← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 184

Sashe 17

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

bai shirya fad'ar maganar ba yace "arhmm! Think ya kamata tunda ke kad'ai kike fad'a mata taji,ki hanata saka irin kayan nan tana zama da su" k'uri Dadda ta masa da ido tace "ko saboda me?" Yace "wanda suke shigowa" kama baki tayi tace "yau naji ikon mai mana ruwa da k'ank'ara,fisabilillahi su waye suke shigowa idan ba ku ba?" Kallonta yaci gaba da yi,Dadda ta fara mita "kuji dai wani magana kuma,wai na hanata sawa,akan me ni kuwa zan hanata,yarinya tana shan iska kawai sai nace ta kirb'a uban kaya a jikinta..? A'a wallahi bazan hanata sa abunda ranta yake so ba,kai wa yake hanaka saka wanda ranka yake so? Idan ba ka son ganinta a haka sai ka daina shigo min,babu lallai babu tilas" gyad'a kai yayi bayan ya gama saurarenta ya juya ba tare da ya ce mata komai ba ya fita ya barta sai mita take,Manar da ta gaji da sauraren mitarta ta mik'e tana b'ata rai ta nufi hanyar fita,Dadda ta bita da kallo tace "ke kuma ina za kije?" bata ce mata komai ba har ta k'arasa bakin k'ofa,haushin shirun da ta mata yasa Dadda d'aga murya tace "kina ji ina maki magana kika share ni?" Still Manar bata kulata ba ta bud'e k'ofar,gyad'a kai Dadda tayi tayi k'wafa fuskarta kamar za tayi kuka ranta ya sosu da abunda Manar tayi mata ta zubawa farfesunta idanu ta kasa ci,Manar dai tuni ta sa kai ta fice daga gidan,a parking space ta hangosa yana shirin barin gidan tun daga nesa take kallonsa sanda ya kallo gurin da take da sauri ta d'auke kai tana zumb'ura baki ta tsaya balcony tana knocking k'ofar tana satar kallonsa,mother ta bud'e mata k'ofar kasancewar duka yaran gidan basa nan,a door way ta tsaya tana k'are mata kallo,fuskarta a d'aure babu alamun wasa ta watso mata tambaya tace "a haka kika ratso gidan kika taho nan?" Kallon jikinta Manar ta fara yi,ta dago a shagwab'e tana kallon mother tace "mother me nayi?" Wani kallo mother ta mata a d'an fusace tace "ni kike tambaya me kika yi?" Rau² idanunta suka yi ta kasa magana,wani tsawa mother ta mata da yasa ta sakin kuka da gudu ta juya ta nufi hanyar komawa apartment d'in Dadda,har lokacin Dadda ta tasa plate d'inta gaba da hannuwanta biyu ta rafka tagumi,sanin yadda suka rabu yasa ko da ta shiga bata tsaya parlor ba ta wuce bedroom da sauri tana matsar k'walla,Dadda ta d'ago ta bita da kallo bata ce mata komai ba,tana shigewa ta kwanta saman gado ta ci gaba da rera kukanta. Da dare lokacin Waleed ya shigo fuskarsa a d'aure ya tarar da su zaune a parlor su hud'u,direction d'in da Manar take ya fara kalla,wannan karon sanye take da 3quarter na jeans da sleeveless light blue kanta babu hula,ya kalli yadda suke hira da Amaar sai dariya take b'ab'b'akawa ita da Ameerah,wani k'wafa yayi a k'asan ransa ya juya zai koma,Dadda da tun shigowarsa ta hangosa tace "kai kuma fa?" Tsayawa yayi daga bakin k'ofa,tace "da kai nake fa Mamman ka min shiru" bai juyo ba yace "me zan miki?" Tace "amma dan wulak'anci kana ji nake maka magana,shi ne za kace me za ka min?" Saurin juyawa yayi yace "laifi ne dan na tambayi abunda zan miki? Think ke kika ce idan bazan iya ganin jikarki a yadda take ba na daina shigowa,right?" Kicin-kicin tayi a masife tace "ehh! Na fad'a d'in,daga yau ma kace ka daina zuwa ka gani idan wani abu zai dame ni" gyad'a kai yayi yace "Ok! That's good,daga yau zan daina shigowa kamar yadda kika ce,but kada kuma daga baya ki k'ara zuwa ki had'a ni da mahaifina,tunda bakya son a nuna maki gaskiya,kin fi son wanda za suyi miki shiru,shi kenan kuyi duk yadda kuka so.." Yana gama fad'a ya aikama Manar da ta kafesa da idanu wani kallo a tsawace yace "bar kallo na" then yasa kai ya fice,tafa hannuwa Dadda ta shiga yi baki sake ta kasa furta komai,Amaar sai k'unshe dariya yake shi da Ameerah,Manar ta d'auke kanta tana tab'e baki,can Amaar ya daure duk da dariyar dake cinsa yace "Dadda wai me ya faru ne?" Kamar yayi playing d'inta idanunta sun cicciko da k'walla ta fara mita "ina ce a gabanku mutumin nan ya gama