Sashe 52
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ga na gida yana nema,wanda zai rik'e mana ita da mutunci fiye da na waje,dama ai a rashin wanda ka sani za ka bawa bare yarka" Mama ta ji dad'i sosai tace "na gode sosai aminiya,but ki fara tuntub'ar Afiyah kiji idan babu matsala,nan dai ta b'angaren mu babu ko wane irin matsala gaskiya" Hjy Sahiba tace "alright! Zan tambayeta naji zuwa gobe duk abunda ake ciki i'll let u know" suka yi sallama. Almost 3 days da yin maganar Mama ta samu tabbaci kan Afiyah ba ta da ko tsayayyen saurayi,and tun ranar da su Waleed suka je gidan ma take damun Mummy'nta da zancensa,here ta mayar da hankali wajen tursasa Waleed ya tsayar mata magana d'aya because tana son tunkarar Abba da zancen,amma sai hanya² yake mata,ba ya son ko had'uwa ma suyi da ita bare dogon magana ya had'a su,idan ya zama lallai sai sun had'u kuwa gaisuwa ne shima yana tafiya yake gaisar da ita ba ya bari magana yayi tsayi tsakaninsu,yau kam da suka yi magana da Hjy Sahiba har ta tura mata digit d'in Waleed da Afiyah ta dameta ta nema mata,Mama ta tura sai dariya take yi tace "Sahibatiiy anya Afiyah bata zurma da yawa ba?" Hjy Sahiba sai dariya take itama cikin jin dad'i tace "wallahi fa kema kya fad'a,nima nan tsiyar da nake mata kenan kullum ba ta da magana sai na Waleed" Mama cikin jin dad'i tace "banda abun Afiyah idan ta yi hak'uri kwana nawa ne maye ya yi amarya ya lashe? Kin san dai baza mu saka tsababan kwanaki ba,so nake ayi abun nan a wuce gurin.." Hjy Sahiba tace "gaskiya kam,gara ayi a wuce gurin,tunda suka fara nuna rawar k'afa kada suyi abun kunya a gaban idanunmu wata rana.." Hiran da suka dunga yi kenan kafin suka yi sallama suka ajiye wayar. Washe gari Waleed ya fito zai tafi office,duka kwanakin ba ya cikin walwala sosai duk a kan maganar auren da Mama take damunsa da shi danma yana dojewa bani cika tsayawa suyi dogon magana ba,har ya nufi stairs zai sauka ya hango parlon babu kowa,ganin haka ya san akwai dalilin da yasa bata fito ba,here ya koma da baya duk da yadda gabansa yake fad'uwa ya daure ya lek'a bedroom d'inta,a tsaitsaye yana rik'e da k'afarta ya gaisheta yace "Mama na fita office" har ya juya zai rufe mata k'ofar ta kira sunansa,ya waiga ya tsaya rik'e da handle d'in,tace "magana nake son muyi,za ka iya shigowa ciki?" Yace "Mama ina sauri ne an kira ni a hospital" tace "kenan ban isa nayi magana da kai a lokacin da nake so ba?" Yace "not at all" ta daure fuskarta race "to ya ya ake ciki? Za ka shigo ne ko kuwa tafiyar za kayi sai ka ba ni lokacin ganinka?" Komawa yayi cikin kad'an ya cusa hannunsa d'aya cikin aljihunsa yana jira yaji me za tace,tace "maganar yarinyar nan da mukayi 3 days back nake son mu k'are ta yau" da sauri ya d'aga kansa ya kalleta yace "amma Mama think an bar maganar tun ranar fa?" Fuskarta babu alamun wasa tace "ba'a barshi ba" yayi still yana kallonta,tsabar mamakinta yasa shi cewa "to Mama ni yanzu me kike son nace?" Tace "maganar kud'in lefe zan maka dama da kake gudun mu had'u,zan ta jiranka ne kana min hanya²? Na gaji na sanar da Abban ku,yanzu mu suke jira dan tuni sun tsayar da ranar auren one month" kallonta ya dunga yi ya kasa magana,tace "sai ka tura min kud'in through account za mu shiga kasuwa da Hjy Izzatu mu had'a kayan tunda kai ba ka da lokaci" yace "amma Mama na fad'a miki matsalata fa!" Tace "ni yanzu ba maganar matsalarka nake ba,abunda nace maka ka tura min kud'in kaya,ban nemi muyi dogon magana da kai ba" ya gyad'a kai yace "alright! Mama kin fi amincewa ayi auren a haka?" Tace "sure!" Yace "kuma kina sane da matsalar da nake fad'a miki?" A fusace tace "wannan wane irin zancen banza ne kake min shi Waleed? Kullum kaita fad'in matsala²,wane irin matsala kake tare da shi ne kam da ni ban san shi ba?" Wani murmushi yayi mai ciwo yace "Mama wallahi kika bari aka yi auren nan a haka,wata rana sai yarinyar nan ta gudu da k'afarta!" Ta d'aga kai tana kallonsa tace "za ka koreta ne hala?" Ya girgiza kansa had'e da d'aga hannayensa alamun surrender yace "not at all Mama!" Tace "to idan ba haka za kayi ba,me kake nufi?" Numfashi ya sauke ya tafa hannuwansa yace "yeah! Yanzun kika yi magana Mama" ta dunga binsa da kallo tana jira taji me zai ce,yace "Mama kinsan Allah yarinyar nan baza ta iya jurewa zama da ni ba" da sauri Mama tace "za ka dunga yankan naman jikinta ne?" Yace "um'um! I just meant she can't take me" wani kallo ta maka masa tace "goyaka za tana yi ne da kake fad'an haka?" Wani dariya yayi yace "Mama kin fa san maganar da nake,kuma kina sane da cewar na mata yawa" kallonsa ta dunga yi tace "wane iskanci ne haka kake fad'a min Waleed?" Yace "daga ganinta Mama baza ta yi lafiya ba,so ni kuma kinga lafiyayye ne,kayan aikina lafiyar su lou,shi ne kawai bayanin da nake miki" yana fad'ar maganar tamkar ya fusatota ta bud'e masa wuta tana fad'a,ganin haka ya girgiza kansa cike da takaici,ya san baza ta tab'a hak'uri ta bar maganar ba,ko me zai ce mata kuwa,kawai sai ya juya yace "shi kenan Mama zan tura miki idan na je office.. Allah sa hakan shi ne mafi alkhairi." Yana fad'an haka ya fice yana jin ransa duk a jagule,yana k'arasawa office ya mata transfer cash adadin da ta nema,yana gamawa bai ma jira ta kirasa tace ta gani ba ya kashe wayarsa ya zauna office yayi shiru yana tunani,sosai ya shiga damuwa da maganar auren nasa,ranar bai tsinana aikin komai a hospital ba,duk wanda ya ganshi cikin abokan aikinsa sai ya tambayeshi lafiya yake? Saboda yadda yake sukuku,sai dai yayi murmushin k'arfin hali kawai ba ya iya ce musu komai,a haka har lokacin komawarsa gida yayi but ba shi da niyyar tafiya,sai wajen 10pm da zaman kad'aici ya fara damunsa sannan ya mik'e a hankali ya fito daga office d'in ya kulle ya nufi inda motarsa take..