Sashe 42
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali tana kallonsa tace "Yaya!" Fuskarsa a d'aure babu alamun wasan da ya saba mata yace "mene ne matsalarki da yasa kika ce baza ki sake zuwa skul ba?" A shagwab'e tace "to ba sune ba duk sai su dunga yin magana da turanci" yace "ke kuma turancin ne ba kya so,right?" Ta gyad'a masa kai,ya sauke numfashi yace "ba ku da lesson teacher ne a gida?" Ta gyad'a kai tace "to su ba sun iya ba!" Girgiza kansa yayi yace "ok! Zanyi magana da Amaar,idan an nemo lesson teacher shi kenan?" Tayi saurin kallonsa za tayi magana ya katseta yace "ba na son k'orafi,lesson teacher ne matsalarki and na gama da wannan maganar" yana fad'an haka dan kada ta samu damar sake masa magana ya katse kiran,saurin kallon Ameerah tayi za ta fara mata masifa da sauri Ameerah ta fice tana mata dariya. Da dare Amaar ya shigo part d'in ya gansu zaune ita da Ameerah tana koya mata assignment d'in mathematics,ya zauna yana kallonsu idan Ameerah tayi sai Manar tace bata gane ba ta sake mata,Ameerah ta gaji tace "ke wallahi na gaji tun d'azu fa muke yi,amma wai baki gane ba,kawai kin k'i ki nutsu ni sai wahalar da ni kike yi" Amaar dai sai murmushi yake yi,ai fa nan itama Manar d'in ta mik'e cikin fushi tace "kada Allah yasa kiyi d'in baza'a je makarantar ba,daga yau na dena zuwan.." Karaf maganarta sai a kunnen Waleed dake shigowa,wani tsawar da ya mata yasa tayi saurin waigawa,ya kalleta yace "me kika ce?" Tayi shiru tana kallonsa,a tsawace yace "ba dake nake ba?" Zumb'uro masa baki tayi tace "ni fa bance komai ba" yace "really?" Ta k'i kallonsa saboda ta san ba gaskiya ta fad'a ba,idanunsa a kanta ya gyad'a kai yace "Ameerah tell me what really happened kafin na shigo" Ameerah tace "Yaya cewa tayi baza ta sake zuwa skul ba" yace "saboda me?" Ameerah ta kwashe yadda suka yi ta fad'a masa,ya gyad'a kai yace "good! Kada kije kin ji,ba ni za ki yima ba" daga haka bai sake ce mata k'ala ba ya nemi guri ya zauna fuskarsa babu alamun ya san yadda ake dariya,Dadda ta fito d'aki tana binsu da kallo tace "hayaniyar me kuke min kuma?" Waleed da hankalinsa ke kan TV yace "hayaniya kamar wasu k'ananun yara?" Tace "yo da meye ku Allah na tuba?" Wani murmushi yayi ya tashi zai fita ta rakasa da kallo bata ce sai dai komai ba har ya fita,Ameer ya kalli Manar yace "zo ki zauna k'anwata,muga assignment d'in" hararar Ameerah tayi ta k'arasa kusa da shi da littafin ta mik'a masa,ya karb'a yana dubawa ya d'ago ya kalleta yace "ke yanzu mene ne abun wahala a nan?" Tace "Yaya nifa yadda take yi min ne ban gane ba" yayi murmushi yace "ok! Ki maida hankali ki ga abunda zanyi,idan mun gama za kiyi da kanki" ta gyad'a kai tace "toh" tiryan² Amaar ya sake gwada mata yadda za tayi,kafin ma ya tambayeta ta gane tayi ihu tace "wallahi na fi gane naka Yaya" ya sake yin murmushi yace "oyah! Yi na gani idan kin gane da gaske" ta d'auki biro ta fara yi tana masa bayani kamar yadda yayi mata,tana gamawa yayi mata tafi yace "ashe dai akwai kan hankaline baki mayar ba" tayi dariya ta juya ta kalli Ameerah ta harareta tace "Yaya itama fa dan