← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 184

Sashe 118

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna gama shiryawa ta d'auki rigarta za ta mayar,yanda taga duk ya yi squeezing ta dunga kallon rigan kamar za tayi kuka ta kasa sawa,Waleed dake kallonta ta cikin mirror sai murmushi yake ganin yanda ta b'ata fuskarta kamar za tayi kuka,a hankali yace "kisa muje lokaci yana wucewa" wani kallo ta masa tace "to baka ga yanda ka mayar min rigan ba?" Ya zaro k'ananun idanuwansa yana kallonta yace "noo! Ni ban mayar miki riga haka ba kar kiyi min sharri" jifansa tayi da rigar ta koma gefen gado ta zauna tana share hawaye,da sauri ya k'arasa ya zauna kusa da ita ya janyota jikinsa yace "shiiii!" Turesa tayi cikin kuka tace "toh a haka zansa rigan kuma?" Yace "idan kin sa waye zai gane? Dubi fa hijab za kisa and it's not short har kasa yake,idan munje gida sai kisa wani tunda ba kya so a gane munyi wani abu" kallonsa ta dunga yi kafin ta turo baki tace "to kai me yasa baka mayar da wancan kayan ba?" Yayi murmushi yana shafa kansa yace "toh ni dama ai dole na canja su,baki ga yanda kika sa na b'ata su ba?" Saurin hararansa tayi ta tashi za ta wuce bathroom da sauri ya rik'ota yana mata dariya yace "ina za kije kuma?" Ta turo baki tace "bathroom zanje nasa rigan" kallonta ya dunga yi yace "kisa muje please,me na wani sai kin shiga bathroom,kunya ta kike ji?" Kautar da kai tayi tak'i cewa komai,yayi murmushi yace "naga dai babu wani kunya tsakaninmu ko akwai?" Da sauri ta gyad'a masa kai,ya kai hannu ya juyo da fuskarta yana kallonta yace "tell me please me kike jin kunyan?" Saurin fad'awa jikinsa tayi ta b'oye kanta a k'irjinsa,yayi dariya yace "tell me yanzun na cire na baki shi" gwalo idanuwa tayi tace "me za ka ban?" Yace "abunda kike jin kunyan mana" dariya ta fara tace "ni wallahi ba na so" yace "kina so mana,fad'a min naji me kike jin kunya?" Saurin kulle idanuwa tayi tace "ni dai Allah ka bari ba na so" yace "ni kuma inaso,dan haka kima fad'a kafin na miki abunda za ki shekara kina jin kunya" wani zaro idanu tayi tace "me za kayi?" Yace "ina ruwanki?" Da sauri tana turo mai baki tace "nifa kunyarka nake ji ba wani abu ba" dariya yayi yace "ban yarda ba,kuma na san ma abunda kike jin kunyan" da sauri ta d'ago tana kallonsa tace "what?" Belt ya fara kwancewa yana kallonta yace "let me show u" tana ganin ya kwance belt d'in zai sauke trouser k'asa ta kwalla k'ara da gudu ta shige jikinsa ta k'ank'amesa tana fad'in "please ka bari ba na so" rungumeta yayi ya dunga mata dariya,sanda yayi mai isarsa ya d'ago kanta yace "ki bari na nuna miki please" da sauri ta girgiza kanta tace "ni wallahi ba na son gani" wani dariya ya dunga yi yace "it's not a big deal kawai kalla za kiyi ku gaisa,i knew it's a new thing for u but ki daure ki d'an kalleta kad'an" girgiza masa kai ta k'ara yi yace "c'mon it's ur new toy fa za kiyi wasa da shi ne" k'ara girgiza masa kai tayi jikinta was vibrate,yayi murmushi yace "okay! Cika ni tou mu tafi" da kyar ta sakesa tayi baya tana turo mai baki,yayi murmushi sanda ya d'auki numfashinta ya rik'ota,da k'arfi ta fasa masa ihu,ya