu" ta fita da sauri,ta sauka k'asan balcony taji an fizgota,ta waiga a tsorace taga Waleed ne,tayi ajiyar zuciya fuskarta a d'aure tace "Yaya ka sake ni aike na Hjy tayi fa" kallonta ya dunga yi ganin yadda tayi ya lumshe idanunsa a hankali yace "ke me yasa idan kina son abu baza ki iya fad'a ba sai dai kice Hjy ta fad'a min?" Da sauri ta kallesa,ya d'aga mata girorinsa,ta d'auke kanta tace "to ba dai ka ce baza ka kaimu ba kuma" yana kallon lips d'inta da suka sha red chapstick hancinta da ring shaped d'inta,nan da nan ya d'aure fuskarsa yace "ban hanaki saka abubuwan nan kina fita da su ba?" Rau² idnunta suka yi da ta gane akan abunda yake magana tace "Yaya.." A fusace yace keep quite.. Ban ce kada na sake ganinki da su ba?" Hawaye suna saukowa fuskarta tace "bazan sake ba" ya saketa yace "oyah! Ku fito muje" da sauri ta juya tana goge hawayenta,ya bita da kallo har ta shige part d'in,yayi ajiyar zuciya,bata jima ba sosai suka fito da Ameerah,can parking space ta hangoshi yana zaune cikin motarsa,suka k'arasa ta bud'e front seat ta shiga Ameerah ta shiga back,ya tada motar suka bar gidan,suna tafiya a hanya motar ya yi shiru,Waleed ya kalleta yace "u two should tell me abunda kuke buk'ata na saukan ku,though ba'asa ni ba na tambaya yanzun" Dariya Ameerah tayi tace "ehheeenn! Yaya muna komawa gida dama zan maka list" ya kallota ta mirror yace "alright!" Hakimar kam ko tari bata yi ba har suka je gidan Tasallah suka kai mata sak'on Dadda,suna fitowa gidan Ameerah ta klleta tace "sis ko za kice Yaya ya kaimu gidan su Nusy mu kai mata card?" Manar tace "tabb' d'i kina kallon yanzu ma fa abunda yayi kafin ya kawo mu" Ameerah tace "please ki gwada kiji ko zai yarda" suna zuwa Manar ta shiga motar ya kalleta yace "gulmar me kuke yi?" Manar ta kalli Ameerah itama ta kalleta da sauri Ameerah tace "babu komai" yace "really?" Ta gyad'a masa kai,ya tab'e baki yace "kada kiyi zaton ban jiku ba" ta zaro ido tace "Yaya ba fa wani abu muka ce ba" yace "ko?" Ta gyad'a masa kai,strictly yace "a ina ne gidan da za ku yake?" Wani zaro ido tayi tace "Yaya dama ka ji?" Ya kalleta ta mirror yace "a'a kin san ai ni kurma ne" tayi murmushi ta fad'a masa,ya gyad'a kai ya tada motar suka bar unguwar su Baba Tasallah. Sanda ya kaisu GRA da gidansu Nusy yake,kafin su fita motar ya musu warning kada su b'ata masa lokaci,suka fita suna amsawa,they spent about 30 minutes a ciki,Waleed yaga ba su da niyyar fitowa,ya fito motar ya jingina yana kiran line Manar,tana ganin kiransa ta kalli Ameerah ta mik'e tsaye tace "Yaya ne yake kira kizo mu wuce kafin ya fara fad'a" Ameerah ta mik'e tana kallon Nusy dake sakin wani murmushi tace "wane Yayan ne?" Ameerah tace "Yaya Waleed" Nusy ta kalli Manar tace "is he our love?" Kafin Manar ta bata amsa ya sake kira,gabanta har fad'uwa yayi,Nusy tace "ki d'auka mana kuma kike kallon wayar" a sanyaye ta d'auka kafin tayi magana yace "It's past six now sai yaushe za ku fito?" Wani sanyayan ajiyar zuciya tayi jin ba da fad'a ya tambayeta ba tace "yanzu za mu fito" bai sake magana ba ya katse wayar,ta kalli Ameerah tana sauke ajiyar zuciya tace "thought fa zai balbale ni da fad'a,muje kada ya k'ara kira ma" suka fita d'akin Nusy,after sun yiwa Mummy'nta sallama ta musu murnan saukar da za suyi tace "it's better ku yiwa friend d'inku fad'a ta k'i shiga islamiyya ku ga shi har za kuyi sauka" Manar tayi dariya tace "in sha Allah Mom za muyi mata" after then suka fita Nusy ta rakasu har gurin mota suka gaisa da Waleed,then suka yi sallama da su tana d'aga musu hannu tace "sai mun had'u skul gobe" Waleed ya ja motar suka tafi,suna kan hanyarsu na komawa gida kira ya shigo wayar Manar,ta kalli screen d'in ganin Azaan ne yake kiranta,ta Dd'an kalli Waleed kafin ta d'auka ta kai wayar kunnenta,a hankali tayi sallama,wani kallon gefen idanu Waleed ya mata bata kula ba kawai sai ji tayi ya k'ure kid'an dake tashi a motar,tayi