← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 184

Sashe 80

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bai dawo ba" k'ofa ya nufa Afiyah ta mik'e ta bi bayansa,Aunty ta bi ta da kallo har suka fita,ta girgirza kai ta mik'e ta tafi ta ci gaba da abunda take,suna fita Waleed ya kalleta fuskarsa a d'aure yace "abunda kika yi kin kyauta kenan? She's my Mom too amma ki kasa gaishe ta?" Tsayawa tayi tana kallonsa with suspicion tace "me nayi kuma?" Yace "did u greet her?" A fusace tace "kai komai mutum yayi sai ka yi k'orafi,ba sai kayi correcting d'ina ba cikin lalama,gaba sai na gyara,amma ka fara min fad'a daga zuwanmu" juyawa kawai yayi ba tare da ya ce mata komai ba ya ci gaba da tafiya ta bisa a baya tana tab'e baki,part d'in su Manar taga zai shiga ta masa wani kallo ta tsaya tace "nan ne part d'in Hjyr?" Ya juya ya mata wani kallo yace "part d'in uncle d'ina" bai jira cewarta ba ya shiga parlon da sallama,d'an tsaki tayi kafin ta shiga,Mother tana zaune a parlon tana ganinsu tayi musu sannu da zuwa da fara'arta,Waleed ya zauna ya gaisheta ta amsa tace "sannun ku da zuwa" Afiyah dai kallo d'aya tayi ma Mother ta wani d'aure fuska tana kallon TV,Mother ma tun da ta kalleta sau d'aya taga ba ta da niyyar gaisheta bata sake kallonta ba,ta tafi kitchen tana cewa "bari in kawo muku ruwa" wani kallo Waleed ya dunga yima Afiyah da ta bud'e jaka ta d'auko phone tana operating,murya can k'asa yace "did u greet her?" Tayi masa banza tana danne²nta,Mother ta fito ta ajiye musu ruwa da drink saman couch dake kusa da shi,yana k'irk'iran murmushi yace "Mother daga gida fa muke" ta zauna saman kujeran da ta tashi before then tace "drink d'in kawai?" Ta d'auki bottle d'aya ta bud'e ta tsiyaya masa cikin cup,ya d'auka ya sha yace "Daddy yana Lagos ne?" Mother tace "a'a yana Abuja yanzun" yace "alright! Za mu je gaida Hjy" tace "toh sai kun fito,na gode k'warai" mik'ewa yayi ya nufi k'ofa Afiyah tabi bayansa,mother ta bi ta da kallo,sai da suka fita balcony ya juya yana kallonta kafin yayi magana,ta wucesa da sauri tana d'aure fuska,ya gyad'a kansa ya nufi hanyar part d'in Dadda,Dadda tana share parlonta taji footsteps ta d'aga kai tana kallonsa tace "waye wannan kuma?" Bai tanka ta ba ya cire takalminsa ya shiga parlon,Afiyah tana k'irk'irar murmushi tace "sannu da aiki Hjy,shara kike yi ne?" Dadda tace "wallahi fa wannan yaran suka shigo min suka b'ata,suka fice suka barni kuma" Afiyah tayi murmushi tace "kawo na taya ki" Dadda tace "a'a bar shi kiyi wucewar ki ciki,daga zuwa kuma sai ki hau shara?" Afiyah tace "don Allah ki kawo na k'arasa miki" mik'a mata tsintsiyar Dadda tayi ta karb'i jakar hannunta da mayafi tace "ai kuwa na gode,dama dan dai wancan matar tana kwance d'aki ne na san da tuni ta sharesa tsaf,to tun jiya take fad'amin ba ta jin dad'i,ashe kuwa da gaske take na d'auka ma wasa take min sai d'azun kawai ciwon ya kwantar da ita,dad'in ta ma na san abunda ke damunta,shi sa ban wani tada hankalina ba,Allah dai ya yaye mata wannan bala'a'en ciwon mara,abu dai yak'i ci yak'i cinyewa shekara da shekaru sai fama take.." Kallonta Waleed ya dunga yi kafin ya kalli k'ofar d'akin da yake