← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 184

Sashe 145

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Since that day da ta koma gidan kullum idan ya fita,ba ya iya wuni a office ba tare da ya dawo ba,and a rana idan zaiyi zuwa goma kafin ya koma sai ya san yanda ya ribaceta,within short period of time da dawowarta sun manta da kowa da komai,gida ma rabonta da zuwa tun da suka dawo ga shi ana maganar 3 month,idan kaga Manar a lokacin zato za kayi ba ita bace,saboda yanda ta k'ara kyau skin d'inta ya yi wani mugun fresh,ass d'inta kuwa yanda suka k'ara zama wide za ka rantse ta yi haihuwa uku ko sama da haka,kullum tana gida tare da shi,idan ba ya nan ma suna mak'ale a waya,family house kuwa ko sau d'aya bata tab'a masa zancen suje ba ganin yanda ta dad'e a can kafin su dawo,ranan wani Friday da yamma guraren 6pm ya dawo daga aiki ya sameta a parlor a kwance sai juye² take a kan rug,ya k'arasa yana kallonta murmushi kwance a fuskarsa,he just thought ko wasa take masa da farkon,ya kalleta ko bra babu a jikinta yayi d'an murmushin jin dad'i yayi sallama,da kyar ta iya amsawa bata d'ago ba har sannan tace "sannu da zuwa" still yayi yana kallonta,because ya saba yana shigowa zaiji ta d'ane jikinsa tana dariya,idan ta fara kissing d'insa kuwa idan ba shi ya tsayar da itaba sai ya kaisu ga bawa gado hakkinsa,ya kalleta da kyau yana tsugunawa kusa da ita in a way style yace "heyy! Lilac" tace "Mmm" yace "are u okay?" Girgiza masa kai tayi,ya tallafo kanta yana kallonta yace "what wrong? Mmmm?" Tana yatsina fuska tace "i don't know what to say.. Kawai ba na jin dad'i,ina jin kamar ba ni da lafiya,or rashin lafiya na son kamani" yace "since when?" Tace "bayan tafiyarka" d'an jimm yayi yana k'ara tsaneta da idanunsa yace "will u help and explain ina kike jin ciwo?" Da kyar ta bud'a idanunta tana kallonsa sai kuma tayi saurin kullewa tana girgiza masa kai tace "i'm feeling dizzy,a haka ma jiri nake gani,komai juyawa yake yi" ya d'an bud'a idanu yana kallonta yace "sorry!" Zaki iya tashi ko na d'aukeki?" A hankali tace "bazan iya ba fa" yace "okay! Sannu" yayi maganar yana shafa kanta,can yayi d'an murmushi yace "bari na kaiki bedroom,maybe idan kin huta zuwa anjima ki dawo normal" tace "Allah yasa" yace "ameen" ya d'auketa ya nufi sama da ita yana mata sannu,sanda ya kwantar da ita saman bed,ya zauna gefenta yana shafa kanta,a haka wani irin wahalallen bacci ya d'auketa,can guraren maghreb a time d'in ana kiran sallah ya zo da niyyar tashinta yaji jikinta da zafi sosai,hankalinsa a d'an tashe ya kirata,a hankali ta d'an bud'a idanuwanta lokacin sunyi wani iri alamun da gaske rashin lafiya ke damunta,yace "sannu!" D'an lumshe masa idanuwa tayi,yace "tashi muje nasa miki ruwa a jikinki ur temperature is getting high.." Girgiza masa kai tayi,yace "what?" Yana kallonta sosai,ta bud'e baki za ta masa magana taji bakinta ya cika da yawu,da sauri ta fara k'ok'arin sauka,yace "ina za kije?" Bathroom ta nuna masa da sauri ta shige sanda ta zubar ta wanke bakinta then ta d'aura alwala ta juyo za ta fito ta gansa tsaye a door way yana kallonta,ta taho a hankali idanuwanta har lumshewa suke yi,sanda tazo wucesa jiri ya fara k'ok'arin kayar da ita,da sauri ya rik'ota ta