saurin kallonsa za tayi magana taga ya d'aure fuskarsa,a hankali ta kai wayar dai² bakinta tace "Yaya zan kira ka idan na sauka" ta katse wayar,suna isa line ya tsaya few houses away,Manar ta kallesa tace "Yaya.." wani kallo ya mata yace "get down" ransa a b'ace,Ameerah tana ganin haka ta bud'e motar ta sauka,Manar kam k'in fita tayi,sai kallonsa take tana mamakin abunda ya b'ata masa rai cikin few minutes,ya kwantar da kansa a hankali jikin seat d'in ya kulle idanunsa yana jin wani irin damuwa yana lullub'esa a hankali yace "fita nace" sunkuyar da kai tayi gabanta yana fad'uwa,tsoronta d'aya kada ace ita ta b'ato masa rai,a hankali tana kallonsa tace "Yaya" bai kalleta ba yace "please jeki zan zo gidan" kuka ne ya kusa kwace mata ta daure duk da cracking da voice d'inta yake tace "I'm sorry Yaya" murmushin takaici yayi kafin a hankali yace "kin san kin yi min laifi kenan?" Ta girgiza masa kai gabanta yana kara fad'uwa,ya d'ago idanunsa da suka d'an birkice saboda ransa da ya sosu yace "i just sit down and think ya kamata ace na kyaleki,but i just can't.. Why na kasa cire son wanda ba ta so na?" Sunkuyar da kai tayi gabanta bai daina fad'uwa ba,a hankali ya kamo hannunta yana kallonta yace "me yasa ba kya so na Manar?" Girgiza masa kai tayi hawaye sun cika mata idanu tace "ina sonka Yaya.. Amma.." A hankali yace "but baza ki iya aure na ba,right?" Tana jinsa ta kasa d'ago kai ta kallesa zuciyarta sai bugawa yake Wanda ta rasa dalilin faruwarsa,bata ankara ba tan can duniyar tunani sai ji tayi ya had'e bakinsu ta kulle idanuwanta da k'arfi,tana jin yanda yake kissing d'inta passionately ta kasa dakatar da shi because she never experience such thing sai a gurinsa,bata san yaushe ya kai hannunsa cikin hijab d'inta ba sai dai taji yana squeezing breast d'inta,yana fitar da wani irin moan jikinsa kuma was vibrating,da yake glass d'in is tinted kuma duk a ride suke,sanda taji yana sauke seat d'in da take a tsorace ta fara turasa baya,tunda take bata tab'a tsorata da moment d'insu ba kamar yau,it was something that had never came to her mind,ko kad'an bata kawo cewar shi da yake mata fad'an ta rabu da Azaan saboda wani dalilin da ya kawo mata zai yi k'ok'arin aikata haka ba,hawaye sai sauka idonta suke ya k'i sakinta,ta fara sheshshek'ar kuka tana ci gaba da turasa,a tsorace ya saketa zuciyarsa tana bugawa,ya koma seat d'insa ya zauna hankalinsa a mugun tashe da wani breaking voice yace "i.. I'm so sorry Manar,it's not intentional haka ya faru" ja baya tayi tana masa wani kallo cike da tsoro ta bud'e motar ta fice da sauri,yana kallon sanda take gudu ta nufi get ya mayar da kansa baya wasu irin hawaye suna zubowa idanunsa,a hankali come da rud'anin abunda yayi mata ya furta "I'm so sorry.." Tana shiga gidan da Azaan ta fara karo,ko kula ma bata yi ba ta bugesa za ta shige part d'insu ya rik'ota da sauri ganin tana kuka,hankalinsa ya mugun tashi,a rikice yake tambayarta "Guddi what happened?" Kasa amsa masa tayi sai sheshshek'ar kuka take tana nuna masa hanyar get da ta baro,ya rik'e shoulders d'inta biyu yace "relax kiyi min bayani" k'irjinta yana d'agawa tsabar tsoron da take ciki da kyar ta iya gathering words d'in bakinta tace "Yaya ne" sai ta sake fashewa da kuka,ya zuba mata idanunsa yace "me ya samesa?" Tana k'ara gudun kukanta ta girgiza masa kai,ya dunga kallonta yace "please be quiet!" Ta sassauta kukan,yace "uhn! What happened to him?" Da muryar kuka tace "babu abunda ya samesa" wani irin ajiyar zuciya yayi kafin yace "ke d'in me aka miki kike kuka?" Wasu hawaye taji suna neman zubo mata ta sake cewa "Yaya ne.." Again kuma ta k'ara fashewa da kuka,Azaan dai ya zubawa sarautar Allah idanu yace "me ya had'aki da shi?" Lips d'inta da not too long Waleed ya gama tsotsewa ta shafo,kawai ta sake kecewa da kuka da gudu ta bar gurin,direct tana shiga part d'insu ta wuce d'akinta ta kulle k'ofa ta fashe da wani sabon kuka..