tuntsure da dariya ya rungumeta yace "matsoraciya kawai.. Muje kada mu b'ata lokaci" saurin wucewa gaba tayi ya bita a baya suka sakko sai kalle² take kamar tana neman abu,hannunta ya rik'o yace "me kike nema?" Ta girgiza masa kai tace "nothing" suka fito ya kulle gidan. Gaban wani had'ad'd'en saloon ya tsaya kafin ya fita ya rakata,sanda ta shiga yana kallonta ya mata murmushi ya mata blowing kiss,tayi dariya ta zauna kan chair da matar take nuna mata,ya koma mota ya zauna sanda ya d'an lumshe idanunsa kafin ya bud'e ya turama Azaan sak'o "kai malam ku muke jira fa,idan kuka b'atan lokaci zan wuce na mayar da ita gida in yaso ka yiwa Hjy Siyama bayani" yana tura masa yayi dariya yana shafa kansa then ya tura masa location d'in da suke,not too long motar Azaan ya tsaya gurin ya sauke glass yana kallon motar Waleed,Waleed ya sauke glass yana kallonsa yana masa murmushi,Azaan ya hararesa yace "ai wallahi za ka san ni kama haka.. Tsaf zan rama abunda kayi min" Waleed sai dariya yake masa ya k'i cewa komai,Azaan ya d'age glasses d'in yana kallon Ameerah dake gefensa a hankali ya d'an karkato da kansa yana kallonta,ganin ta k'i d'ago kai ta kalleshi ya kai hannu ya juyo da fuskarta,still k'in yarda tayi su had'a ido but fuskarta a sake tana masa murmushi,yayi murmushi da wani cool voice kamar ba Azaan ba yace "look into my eyes please" k'in yarda ta kallesa tayi yayi murmushi a hankali ya d'ora lips d'insa kan nata idanunsa suna kallonta yana tsotsa a hankali,Waleed yaga basu da niyyar fitowa ya kira Azaan,da sauri Azaan ya d'auka har lokacin bai saki bakin Ameerah ba,Waleed yace "kai malam kada ka zama cinye du mana,ka saki yarinya taje a mata abunda za'a mata suzo mu tafi" d'an lumshe ido Azaan yayi kafin ya saketa yace "kai kuma d'an sa ido meya ruwanka tunda ka hanamu gurin da zamu huta a gidanka?" Waleed yayi dariya yace "haba so kake na zama babban banza,da na maka k'ok'ari ma na fito maka da ita ban maka ba kenan?" Azaan ya tab'e baki yace "ba wani sosai ba" k'wafa Waleed yayi yace "good.. Ka ga kace gobe ma idan na tashi fitowa ba sai na kiraka ba" daga haka ya katse wayarsa,Azaan ya kalli Ameerah yace "let's go" ya bud'e motar ya fita sai fama yake da jallabiyya kamar wanda ke shirin karb'an shaidan zama limami,Waleed yana cikin motarsa sai dariya yakema Azaan ganin yanda yake wani rawar jiki,yace "tukuna ma guy" yayi wani murmushi ya lumshe ido yana shafa k'irjinsa. Kuka sosai Mama da Afiyah suke yi a gaban bokan Mama fad'i take "yanzu babu wani hanyan da za'a iya bi kuma? Wallahi ba zan iya juran ganinsu tare da yaro na ba,dan Allah kayi wani abu ka rabasu wallahi ba na son ta auran min d'a" boka dai yayi iya yinsa ya d'ago yace "babu wani sauran hanyan da ya rage.." Mama ta d'ora hannu aka tana kuka wiwi tana kiran mutuwa,ni dai na kalleta nace "kuji matar dake gurb'ataccen hanya ita ke kiran mutuwa,to wai idan ma mutuwar ya zo mata,taje lahira a me za ta tashi ne?" Afiyah kam ma gaba d'aya ta kasa magana kukan ma ya k'i zuwa ajiyar zuciya kawai take iya saukewa da k'arfi,boka yace "sai dai kuma idan za ku yi k'ok'arin raba su ta hanyar kissar ku na mata,da zaran kun