← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 184

Sashe 40

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yazo muje tare" da sauri Ameerah ta tsayar da dariyarta tace "ni dai kinga babu ruwa na,idan ya dawo kuma wallahi kada kice masa nice na fad'a miki sun je makarantar mu" a fusace Dadda tace "to uwata ba sai ki hana na gaya masa ba" Ameerah dai kamar za tayi kuka ta dunga kallon Dadda ta san tsaf sai ta fad'a tunda tace haka,da sauri ta juya ta bar gidan ranta duk a jagule,wasa² tun Dadda tana sa rai da ganinsu har ta fara cirewa,hankalinta gaba d'aya yana kan k'ofar shigowa duk taji motsi ta baza idanu tana jira taga waye zai shigo idan taga ba su bane sai tayi tsaki,su kansu masu shigan suna ganin haka ba sa zama suke ficewa,after maghreb ta idar da sallah ta tashi a fusace ta fita gidan,tana tafe tana mita sanda ta isa k'ofar gidan bata tsaya kwankwasawa ba ta hankad'a musu k'ofar da k'arfi,Aunty dake zaune parlour ta d'aga kanta taga waye Allah ya so bata yi magana ba ta ga Dadda tana shigowa,ta tashi da sauri tana fad'in "sannu da zuwa Hjy" fuskar Dadda a tsuke tace "Fatima wai ni kam nace kin san inda gantalallen yaron can ya d'auke yarinyar nan suka je?" Aunty girgiza kai tace "Hjy ba dai basu dawo ba har yanzun?" Cikin fad'a Dadda tace "ina fa suka dawo,ni dai da ya dawo min da ita ma hankali na duk ba zai tashi ba,kawai kuma daga na yi masa shiru shi kenan sai yak'i dawo min da ita har yanzu" cikin nuna jimami Aunty tace "gaskiya bai kyauta ba,amma bari na kirasa muji suna ina" Dadda tace "yi sauri dan Allah,ni idan ma bazai dawo ba,to ya dawo min da ita gaskiya" kiran line Waleed Aunty tayi ya d'auka yace "hello Aunty!" Aunty tace "Waleed ina kuka je har yanzu baku dawo ba?" Yayi murmushi ya kalli Manar dake gefensa yace "muna hanyar gida Aunty,yanzun za mu k'araso" ajiyar zuciya tayi tace "alright! Sai kun dawo" ta kashe wayar,idanun Dadda akanta tace "me yace miki kuma?" Aunty tace "suna hanya yace min" Dadda ta gyad'a kai tace "Allah sa da gaske yake" suna cikin maganar Mama ta sakko daga sana ganinta yasa su yin shiru,Dadda ta tashi da sauri tana tsuke fuska tace ma Aunty "to ni dai na tafi,idan sun dawo su same ni can gidan" Aunty ta amsa tace "sai da safe Hjy" Dadda dai tuni ta yi gaba bata tsaya amsawa ba,Mama ta bita da kallo tana tab'e baki,Aunty ma dai bata kalleta ba ta d'auke kanta,ganin babu fuska yasa ta neman guri ta zauna. Sanda suka shigo gidan kowa haushin kowa yake ji,yana yin parking ta bud'e ta fita da sauri ya kalleta yace "waye yaronki da za ki fita ki barma kayanki?" Ta juya ta kalleshi bata dawo ba tayi wucewarta b'angaren Dadda tana k'unk'uni,k'wafa yayi ya bud'e ya fito ya bud'e back seat ya d'auko kayan ya bita da su,yana shiga yaga Dadda a tsaye bai kulata ba ya ajiye kayan ya juya zai fita,a fusace Dadda tace "kai dai wannan mutumi ba ka da hali ko d'is" a fusace ya juya ya kalleta fuskarsa a d'aure yace "na yi miki wani abu?" Fuskarta a tsuke tace "da ka d'auketa ka tafi gantali da ita gidan wace uwar ka kai min ita?" Wani kallo ya