bata min kamar yadda kayi ba shi yasa ban gane ba" Ameerah tace "wallahi k'arya kike yadda yayi nima ai haka na miki" Manar ta harareta tace "Hummm! Ba wani nan" Ameerah tayi dariya ta tashi tace "ke kika sani gobe ai sai kisa Yaah Amaar d'in a jaka ku tafi skul tare" Manar tace "ehh za muje d'in ina ruwanki" gwalo Ameerah tayi mata tace "woooo! Slow leaner" haushi Manar taji ta tashi a fusace Ameerah tana ganin haka tasa gudu suka fara zagaye parlon,Amaar dake zaune yana danna wayarsa ya musu banza bai kulasu ba sai da suka dameshi ya musu tsawa,duka suka zube suna haki Manar sai hararar Ameerah take daga k'arshe tayi k'wafa tace "ai dai za mu had'u" Ameerah ta mata gwalo tace "mu had'u d'in na zane ki" dariya Manar ta fashe da tana nuna Ameerah tace "ni za ki daka? Lallai ma yarinya jikinki zai yi tsami na kama ki" wani kallo Amaar ya musu yace "baza ku min shiru da bakunanku a nan ba" suka yi tsit babu wadda ta sake cewa k'ala har ya fita. Ranar alhamis da yamma Amaar ya kaita islamiyyar su Ameerah,da yake tsarin makarantar alhamis da jumu'a da yamma,Saturday and Sunday kuma da safe shi ma dai da kyar aka kaita ajin su Ameerah saboda sunyi kusan izu 30,sai da malamin yaga tana kuka wiwi sannan yace a kaita amma idan yaga bata yi k'ok'ari ba a jarabawar k'arshen term za'a mayar da ita ajin k'asa tayi tsalle ta dire tace ta amince,ranar saturday da yamma lesson teacher da Azaan yasa a nemo mata ya fara zuwa,suna kan yin lesson Waleed ya shigo gidan,ya gansu ita da Ameerah zaune balcony d'in gidan Dadda ana musu lesson ya kallesu ya d'auke kansa ya wuce bai musu magana ba,sanda ya sake fitowa sun gama lesson teacher har ya tafi,cikin isa ya shiga parlon yayi sallama a k'asan mak'oshi,Ameerah dake kwance tana game da wayarta ta amsa,ya kalleta fuskarsa a d'aure yace ke "waye na ganku da shi?" Ameerah tace "lesson teacher d'inmu ne" ya kalleta da kyau yace "waye ya d'auka muku lesson teacher?" Tace "Yaa Azaan ne.." Wani kallo ya mata yace "Azaan?" Ta gyad'a masa kai "ina Manar?" Ya tambayeta fusakarsa a d'aure har ya fi na lokacin da ya shigo,a tsorace tace "tana ciki" wucewa yayi hanyar d'akin gadan²,Ameerah tana ganin haka bata tsaya shawara ba ta shafawa kanta lafiya ta bar gidan kafin ya juyo kanta. Manar ta fito band'aki d'aure da towel ta zauna bakin gado tana yatsina fuska,gaba d'aya bata jin dad'i,tun shigowarsu take jin kamar something is about to happen,tayi shiru tana tattab'a cikinta zuwa mararta da ta rasa gane asalin inda yake mata ciwo tsakanin gurare biyun Waleed ya bud'e k'ofar d'akin,footsteps d'insa da ta ji suka sa ta d'ago kanta a hankali ta bisa da kallo,cikin fushi bai ko kula da yanayinta ba ya fara mata fad'a "uban waye yace ma Azaan ya d'aukar muku lesson teacher?" Kawar da kanta tayi tak'i masa magana,haushin yadda ta masa yasa shi fizgota da k'arfi yana huci yace "ba magana nake maki ba za ki min shiru saboda kin raina ni?" Kuka ta fashe masa da shi ta fara ture shi,ya rik'eta sosai yana mata wani kallo yace "stay still kafin na gaura miki mari" da muryar kuka tace "ni ka kyale ni bani da lafiya" wani