farfad'a min maganganun duk da suka zo bakinsa? Fisabilillahi ko dai ban had'a alak'a da shi ba,ya dace ya kalleni ya gaya min wannan maganar? Ko dai bai girmama shekaruna ba ai ya girmama furfura ta,ko ba haka ba?" Amaar ya gyad'a mata kai yace "hak'k'un!" Ta fara share hawaye kafin tayi zaraf ta mik'e,Amaar yayi saurin kallonta yace "ina kuma za kije yanzun?" A fusace kamar shi yayi mata laifin tace "ya ma za'ayi bayan kana kallon abunda ya faru ka tambayeni inda za ni?" Wani murmushi yayi yace "Allah ba-ki hak'uri" tayi gaba tace "ameen" tana fita Ameerah ta fara dariya tace "wallahi ta tafi kai k'aransa gurin Abba" Manar ta b'ata rai tak'i cewa komai kamar ba ta parlon,sai da aka jima kafin Amaar ya kalleta yace "wai me ya faru?" Manar tayi saurin kallonsa,yace "i meant me ya had'a su?" Tab'e baki tayi kafin ta sanar masa abunda ya faru da safe,Amaar dake saurarenta ya gyad'a kai yana kallonta yace "My brother ya yi gaskiya,as he said bai kamata kina zama da irin kayan nan ba tunda kin san muna shigowa,dukan mu babu muharraminki,so kinga akwai aure tsakaninmu kenan,a shawarin da zan iya ba-ki matsayin k'anwata,duk lokacin da muke nan ki daina sawa kinji?" Shiru tayi ta kafesa da idanunta,yayi murmushi ganin yadda ta b'ata rai yace "Ba fa ina nufin ki daina sawa duka ba,i just mean idan mun shigo nan,kin gane?" Gyad'a masa kai tayi ba don ta so ba,yayi murmushi yace "yawwa k'anwata,na san ki da biyayya Allah sa za kiyi amfani da shawaran da na ba-ki" k'in cewa komai tayi har Amaar ya gaji da mata maganar,ya d'auki wayarsa yana sakin murmushi yace "ko dai na kira maki Mommella kuyi magana?" Tayi sauri ta kallesa,bai jira cewarta ba yayi murmushi ya fara making call,ba'a jima ba Mommella ta d'auka,yasa wayar a hands free suna jin maganarta suka fara rige²n mata magana,da sauri ya mayar da wayar yadda shi kad'ai zai ji ya kai wayar kunnensa,suka gaisa da Mommella,Manar ta zuba masa idanu ta b'ata rai,Ameerah ma ta koma gefe ta masa k'uri da idanu tana jira yace su zo su karb'a,yana kallonsu yayi murmushi ya mik'e tsaye kamar zai fita da sauri suka fara masa magiya "Yaah Amaar dan Allah.." Saurin juyowa yayi ya d'aga musu gira yace "what?" Manar dai kamar za tayi kuka tace "to kuma ya za ka fita baka bari mun gaisa ba?" Ya d'an matsar da wayar daga kunnensa yana musu wani kallo yace "thought bakwa buk'atar ku gaisa ne?" Da sauri Ameerah ta tari numfashinsa "a'a wallahi muna so" gyad'a kai yayi yace "ohoo!" Ya dawo ya zauna,a nutse suka gama magana da Mommella then yace "Mommella Azaan fa?" Mommella tace "baya nan ya fita" yace "alright! Na kirasa ban samesa ba" Mommella tace "think ya bar wayoyinsa a gida,nima tun d'azun nake kiransa ban samesa ba" kallon Manar yayi da take cika yace "ga kids d'inki suna hararata saboda ban basu waya kunyi magana ba" Mommella tayi tace "give them the phone kai kuwa mana.." Manar ya kalla yana d'aure fuska yace "ni kuke jira na kawo muku wayar?" A tare suka yi saurin tasowa ya mayar musu wayar hands free,suna kan magana da Mommella Azaan ya shigo,yayi sallama Mommella ta amsa masa,zaunawa yayi har suka gama magana,suka yi sallama lokacin Manar take tambayar Mommella "Mommella yaushe za ku zo?" Shiru Mommella tayi da farko then tace "i'm so sorry baby mun d'aga zuwan ne amma da yanzun haka muna 9ja" b'ata rai tayi kamar za tayi kuka tace "to kuma sai yaushe za ku zo?" Mommella tace "maybe sai end of the year" ba'a son ransu ba suka amsa "Allah kawo ku lfy" Mommella ta amsa "ameen" Azaan da tun zamansa baiyi magana ba Mommella ta kalla tace "Amaar ya kiraka bai sameka ba,ina ka bar wayoyinka?" Suna jin sanda yace "i'll call him" Manar tace "Yaah Azaan!" Yace "Mmm! Baby ya kike?" Tace "lafiya lao.. Kaifa?" Yace "alhamdulillah" kafin ta sake magana yace "kice da Amaar za muyi magana anjima kad'an" kallon Amaar da ya kulle idanuwa tayi tace "yana jinka ma" yace "alright! Later dear.." Suna yin sallama suka mik'awa Amaar wayarsa,ya tashi ya fita ya barsu su biyun suka ci gaba da hira suna dariya..
Chapter 17 · 0% Book details