mata ya juya yana tafiya yace "ina ruwanki?" Kamar za tayi kuka ta dunga kallonsa har ya kai k'ofa ta d'aga murya tace "ka fad'awa uwarka Asama'u" k'wafa yayi ya wuce ya fita,yana barin apartment d'in ta juya ta shiga d'akin,a tsaye ta ga Manar tana cire kaya sai b'ata rai take,ta bita da kallo tace "kema da yake ja'irar kanki ce ina maki magana kika barni tsaye saboda ga gantalalliya" d'auke kai Manar tayi tak'i kulata ta shige bathroom,haushin rashin maganar da bata yi mata ba yasa Dadda yin k'wafa mai ciwo ta fita. Da safe Ameerah ta fito daga wanka ta tarar Manar bata tashi ba,ta k'arasa da sauri ta d'aka mata duka,Manar ta tashi a tsorace tana sosa gurin,Ameerah tace "dallah ki tashi ke baki san za mu makara ba idan kika ci gaba da baccin?" Manar tace "kuma sai ki dake ni?" Ameerah tace "ni dai ki tashi ki shirya kafin Yaya ya shigo" jin ta ambaci Waleed da sauri ta tashi ta shiga wanka,ta fito ta shirya Ameerah tana tayata,suna gamawa ganin yadda uniform d'in suka mata kyau yasa Ameerah tayi mata pictures suka yi wasu tare then suka fito,Dadda ta d'aga kanta ta dunga kallonsu duk da ta ga kyaun da kayan suka yiwa Manar amma fushin da take yasa bata ce musu komai ba ta mik'e ta fara goge²,Ameerah ta tab'a Manar ta nuna mata Dadda,tab'e baki tayi tana tafiya tace "ina kwana?" Dadda bata kulata ba ta ci gaba da aikinta,Ameerah da neman tsokana tace "Hjy Dadda ana gaisheki" juyowa Dadda tayi a fusace tace "bazan amsa ba" Ameerah ta kyalkyale da dariya ta rik'e hannun Manar da sauri suka fita apartment,Dadda ta bisu da harara tace "kuma ba zance a dawo lafiyan ba" Manar da har sunje balcony ta jiyota ta dawo ta tsaya bakin k'ofa tace "dama waye yace ki kulasa?" Dadda ta juya fuskarta a tsuke tace "nima bazan kula ki ba d'in" Ameerah dai sai dariya take musu da kyar ta janye Manar suka bar gurin,suna tafiya Ameerah ta kalli Manar tace "sis idan munje skul kada ki yi dariya ki kama ajinki ko a class kada ki dunga kula mutane sosai" Manar tace "me yasa?" Da baki Ameerah ta nuna mata su Deejah dake tsaye parking space suna kallonsu tace "saboda wancan" Manar ta kalli inda Ameerah take nuna mata ta tab'e baki,suka k'arasa Deejah da Diyanah sai cika suke,Manar ta d'auke kanta bata kulasu ba suka tsaya jiran driver,ko a mota da suka tafi k'ala bata ce ba har suka je skul,duk yadda su Diyanah suke yar musu magana Ameerah ma bata yarda ta kulasu ba suka musu banza. Sanda suka shiga class gaba d'aya idanun y'an class d'in suka yo kan Manar ta d'aure fuskarta ta k'i dariya a dole sai ta nuna itama tana da aji,sosai bata manta abunda Ameerah tace ba,Ameerah ta rik'e hannunta suka je gurin zamanta suka zauna,wata k'awar Ameerah Nusaiba dake zama bayan seat d'inta tayi murmushi ta mik'awa Ameerah hannu suka gaisa,then Manar da tak'i ko da murmushi,ranar gaba d'aya babu abunda Manar ta gane saboda turancin da teachers d'in suke yi,duk malamin da ya shigo ba ya musu Hausa,shisa har aka tashi cikin k'unci take,da suka dawo gida ma driver yana yin parking ta fice a fusace ta nufi part d'in Dadda,Ameerah ta