← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 184

Sashe 84

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

dawo toh" ya d'an had'e rai yace "and if u deny me i won't be happy" bai tsaya jiran abunda za tace ba ya fara tafiya yace "u have to expect the call anytime right from here,maybe tommorow i might leave in sha Allah" da kallo ta bisa har yayi nisa kafin ta juya a sanyaye ta koma part d'in Dadda. After salatul isha'a tana zaune d'aki ta gama shan drugs d'inta Ameerah ta fita ba jimawa taje kiran da Aunty tayi mata,ta gama shirin bacci kenan za ta kwanta ta tuna wayarta yana flight mode tun jiya,and kuma Azaan ya ce zai kirata da yamman,sauka tayi da sauri ta saka hijab ta fito parlor,ta san ma k'ila yana ta kiranta wayar ba ya shiga,Dadda dake zaune parlon tana cin naman da Amaar ya shigo mata da shi da fura,tana ganin ta fito ta zuba mata ido har ta k'araso tace "Hjy ina wayata?" Dadda dake kai nama bakinta tace "sai dai ki shiga d'akin ki d'aukosa yana nan cikin kwalla na adana maki ita,ni dai yanzu kinga bazan tashi ba,idan za ki jira kuma har na gama to sai na d'auko maki" wucewa Manar tayi da sauri ta nufi d'akin Dadda,bata ma saurari maganar da Daddan take mata ba ta bar parlon,ta d'auko ta fito daga d'akin taga mutum ya shigo daga nesa ta hango kamar Amaar kamar kuma Waleed,duk da babu jimawa taji Amaar d'in ya shigo ya fita,tsayawa tayi har sai da ya k'araso ciki tana ganin Waleed ta turo baki ta juya da sauri ta koma d'aki,Dadda data gama cin namanta ta shiga kitchen kai plate d'in ta fito,taga shigar Manar d'aki ta bita da kallo tace "kinga wayar ko naje na d'auko maki?" Manar da har ta shige ta jiyota tace "na gansa fa" Dadda tace "toh ai shi kenan tunda ma kin ga inda yake har kin d'auko" har za ta wuce ganin Waleed ta bisa da wani kallo tace "yau nake ganin abu.. Yanzu ka tafi gidan naka ka sake dawowa,kai kenan baza ka barmu mu sarara ba kuma Mamman,kullum kai ta mana sintiri a gida,ba d'azu da rana kuka zo ba? Me kuma ya sake dawo da kai,ko ka yi mantuwa ne ka dawo d'auka?" Bai ce mata k'ala ba ya nufi k'ofar d'akin da Manar take ya bud'e,ta dunga kallonsa ta kasa dakatar da shi,Manar tana ganin ya shigo ta koma k'arshen gado tana kallonsa idanunta sunyi rau² kad'an take jira ta fashe da kuka,fuskarsa a mugun d'aure yana mata wani kallo yace "u had better keep on running away from me because billah kika bari na kamaki za kiji mamikina.. I'm promising u this,i'll seriously deal with u" a fusace Dadda data biyo bayansa tace "ai yau kuma na gama shiga uku ni dai tunda Allah ya sa ka dawo,da dai bakina alaikum babu ruwana da d'aga murya duk gari ana jina,don Allah Mamman kana yiwa Allah da manzonsa ka rufa mana asiri ka kama hanya ka tafi gidanka haka nan sai kuma Allah ya kaimu gobe,me yarinya ta maka kake k'unduma mata zagi haka,yarinyar da kamar baza tayi rai ba d'azu,Allah ya rufa mana asiri wancan yaro Mamman da ya zo ya aiko likita ya dubata tsaf ya mata allura ya bata magani taji sauk'i,shine yanzu daga farfad'owarta za ka zo kana zaginta ta uwa ta uba kana nuna ta da yatsa kana yab'a mata mugayen kalamai irin wad'annan,to ni dai gaskiya ka tafi ka ba mu waje kafin ma na kai k'aranka wajen Yaro ya d'aukar min ashshin akanka,yo ni na tab'a jin inda aka aurar da mutum kuma yayi ta sintirin zuwa gida kullum babu k'ak'k'autawa,to ni dai gaskiya dama na gaji da zuwan da kake min kana sa ni magana,tunda ka yi aure kayi zamanka a gidanka ka barmu haka nan muma mu sarara.." Bai tsaya bin ta kanta ba ya kulle k'ofar d'akin ta ciki,Dadda ta fasa ihu tana kwala masa kira iya k'arfinta,babu wanda zai ce ba wani mugun abun ta ga yana yi ba,Manar tana ganinsa ta sake tsorata ta tashi za ta shige bathroom ya fizgota,ji tayi kawai an wanka mata mari,ta dafe cheek d'inta a firgice,Dadda sai dukan