← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 184

Sashe 176

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da akayi knocking kafin ta jiyo muryar Deejah na cewa "sis Manar kizo Alhassan na kuka" a hankali Manar tayi ajiyar zuciya then tace "alright! I'm coming" Waleed dake kallon yanda ta tsorata yayi murmushi yana kai hannunsa k'irjinta zai tab'a tayi saurin bige masa hannu tace "ni wallahi ka kyale ni,yanzu sai ka sa na manta da su na shashance a nan" dariya yayi yace "to ba ni ya kamata dama afi bawa kulawa ba?" Juyawa tayi tana masa wani kallo tace "kou?" Ya d'aga mata gira yace "yes! Ba ni na biya sadakina ba?" Wani kallo ta masa tace "a'a banda rinto,su Abba suka biya maka dai" gwalo idanunsa yayi yace "whatever! Amma da suna na aka biya,right?" Ta k'ara tab'e baki sanda ta sauka daga gadon ta nufi bathroom tace "umm! Wannan dai zan iya yarda,shima bayan ka gama zurfin cikinka suka ga dai bari su taimaka maka kada ka rasa ranka" saurin tashi yayi zai bita bathroom d'in saboda yanda take tafiya tana kad'a masa bom²,kafin ya k'araso tayi maza ta fad'a ciki ta kulle k'ofar tana masa dariya,yayi k'wafa yace "za ki fito ne" ta k'ara kyalkyalewa da dariya tace "tou ba gaskiya na fad'a ba?" Yace "ohoo! Za kimin bayani da capital letters" tace "har da small² one ma zan maka" yayi murmushi ya zauna bakin gadon yace "Allah ya so ma ba ni kad'ai nayi zurfin ciki ba" d'an bud'a k'ofar tayi ta lek'osa tana kallonsa ta d'aga masa girarta d'aya tace "kai da wa kuka yi?" Yace "ohoo! Kin fi kowa sani" tayi d'an dariya mai cike da shak'iyanci then ta koma tayi wankan ta fito. A haka kwanaki sukaita juyawa daga d'aya zuwa biyu zuwa sati,tafiya tai tafiya har yanzun ga shi Manar ta samu kimanin watanni uku da haihuwa,yaranta kam sai dai muce alhamdulillah dan yanzun idan ba su ba da wuya ka iya bambance su,dama Alhussain ne idan ka kalla za ka iya gane su,yanzun kam tuni ya kamo d'an uwansa,in ba kula kayi da wani abu tattare da su ba zai matuk'ar ba ka wahala ka iya cankansu a kallo d'aya,suna k'ara wayo kamanninsu da Waleed na k'ara fitowa,Dadda da Deejah kuwa har lokacin suna nan a masarautan Vishakpatnam basu koma Nigeria ba,Waleed ya rik'esu da dad'in baki,and yanzun kuma sam ba shi da lokacin zama,idan bai shiga skul ba yana hospital,d'an zamansu Dadda d'in nema suke d'ebe mata kewa duk da su Ameerah da Rania suna nan kullum manne da juna sai lokacin bacci yake raba su,da yake suna saka ran zai samu hutu ba da jimawa ba,ranan da yake fad'a ma Dadda ya samu hutu though ba mai tsayi bane,ta fara murnan za ta koma gida,cikin satin kuwa gaba d'aya suka fara shirin zuwa Nigeria dan sun d'auki lokaci mai tsayi rabonsu da k'asar,shiri na sosai da sosai suka yi,su kansu suna missing gida da y'an uwa,ranan da za su tafi bayan sun gama shiryawa sun yi sallama da iyayen dan kaf d'insu ne za suyi tafiyar Waleed,Manar da yaransu,Azaan,Ameerah,Amaar,Rania,Dadda da Deejah da ta zama y'ar gari,yanzun kam ta rage jin damuwa idan suna tare da su Manar,saboda yanda suke janta ajiki ya sa ta manta da komai ta sake cikinsu,idan ka gansu baza ka tab'a cewa su ne wanda a baya ba sa shiri ba ko na sisin kobo,here jirgin masarautan ya kwashesu zuwa Nigeria. Sanda jirginsu yayi arriving bayan sun