had'a su fad'a,za mu muku taimakon da zai raba su har abada" a wani irin guje suna had'a baki suka ce "za muyi in dai komai zai dawo mana kaman da" boka ya gyad'a kai yace "ku bani nan da sati biyu kafin ku dawo na kammala duk abunda zanyi" har rige² suke wajen yi masa godiya,kafin suka taho suna tafiya cikin dajin suna k'us² d'in yanda za su gillama Manar da Waleed tuggun da zaisa suyi fad'a kaca². Har ciki Azaan ya raka Ameerah,Manar tana hangosa ta mirror ta kulle idanunta dan wani kunyarsa take ji yanzun data rasa na mene ne,ta k'asan lashes d'inta take satan kallonsu tana b'oye dariyan da take,yama matar bayanin yanda yake so ama Ameerah ponytail style,ya juya zai fita gurin Waleed Manar ta bud'a idanu tana kallon Ameerah tana mata dariya,Ameerah ta gilla mata harara tace "muguwa" dariya Manar ta kyalkyale da shi,Azaan ya juyo yaga Manar tana dariya,kunnenta ya rik'e da kyau tayi y'ar k'ara tace "auch! Yaya it really hurts" ya dungure mata kai yace "za mu had'u dake ne" ya fita da sauri ya barsu,motar Waleed ya bud'e ya shiga yana kallonsa yace "ka kyauta" Waleed ya d'auke kai yana sakin murmushi yana shafa kwantaccen gashin k'irjinsa yana wani lumshe idanu,Azaan ya zaro idanu yace "hey Mr Man" Waleed ya d'an kallesa yana d'aga masa eyebrows yace "what?" Azaan yace "ya dai? Ko baka gama bane har yanzu?" Dariya Waleed yayi yace "baza ka gane ba Bhidu" Azaan ya fara dariya yace "noo! Yanzu kam zan gane,tell me what's going on?" Kallonsa Waleed yayi yace "ka bari dai ba yanzu ba" gyad'a kai Azaan yayi yace "alright.." Sanda aka gama musu gyaran kai kada kuso ganin drama tsakanin Waleed da Azaan,Waleed yana cewa shi zai biya,Azaan yana cewa shima shi zai biya ai both Ameerah da Manar k'annensa ne,Waleed yace "wallahi baka isa ba,akan me za ka biyama matana kudin gyaran kai?" Azaan yana masa dariya yace "mene to dan na biya?" Waleed ya girgiza masa kai yace "it's my duty.. So karb'i kud'inka if not kuma yanzun nasa a mayar mata da kanta yanda yake" matar da ta musu saloon dai ta tsaya kallon ikon Allah tana ta dariya,k'arshe da kyar suka hak'ura kowa ya biya nasa,then suka fito suka kama hanyar gida,ko a mota Waleed suna tafiya suna hira ne,Manar ta zame hijab d'in kanta tace "Yaya ka ga" ta nuna masa fishtail braids da aka mata,d'an kalla yayi yana sakin mata lallausan murmushi yace "awwwn! Ya yi kyau" ya kai hannu yana tab'awa,bige masa hannu tayi tana turo baki tace "to sai ka lalata min kuma?" Yace "ba sai mu koma a sake wani ba?" Harararsa tayi tace "tabbb' da zafi fa suke jan gashin kuma" ya kalleta yace "really?" Ta gyad'a masa kai kamar za tayi kuka,gyad'a kai yayi yace "ohh! Tunda suna yi maki da zafi baza mu sake zuwa ba" ta d'an yi dariya tace "da wasa fa nake yi,da tana tab'a min kai har bacci na fara" yayi murmushi lokacin suka tsaya 2 houses away,motar Azaan ya k'araso gurin yayi parking,a hankali ya kai hannu ya d'an d'aga hijab d'in Ameerah yana kallon style d'in da yasa aka mata,yayi murmushi a hankali ya zame hijab d'in duka ya saita camera ya musu selfie,shooter sound d'in yasa ta d'ago idanunta da suke nan kamar an watsa
Chapter 118 · 0% Book details