kallon karki raina ma kanki hankali ya mata kafin ya bud'e bakinsa yace "me yake damunki?" Hannu ta watsa tace "nima ban sani ba" ya mata kallon rainin hankali yace "baki sani ba?" Ta gyad'a masa kai tana share hawaye,ya tab'e baki yace "ke kika sani" fizge jikinta tayi za ta koma kan gadon ya rik'o arm d'inta da k'arfi sai da ta saki k'ara,cikin shagwab'a tace "Yaya meye haka wai?" Ya juyata ta fuskancesa yace "waye ya ce ma Azaan ya d'aukar muku lesson teacher?" Tace "to ni nace masa?" A fusace ya doke mata baki yace "amsan abunda na tambayeki kenan?" Sheshshek'ar kuka ta fara tace "ni wallahi ka kyale ni na kwanta" yace "idan nak'i fa?" Cikin kuka tace "zan fad'awa Dadda" sakinta yayi ya koma gefe yana kallonta yace "Oyah! Je ki fad'a mata" ta murgud'a masa baki ta koma ta zauna tana share hawaye,yayi k'wafa cikin kaushin murya yace "daga yau kar na k'ara ganinsa a gidan nan,idan ya zo gobe ku sanar masa ba kwa buk'ata,kin ji me nace?" Saurin d'ago kanta tayi ta kallesa tace "to saboda me?" Yace "ban sani ba" tab'e baki tayi cikin k'unk'uni tace "a'a wallahi ni dai muna so" a fusace ya mata tsawa yace "ba shawarar ki na nema ba,umarni na bayar" da muryar kuka tace "ni wallahi bazan ce ba" mamaki shimfid'e a fuskarsa yace "ni kike fad'ima haka?" Tace "to ba kai bane kace muce bama so" kansa ya gyad'a ya wuce yana fad'in "kada kuce kinji,ki bari na sake ganin ya zo kiga yadda zanyi da ke a gidan nan" yana gama fad'a ya wuce ya fita,k'unk'uni ta fara masa tana ganin ya tsaya kafin ya waigo da gudu ta shige toilet ta kulle k'ofar,ta jingina jikin k'ofar ta murgud'a baki tace "kuma baza'a ce d'in ba" ficewa yayi gaba d'aya daga gidan ransa a b'ace,ya wuce apartment d'insu yana shiga yayi sama,yayi knocking d'akin Aunty Ameerah da ta gudo nan ta b'uya ta yi zaton Manar ce ta biyota ta tashi tana fad'in "ke wallahi kar kizo ki shafan kashin kaji" ido biyu suka yi da Waleed dake tsaye gurin fuskarsa a d'aure ya watso mata tambayar "waye yace ma Azaan ya d'aukar muku lesson teacher?" Tambayar ne yasa tsoro ya kamata ta fara in'ina,ya mata tsawar da sai da hanjin cikinta suka juya a tsorace tace "Yaya nifa" ya mata tsawa yace "idan kika sake kika min k'arya jikinki zai yi tsami" hawaye suna sakkowa fuskarta tace "Yaya ba ni bace" a kausashe yace "waye?" Ta fara in'ina tace "yay... Ya shi ne fa ya d'aukar mana" yace "ko kuka ce masa kuna so ko?" Ta girgiza masa kai da sauri tace "a'a Yaya" ya d'aure fuskarsa yace "Uhn! Waye yace masa kuna so?" Tayi shiru tana matsa fingers d'inta ya mata tsawar da yasa Mama fitowa daga d'akinta ta tsaya bakin k'ofa tana kallonsu bata ce musu komai ba,Waleed yace "za ki fad'a min gaskiya ko sai jikinki yayi tsami?" Girgiza masa kai tayi da muryar kuka ta fara magana,ya mata tsawa yace "idan kika bari naga drop d'aya na hawaye a fuskarki sai na fasa miki jiki" ta dunga k'ik'k'ifta idanuwa tana mayar da su tace "Yaya wallahi ba mu muka ce masa muna so ba" yace "Uhn! Waye yace masa?" Tace "babu kowa" yace "k'arya kike.. Cikin biyu dole za'ayi d'aya,ko dai ke ko Manar wata ta fad'a masa" saurin girgiza masa