fad'a jikinsa,yana kallonta da kyau yace "har yanzu jirin kike gani?" Kasa amsa masa tayi kawai ta fashe da kuka,ya d'aukota ya dawo da ita kan gado ya ajiyeta ya matsa gaban press ya d'auko mata hijab ya shimfid'a mata pray mat then ya d'auketa ya ajiyeta kai yace "yi sallah bari nayi wanka nazo muje hospital" da kai ta amsa masa,ya goge mata hawaye yace "stop shading those tears,u will be fine okay?" Then ya tashi ya shiga bathroom yayi wanka a gaggauce ya fito ya tarar da ita tana sallah a zaune,wani tausayinta ya dunga ji,ya wuce ya d'auko jallabiyya milk color da skinny jeans sai sleeveless ya shirya ya feshe jikinsa da turarukansa masu dad'i,ya shimfid'a wani pray mat d'in ya kabbarta sallah,sanda ya idar ya juya ya ganta a kwance idanuwanta a lumshe,ya matsa kusa da ita ya kai hannunsa goshinta ya tab'a,a hankali ta bud'a idanuwanta ya dunga kallonta da kyau,can yace "open ur mouth please ki fito min da harshenki" kallonsa ta tsaya yi sai da ya sake maimaita mata then tayi abunda yace ya kai hannunsa ya d'an bud'a idanuwanta,then ya d'agota da kyau ya rik'o hannunta yana duba nails d'inta,d'an gyad'a kai yayi yana sakin murmushi yace "za ki iya daurewa muje hospital?" A hankali ta gyad'a masa kai hawaye cike a idonta,yace "sannu!" Ta sake gyad'a masa kai,ya mik'e ya d'auki car key d'insa then ya dawo ya dauketa ya fita,sanda suka fito daga gidan get keeper yana musu addu'ar Allah ya tsare,Waleed ya amsa ya d'auki hanyar hospital d'insu,tun suna hanya ya yiwa Dr Mahfouz waya,sanda ya d'auka yace "Dr ba dai har ka fita ba?" Waleed yace "yeah! Na je gida na tarar madam babu lafiya,so kana hospital ne na kawota ka k'ara dubata,i'm suspecting something,but ina son kamin confirming ne" Dr Mahfouz yayi murmushi yace "okay! No problem ina office sai kun shigo" suka ajiye wayar ya juya yana kallon Manar da lokaci d'aya ta zama wata quite ya mata sannu,ita dai sai kallon hanya take tana jin zuciyarta tana tashi,har dai suka shiga hospital ya fito ya sake d'aukarta suka k'arasa office d'in Dr Mahfouz,yayi knocking door d'in,daga ciki Dr Mahfouz yace "yes come in" Waleed ya tura k'ofar yayi sallama,Dr Mahfouz yace "ohh! Thought wani ne ba kaiba,kai da za ka shigo ka tsaya knocked?" Waleed yayi d'an murmushi yace "noo! Thought kana wani aikin shisa bamu fara shigowa ba" Dr Mahfouz yace "bismillah!" Ya nuna musu gurin zama,yana kallon Manar yace "Madam barka dai ya gida?" Da kyar ta iya amsawa,then suka gaisa da shi,yace "meke faruwa ne Dr?" Waleed yace "so kake na k'ara maimaitawa kenan bayan na fad'a maka kafin muzo?" Dr Mahfouz yayi murmushi yace "yeah! Ina so ka maimaita min naji,so sai musan me ya kamata muyu" Waleed yayi murmushi yace "i just suspect ta samu shigar ciki ne,so ina son kamin confirming if it's true" Dr Mahfouz yayi dariya yace "tsakani da Allah kai yanzu d'an wannan aikin shi ne ya kawoku?" Waleed yace "yeah! Idan ni nayi ba lallai na gamsu lokaci d'aya ba" Dr Mahfouz yayi dariya yace "alright! bari na kira sister Amina ta d'auki jininta" Waleed yace "alright!" Dr Mahfouz ya mata sannu ya fita,not too long suka shigo da wata nurse kyakykyawa,tana ganin Waleed tayi d'an murmushi tace "Dr ina wuni?" Ya amsa idanunsa akan Manar,Dr Mahfouz yace "ki d'auki