k'ofar take tana kiransa tana masa magiyan ya fito kada ya yima Manar komai,da taga ba shi da niyyar fitowa ta juya da gudu ta fita gidan tana ratatun neman agaji,Waleed yana kallon Manar da idanunsa da suka kad'a cikin masifa yace "muharraminki ne shi da za ki bari ya rik'e maki hannu? Wato kema kin zama budurwa kin fara tsayawa da samari,shi sa kika bashi fuskan tab'aki ko? Kin barsa ya tsaya dake a kusa² kamar zai rungumeki,ke kuma kina bud'e masa hak'orinki saboda ba ki da wayo,billah kada ki bari raina ya b'aci akan ki,idan kika yi wasa zan miki mugun duka kafin na sanar da Daddy'nki abunda yake faruwa" rik'osa tayi saurin yi hawaye duk sun wanke mata fuska ta fara bashi hak'uri tana cewa "Yaya don Allah kayi hak'uri wallahi bazan k'ara ba,don Allah kayi hak'uri kada ka fad'awa Daddy" sosai ransa ya b'aci zuciyarsa har tafarfasa take tsabar kishin dake cin ransa,hawaye suna k'ara zubowa fuskarta tace "don Allah Yaya kayi hak'uri,wallahi bazan sake ba ka ji?" Ta fada lokacin da take fad'awa jikinsa ta cukuikuyesa tana kuka mai sosa zuciya,har ransa yake jin kukanta,bai san lokacin da ya jawota jikinsa ba cikin sanyin murya yace "That's very wrong Manar,every guy da za kiga yana zuwa gurinki,ba komai suke yiwa ba sai jikinki.. Idan kina sakewa da su haka,suna samun abunda ya kawosu za su rabu dake,ko shi da kika saki jiki da shi he is..." Sai kuma yayi shiru bai k'arasa ba,dan yadda zuciyarsa take tafasa kamar ana had'a masa wuta cikinta,Manar kam sai kuka take a hankali ta kasa ce masa komai,ko kad'an bata yarda da abunda yake fad'a ba,dan ita tafi kowa sanin waye Azaan,da yana da niyyar yi mata wani abu tuni ya jima da cika burinsa akanta tun ma bata kai haka ba,ko da ma ace d'an iska ne kamar yadda Waleed yake k'ok'arin fad'a mata,ko yaya da ya nuna mata halinsa tun ba'a zo yanzun ba,ita ta sani he only loves her,kamar yadda itama take sonsa,bayan wannan kuma babu wani abu da take hange in between,hannunsa ya kai ya d'ago fuskarta yana kallon eyeballs d'inta da ya canja colour,muryasa a k'asa yace "for my sake Manar ki rabu da shi kinji k'anwata?" Fashewa da kuka ta sake yi cikin wani breaking voice tace "I love him Yaya,and aure fa za muyi da shi kake cewa na rabu da shi.." Kallonta Waleed ya dunga yi ya kasa k'iftawa,zuciyarsa banda bugawa babu abunda take cike da tashin hankali,ganin ya kasa yi mata magana da kyar ta tattara words d'in da suka rage mata,cike da k'arfin hali tace "I'm sorry Yayana,believe me ina sonsa da gaske,but i promise u bazan bari ya sake rik'e hannuna ba sai mun yi aure.." Saurin sakinta Waleed yayi ya koma baya yana mata wani kallo mai cike da rud'ani,lokaci d'aya ya juya ya nufi k'ofa ya fita,ta bi sa da kallo tana share hawayen dake zubowa daga idanunta,a hankali ta koma ta zauna a bakin gado tana sauke ajiyar zuciya,ko minti biyar ba'ayi ba da fitar Waleed daga gidan Dadda ta dawo d'akin tace "tashi muje Yaro yana son ganinki yaji laifin da kika yiwa mutumin can,yau dai in sha Allahu in munyi sa'a ya yi mana iyaka da shi,ina murna ya yi aure,zan rabu da saka ni maganar da yake zuwa yi,ya ce shegiyar tukuna ma da duk ban sa ki magana ba" kallonta Manar tayi saurin yi tace "ni dai wallahi babu inda zanje,haka kawai ke kamar an saka ki daga abu ya faru sai kice za ki kaiwa Abba k'ara,naga dai bai min komai ba,ni ce ma na masa laifi d'azun shi sa,kuma na ma basa hak'uri" sakin baki Dadda tayi tana kallonta,Manar ta mik'e ta nufi k'ofa tana cewa "ke komai akayi sai ki d'auka kije ki sanarwa Abba,baza ki jira kiji abunda ya faru ba" daga haka ta fice daga d'akin tana zumb'uro baki ta bar Dadda a tsaye sororo ta fice ta bar mata gidan ma gaba d'aya because she knew idan ta zauna yau mitar da Dadda za ta mata kan abunda tayi ko bacci ba lallai ta barta tayi ba..
Chapter 84 · 0% Book details