fito hadiman da suka musu rakiya da wanda za su zauna da su har sanda za su koma suna biye da su da kayansu,Waleed d'auke da Alhassan dake cikin baby pack ya mashi goyon gaba,saboda yaron bai cika sakewa ba idan ba a hannun iyayensa ba,yaran gwanin burgewa suna cikin k'ananun k'aya iri d'aya,blue d'in jean da white riga mai zanen Micky mouse,hatta pack d'in da suke ciki shima babu bambanci blue da ratsin fari sai takalmansu farare,Alhussain kam yana gurin Deejah da yake shi babu da wanda bai sakewa,yanda suke tahowa hannun Waleed rik'e da na Manar suna hira da dariya kad'ai zai maka describing ba karamin dad'i yanayin da suke ciki yake musu ba,ganinsu a k'asarsu mahaifarsu wani shauk'i yake k'ara musu na sosai da sosai,sun shigo arrival inda mutane suke jiran y'an uwansu because lokacin kusan jirage hud'u suka sauka har wanda suka zo a ciki,kamar wanda akace Manar ta kalli mutanen gurin ko mai son neman wani abu,can daga gefe idanunta suka kai kan wata fuskar da taji kaman ta santa somewhere,har ta d'auke kanta kuma da sauri ta d'an juya ta sake kallonta tana squeezing fuskarta da son tuna inda ta san mai fuskar,lokacin ya yi dai² da sanda itama Afiyah dake jiran fitowar Daddy'nta ta kallesu jin mutanen kusa da ita suna maganar fine kids d'in da suke hannun Deejah da Waleed,tar idanun Afiyah suka sauka cikin na Manar data waigo,d'an bud'a idanu suka yi su duka biyu,Afiyah cikin mamaki take kallon Manar tana mamakin kou daga ina suke,haka itama Manar mamakin ganin Afiyah a gurin take,Waleed dake mata magana bata jiba,sanda ya waigo yaga tana kallon wani guri,ya kai hannu ya d'an bugo backhead d'inta,da sauri ta juyo tace "ouch! Master da zafi fa" tana shafa gurin,wani kallo ya mata ya sak'alota k'asan arm d'insa yace "me kike kallo ne baza ki kula ba sai kin fad'i ki janyomin aiki?" A shagwab'e tana kumbura fuska tace "tou ba tsohuwar matarka na gani ba,zan mata magana" da sauri ya fiddo k'ananun idanuwansa,sai kuma ya d'aure fuska dan ma karta k'ara masa maganar yayi saurin mayar da hankalinsa kan Alhassan yana shafa sumar kan yaron dake kwance luff,Manar da taga ya d'auke kai ta fahimci maganar ne ba ya so,tayi wani murmushi sai itama bata ce komai ba har suka fita inda motocin da suka zo d'aukansu suke,har lokacin fuskarsa a d'aure ya bud'e mata back seat,ba tare da ya kalleta ba yace "get in" ita dai kallonsa kawai take kafin ta fara shiga,Deejah ta shiga front seat,lokacin yana k'ok'arin shiga Afiyah da ta kasa hak'uri ta biyosu ta kirasa "Waleed!" Tsayawa yayi cak kaman wanda aka dannama pause yana gritting teeth d'insa,since Manar ta masa maganarta yaji ba ya k'aunar ko had'a ido suyi da ita,tsaf abunda ya faru shekara guda da wasu watanni ya dawo masa,kamar yanzun yake kan faruwa,Afiyah cikin raunin murya ta sake cewa "Waleed! Yanzu daman za ka iya gani na ka wuce bamu gaisa ba?" Daga Manar har Deejah juyawa suka yi suna kallonta,shi kam gogan yana tsaye yanda yake ko tari baiba bare ta sa rai zai juya ya mata magana,Afiyah ganin haka tana kallon yaron da yake mik'ama Manar tayi d'an murmushi hawaye cike a idonta tace "Babyn kune?" Manar da taga yanayinta ta gyad'a mata kai,a sanyaye Afiyah ta matso tana kallon yaron dake kwanciya jikin Manar yana kallonta tace "wow! Allah