jininta da sauri ki kai lab,ina son result d'in yanzu" ta amsa tana kallon Manar tace "sannu Madam" Manar dai babu baki,sanda ya rik'eta kafin ta bari aka ja jininta,duk ta k'ank'amesa ta cusa fuskarta a jikinsa wai ba ta son ganin jininta da aka d'iba,Dr Mahfouz dai sai dariya yake musu ganin dramansu,Nurse d'in da ta d'auki jinin sai dariya take yi itama tace "haba sister kada ki bada mu a gabansu,kina gani har sun fara mana dariya" Manar ta d'ago kanta fuskarta duk gumi kamar wanda aka sha kokawa da ita tace "idan na bada ku wata rana zan karb'o ku" Waleed ya dunga kallonta jin bakinta cakwai har ta iya bada amsa,yace "oooohhh! Ashe dai bakinki bai mutu ba har yanzu" wani kallo tayi masa tace "tou kai ya ka gani da?" Ya gyad'a kai yace "yanzu fa sai da na d'aukeki tafiya kasa yi kike" tace "tou ai dai ba da baki ake tafiya ba,kafafuna sunyi min nauyi ne da kaina" ya gyad'a kai yace "okay! Idan za mu tafi ai kya tafi da kanki kuma" wani marairaice fuska tayi tace "kai Yaya yanzu sai ka barni na tafi da kaina? Idan na fad'i kuma fa?" Yace "ke kika sani kuma" basu wani jima sosai suna jira ba Nurse d'in ta kawowa Dr Mahfouz result,Dr Mahfouz ya karb'a yayi mata godiya,ta fita tana yiwa su Manar sallama suka amsa,tana fita Dr Mahfouz ya warware takardan yana duba content dake zane,wani murmushi yayi ya mik'awa Waleed paper yace "congratulations Dr" Waleed yayi wani kyakykyawan murmushi yace "thanks friend" ya karb'i result d'in yana dubawa,tun bai gama karantawa ba ya gano tana d'auke da ciki na 8 weeks,yayi wani k'ayataccen murmushi yana kallonta da wani yanayin farin ciki mara misali yace "alhamdulillahillaziiy bii ni'imatihi tatimmussalihaat" ya rik'o hannunta da kyau yace "u are once again pregnant.." Bud'a idanuwanta tayi tana kallonsa sai kuma murmushi ya sub'uce mata mai tafe da hawaye,za ta fara masa kuka ya d'agota yace "this is not the time for cry.. Godiya za muyiwa Allah ya mayar mana abunda muka rasa a baya" ta dunga gyad'a masa kai hawaye suna sauka cheeks d'inta,Dr Mahfouz dai sai kallonsu yake ba k'aramin burgesa suke ba,suka tashi tafiya Waleed sai godiya yake masa ya rakosu har bakin mota yana tsokanarsu kafin suka masa sallama suka wuce,a hanya suna tafiya yana kallonta cike da so da nuna kulawa yace "what do u want to eat? Ko ba kya jin sha'awar komai?" Tayi shiru kamar tana tunani,can ta hango apples a jere gurin masu siyarwa anyi packaging d'insu a wani kamar kwando k'arami,ta dunga kallon apples d'in,yanda taji ranta ya biya har ji take idan bata ci ba za'a iya samun matsala da sauri tace "zanci apples" ya kalleta yana sakin murmushi yace "apples ma ba apple ba?" Ta gyad'a masa kai tace "please ka karb'o min ni dai" yace "an gama madam" yayi parking gefen hanya ya fita yaje gurin masu siyarwan ya siya mata kusan package 3 suka saka masa a leda,ya karb'a bayan ya biya kud'in ya k'arasa mota ya bud'e yana kallonta ya mik'a mata ledar itama har saurin kawo hannu take ta karb'a,ta bud'e ta d'auko biyu ta d'auki bottle water dake kusa da ita ta sauke glass ta wanke,yana kallonta ta fara ci ko kallonsa bata kuma yi ba sai da ta kusa cinye d'aya ta juya ta kallesa taga ita yake kallo,tayi masa murmushi tace "na san maka ne za
Chapter 145 · 0% Book details