biyota tana mata dariya saboda ta san matsalarta,itace ma da taga abun ya yi yawa taita rarrashinta tana cewa za ta saba,za ta iya itama idan ta mayar da hankali,Manar a gaba Ameerah tana binta suna shiga Manar tayi cilli da jakarta ta saki kuka,Dadda ta fito kamar an cillota tana ganin Manar tsaya tana kallonta tace "ke kuma lafiyarki za ki shigoma mutane da kuka?" Ameerah dake k'ok'arin zama tace "nima tun d'azu muke yi da ita a skul" Dadda ta kalleta tace "mene ne kuma wani zuk'ul?" Ameerah ta fashe da dariyar da bata yi niyya ba tace ''makaranta fa nake nufi" Dadda ta tsuke fuska tace "shi makarantar ne dan kinibibi baza'a fad'a yadda kowa ya sani ba?" Ameerah dai sai dariya take,Manar ta tashi a fusace ta share hawaye ta nufi d'aki tana cewa "ni wallahi ba zan sake zuwa ba daga yau" Ameerah ta mik'e da sauri tace "wallahi ba ruwa na ke da Yaya" a fusace Dadda tace "ai kuwa tunda ba ta so ba ta sake zuwa shegen makarantar nan,dama shiru nayiwa Yaro ko da yake sanar min zai mayar da ita makarantar yahudawa nan" Ameerah ta zaro idanu tace "ke dai Dadda Allah babu ruwanki ita da Yaya idan yaji" Dadda cikin masifa tace "yaji mana,zai zare mata rai ne?" Ameerah ta fizgi jakarta da sauri ta shige ta barta sai mita take,tana shiga d'akin taga Manar duk ta yi watsi da uniform d'in,ta zauna bakin gado sai kumburi take,ta k'arasa ta tsince mata kayan ta ajiye saman gado,a fusace Manar ta sake watsi dasu k'asa tana hararanta,Ameerah ta sake tattarawa tana kallon Manar tace "sis kada kiyi fushi please!" Kamar jira Manar take ta kulata ta sake fashewa da kuka,Ameerah ta zauna kusa da ita tayi tagumi ta zuba mata ido,can da ta gaji ta mik'e da sauri bata kulata ba ta d'auko wayarta a cikin press da suke b'oyewa,ta dawo ta zauna kusa da ita ta fara kiran Azaan,ba'ayi taking long ba ya katse ya kirata,ta d'auka tana sauke ajiyar zuciya tace "Yaah Azaan ina wuni?" Yayi murmushi yace "lafiya lou Ameerah ya gida da su Aunty?" Tace "suna lafiya" yace "Dadi fa?" Tace "itama haka" Manar dake gefenta tana jin ta ambaci sunan Azaan ta tsayar da kukan,cikin sanyi murya Ameerah tace "Yaah Azaan u know what?" Yace "nope! Sai kin fad'a" ta d'ago a hankali za tayi magana suka had'a ido da Manar da ta kafeta da idanu,harararta tayi da sauri ta tashi daga kusa da ita,Azaan yace "ina baby fa?" Tace "ka ganta nan mun dawo skul wai baza ta sake zuwa ba" yace "saboda mene ne?" Tace "wai kawai dan malaman suna yin turanci ita bata ganewa shi ne tace baza ta sake zuwa ba" murmushi Azaan yayi yace "kyale ni da ita zan kirata yanzun naji matsalarta" Ameerah ta gyad'a kai tace "Allah Yaya kada ka biye mata,ita kullum sai ta dunga biyewa Dadda,bata san ita ce take cutuwa ba,ko fa islamiyya ma bata zuwa,komai aka ce mata sai tace bata iya ba" Azaan ya gyad'a kai yace "alright! Bari na kirata yanzun" Ameerah tayi ajiyar zuciya tace "toh!" Suka yi sallama suka ajiye wayar,ko minti biyu ba'ayi ba ya kira Manar through video,ta kalli wayar da Ameerah ta ajiye mata ta kai hannu ta d'auka sai b'ata rai take..
Chapter 40 · 0% Book details