tsammanin tana ciki ba tare da ya ce komai ba,Afiyah ta gama share parlon ta kwashe dattin da parker ta mik'e tana murmushi tana kallon Dadda tace "ina zan zubar da sharan?" Dadda tace "kina fita akwai kwandon shara yana nan za ki gansa daga gefe" Afiyah tana fita daga parlon Waleed ya kalli Dadda yace "me ya sameta?" Dadda dake k'ok'arin zaunawa tace "wai Manar?" Yace "ehhh" tace "to hailarta ne dai ina jin zai zo,idan ba haka ba dama me zaisa ta ciwo ita kuwa,ai lafiyayya Maryam ta haifeta dama,d'azu ta gama sharb'an kukanta a nan,babu inda bata zagaya ba a gidan nan,to nace ta tafi gidansu ko uwarta za ta kaita kyamis ta k'i ya zanyi da ita?" Mik'ewa yayi da sauri,Dadda tace "ka rufa min asiri kar kaje ka tasheta na samu ta yi bacci da kyar,d'azu wannan d'an albarkan dake neman aurenta ya aiko d'an fodiyo da wani likita ya dubata ya taho da magunguna da allurai.." Tsayawa Waleed yayi yana kallonta,Afiyah ta shigo parlon ta zauna k'asan rug tace "ina wuni Hjy?" Dadda tana murmushi tace "lafiya lau 'yar nan,ya hanya kuma? Kin dai yi kyau wallahi,zama wancan k'asa na su Hafsatu ya karb'eku,ince dai ko har kin samo mana tsaraban ciki a can ba'ayi zuwan banza ba?" Sunkuyar da kai Afiyah tayi tana ta k'irk'irar murmushin k'arfin hali kirjinta sai dukan you take yi,Waleed zai shiga d'akin da Manar take Dadda tayi saurin kallonsa tace "yau na bonu ni jikar laraba,ai fa Allah kuma ya dawo da kai,yanzu zan shiga uku da yawan sa ni magana.. Waleed na ce kar kaje ka tasheta,wallahi alluran da aka mata yasa ta samu bacci,ya zan yi da raina idan ka tasheta yanzu fisabilillahi?" Bai tsaya saurarenta ba ya shiga d'akin,Afiyah ta kalli Dadda da sauri tace "waye ba lafiya?" Dadda tace "wallahi Manar ce,kamar bazata yi rai ba d'azu,na ce kar yaje ya tasheta amma ya k'i saurarata,jibi dai duk ya rikice daga zancen Manar babu lafiya.." Mik'ewa Afiyah tayi da sauri tace "Ya salaam.. Bari naje na dubata" daga haka tabi bayansa zuwa cikin d'akin,sanda ya shiga tsayawa kawai yayi akan Manar dake bacci yana kallonta,yanda ta k'ara girma jikinta ko ina was full da kayan alatu har wani special ajiyar zuciya yake saukewa yana k'are mata kallo,bacci take sosai kamar babu abunda yake damunta,ta yi wani fresh ga kyaun da ta k'ara da d'an k'ibar da tayi kad'an,ya zauna gefenta a kan gadon idanunsa akanta,then ya kai hannunsa forehead d'inta yana kallon fuskarta,ta bud'e idonta a hankali ta sauke su kansa,lokaci d'aya gabanta yayi mugun fad'uwa ta dunga kallonsa tana ganin kamar cikin nightmares da ya saba mata gizo ne,zai yi magana Afiyah ta shigo d'akin kamar an cillota,ganinsa kusa da Manar ta rik'e kugu tana kallonsu,Manar tana ganinta ta zaro ido it was there ta tabbatar ba mafarkin da ta saba yi bane,Waleed ya yi mamakin ganin Afiyah ta biyosa but bai nuna mata komai ba ya d'auke kansa daga kallonta,Manar tayi sauri ta mik'e zaune ta d'aure fuskarta tana tab'a mararta da taji ya d'aure,Waleed yana kallonta murya can k'asa yace "wane maganin kika sha?" Medications d'in da Amaar ya shigo mata da su bayan Dr ya dubata ya tafi ta nuna masa,ya d'auko ledan ya ciro drugs d'in yana kallonta yace "waye ya kawo miki?" Shiru tayi ta k'i