rayasa,what's his name?" Manar tace "Ameen! Alhassan" d'an bud'a idanu Afiyah tayi tace "twins ne?" Ta gyad'a mata kai,Afiyah ta k'ara yin murmushin yak'e tace "ina d'ayan fa?" A hankali Deejah ta bud'e gurinta tace "ga shi nan bacci yake.. Ina wuni?" Afiyah ta amsa tana kallon Deejah ta d'an lek'a fuskarsa tana ta k'ok'arin mayar da hawayenta tace "maa sha Allah,Allah musu albarka" Waleed dake tsaye gurin ya amsa addu'ar da tama yaransa,har ransa yaji dad'i da sanyi,then a hankali ya shiga motar eye in eye yana kallon Afiyah ya d'an saki fuskarsa yace "yaushe ne aurenki?" Da fari shiru tayi tana jin kamar taita kurma ihu,sanda ya sake maimaita mata tambayar a sanyaye tace "an kusa in sha Allah" ya gyad'a kai yace "Allah nuna mana" tace "Ameen.. Amma za ku zo ai?" Yayi d'an murmushi yace "idan an gayyace mu ko?" Tayi murmushi itama tace "za'a gayyace ku mana" ya gyad'a kai yace "tou Allah sa" tace "ameen.. Na ji dad'i sosai wallahi.. Na gode" yace "babu komai.." Sanda ta kalli Deejah tace "ya Hjy?" Deejah tayi murmushi tace "tana lafiya" Afiyah tace "a gaisheta.. Sai an jima" tana fad'a bata tsaya ba ta juya ta bar gurin da sauri,Waleed ya d'an juya ya bita da kallo har ta bar gurin,wani irin harara Manar ta galla masa a fusace tace "ka sauka ka bita mana" sai kuma tayi tsaki cike da jin haushi,da sauri ya waiga yana kallonta ya bud'a idanu,cike da mamaki yace "what?" Tace "ohoo" kallonta ya dunga yi ya kasa magana,can kuma ya kai hannu ya d'auko yaronsa ganin irin rik'on da ta masa yana daf da fad'owa,ya kwantar da shi a jikinsa yana shafa bayansa,Manar dai gefe ta juyar da fuskarta tana kallon waje,driver ya shiga ya ja su suka bar airport d'in,tunda suka taho bata k'ara magana ba,Waleed ya kalleta ya fi a k'irga but ya kasa mata magana,saboda yanda ta d'aure fuska ya ji shayin tanka mata,motocin su suna shiga gidan drivers suka yi parking Manar ta bud'e gefenta ta fita lokacin su Asad da su Mu'awiyah suka k'araso suna musu sannu da zuwa,tayi musu murmushi ta rungumesu d'aya bayan d'aya then ta wuce b'angarensu,Waleed dai da kallo ya bita ya san ya tsokanowa kansa,direct duka suka bi bayanta zuwa side d'in,Mother tana kitchen ta jiyo muryan Manar tana kwalo mata kira,da sauri Mother ta taho parlor tana cewa "ga ni nan habibtiiy" Manar da ta nufi hanyar bedroom tana jin maganarta a bayanta tayi saurin juyawa,da saurin kuma sai ta nufi Mother tana sakin murmushi da fad'in "i missed u Mother" mother dake mata murmushi tace "i missed u too my kid" suka rungume juna cike da farin ciki,shigowar su Ameerah yasa Mother sakin Manar ta rungume Ameerah da Rania then Deejah da tayi shigowar k'arshe,nan mazan suka shigo suma da yaran duka,a nan suka baje suka cika gidan da hayaniya,Aunty kam da aka kai mata labarin zuwansu nan ta taho itama,ta musu barka da zuwa aka gaggaisa,then suka fita ita da Mother suka nufi b'angaren Dadda,because suna sauka ta nufi gidanta tana cewa "dan Allah Mamman kuyi zamanku a b'angaren iyayenku kada kuzo min nan ku dame ni da kafirin surutunku" Amaar yace "Hjy koranmu kike kuma?" Tace "yo wallahi na gaji ne d'an fodiyo kuyi zamanku can kuyi hiran" Amaar ya yi murmushi,shi dai Waleed baima kulata ba yayi shigewarsa,wuni suka yi a gidan sai
Chapter 176 · 0% Book details