cewa komai,ya had'e rai yace "i'm asking u" ta turo baki ta koma ta kwanta,Afiyah dai sai kallonsu take rik'e da kugu,Dadda ma ta biyo bayansu har d'akin tana kallon Afiyah tace "Safiyah kike ko?" Afiyah tayi murmushi tace "a'a Afiyah ne Hjy" Dadda ta kyab'e baki tace "to koma dai wa kike,ke kuwa idan kin dubata ai sai ki d'an koma daga parlor ki jira su gama,ko kuma kije gurin Asama'u ya sameki a can" Afiyah dai bata ce komai ba sai murmushin yak'en da take yi tana sunkuyar da kai,kamar an tambayeta Dadda tace "ai babu wani abu dake jikin Manar wanda Mamman bai sani ba in fad'a maki,yanda kika san y'ar uwarta mace haka ta d'aukesa tun tana mitsitsiyarta,ko ina ne taji ciwo kwailayewa take ta nuna masa ba ta jin kunyarsa ko d'is.." Juyawa Afiyah tayi saurin yi ta nufi k'ofa ta fice saboda wani bak'in cikin da maganar Dadda ya saukar mata,Dadda ta bi bayanta tana waigen Manar tace "sannu Manar.. Tunda Allah ya sa ga Mamman nan ya zo sai ki zage ki nuna masa inda ke maki ciwon,karki b'oye ki sanar masa kinji ya duba ki tsaf.. Nan da anjima sai kiga kinyi ras kamar baki tab'a ciwon ba,kinga dai yanzu ba gidan yake ba,kada sai ya tafi ciwon ya dawo maki mu rasa yanda za muyi kuma" d'an murmushi Waleed yayi har Dadda ta fita,can ya d'aure fuskarsa yana kallon Manar yace "kiran saurayin naki kika yi kika ce masa baki da lafiya ko me?" Kamar za ta yi kuka tace "nifa ban kirasa ba Yaya" fuskarsa a d'aure yace "toh wa ya kirasa?" A hankali tace "kira na yayi a waya bai sameni ba shi ne ya kira Ameerah" yana mata wani kallo yace "k'arya kike idan baki ce ta kirasa ta fad'a masa ba za ta kirasa?" Kamar za tayi kuka tace "nifa Yaya ba ni da lafiya lokacin ban san me tace ba" ya k'ara had'e rai yace "shine sai tace masa kina period ko?" Zaro ido tayi tace "Yaya ni fa ban ce ta fad'a ba Hjy ce ta fad'a masa nima kuma sai da naji kunya da tace haka" tana magana tana turo baki,yace "wa yayi miki alluran kuma?" Tayi shiru ta k'i cewa komai,ya mata tsawa yace "answer me now" turo baki tayi tace "Dr da suka zo tare da Yaa Amaar ne yayi min" kallon ta ya dunga yi yana jin zuciyarsa tana masa zafi,a hankali ta d'ago tana kallonsa,ganin yanda ya d'aure fuska ba shiri ta sake shiga nutsuwarta,strictly yace "shi k'aton kika bud'e ma jikinki ya miki allura yana kallon ki?" Dariya maganarsa ya ba ta sai dai babu halin yi,tana komawa baya a hankali tace "nifa ban bud'e masa ba a haka nace yayi min akan skirt d'ina,kuma bari ma kagani har jini ya b'atan pant" tana fad'in haka ta janye skirt d'in jikinta a hankali tana nuna masa saman buttocks d'inta,a hankali ya sauke idonsa yana kallon fresh skin d'in bayanta,lokaci d'aya yaji ransa yayi wani mugun b'aci zuciyarsa tana tafarfasa,tayi murmushi ta rufe gurin tace "ka gani ko?" Fuskarsa a tamke yace "when za ku fara exams?" Ta bud'a manyan idanunta tace "remain 3 months fa" yace "good ana gama saukan ku dama kice za kije gidana kiyi hutu" ta zaro ido tace "saboda me Yaya?" A tsawace yace "don't question me,umarni na baki" daga haka ya mik'e ya nufi k'ofa ransa a mugu b'ace,ta bi sa da wani kallo mai kama da harara Dan dama haushinsa take mugun ji ya yi
Chapter 80 · 0% Book details