Sashe 149
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ina iliminka,hankali da tunaninka suka je? Ka manta da cewa sai ka yiwa mahaifanka biyayya za ka samu dacewa a gidan duniya da lahira? Ka manta cewa su ne mukullin shiga aljannarka?" Shiru yayi kansa a k'asa yana sauraren bayanin mother,tace "haba Waleed ya kai da nake yabonka sallah kake k'ok'arin kasa alwala.. Kada ka manta kai ne babba a duka yaran gidan nan,yanzu za ka so ganin kannenka su aikata wani d'abi'a mara kyau?" D'an girgiza kai yayi yace "a'a" tace "muddin ba ka son wani abu ya faru,ya zama dole akanka ka fara gyara kuskurenka,kome ya faru tsakaninka da mahaifiyarku kayi hak'uri ka manta da shi,ba'a fushi da iyaye ko me suka yi,sai dai akan sab'on Allah.. But don't look at what she has done for both of us please,even if she is still on her spectrum,kai dai ka kyautata mata ta yadda ita akankin kanta she should feel ashamed of her past deeds,ka gyara tsakaninka da ita please,kamar yanda Allah (S.W.T) yace a cikin suratul isra'a verse 23-24:"Bismillahir-rahmanir-rahiim.. Wa-k'adhaa rabbuka allaa ta'abudu illa iyyahu wabil walidaini ihsanaa,immaa yablughanna indakal kibari ahaduhuma aw kila humaa falaa tak'ul lahumaa uffin walaa tanharhuma wak'ul lahumaa k'aulan kariymaa,wakhfidh lahumaa janahazhulli minar rahmati wak'ur-rabbirhamhumaa kama rabbayaniy saghiraa.." Duk wannan na san ka sani,but ina k'ara tunatar da kai ne as the verses of the Holy Quran confirmed,such as verse 36 of surah an-nisa'i,verse 151 in surah Al'an'am,and verse 23 of Is-ra'i,and verse 14 in surah Lukman,and in several hadith of Bukhari and Muslim said that,the Messenger of Allah (pbuh) was asked:"Ayyul amaal afdhaal? He said:"Prayer on time,and then what? He says that,obedience to parents" in another hadith of Bukhari he says that:-"the Messenger of Allah (pbuh) was asked about the serious crimes? He said that:-"polytheism to Allah and disobedience to the parents",yana daga cikin parental right,k'aunar su/girmamasu/ciyar da su/tufafatar da su/yi musu ladabi da biyayya/yi musu addu'a/girmama y'an uwansu/their friends/establish good deeds with their names after their death,and do not forget that a ciki Ameen (3) da Annabi (S.A.W) ya amsa a lokacin yin khud'uba zai hau mambari har da wadda aka ce duk wanda ya riski iyayensa bai yi musu biyayyar da zai shiga Aljanna ba... Allah (s.w.t) ya tsine masa,and prophet said Ameen. So how do u think idan akace wani babban malami ya amsa maka addu'ah bare kuma prophet (S.AW)? Akwai hadith daga Annabi (S.A.W) inda yace:"Sab'awa iyaye yana daga cikin manya manyan zunubai,and ka sani maganar Annabi ba tatsuniya bace da za muyi tunanin za ace kurunk'us.. A wani hadith d'in Annabi yana cewa:"Ku bautawa Allah kada ku had'a wani da Allah kuma ku kyautatawa iyaye. An karbo daga Abu-Umamata (R.T.A) Hak'ik'a wani mutum yace:"Ya Manzon Allah,mene ne *HAK'K'IN IYAYE AKAN D'ANSU!?* Sai Manzon Allah (S.A.W) yace:Su ne *ALJANNARKA DA WUTAR KA."* If u obey ur parents u will be successful,but if u disobey them u perish and u are approaching to hellfire,Allah ka tsare mu baki d'aya.." D'an girgiza kai yayi cike da gamsuwa,yace "ameen.. Thank u mother for the reminder" ta girgiza masa kai tace "hakki ne akanmu mu sanar da ku a lokacin da kuke k'ok'arin kauce hanya,haka nan kuma akwai wannan hakkin akanku,matukar akan sanar da mu gaskiya ne" ya sake gyad'a kai yace "in sha Allah i'll visited her" tace "Allah ya bada iko" ya amsa yana kallon agogon dake d'aure a wrist d'insa,a hankali yace "mother zan wuce" tace "tou son Allah ya tsare hanya ya bada sa'a" yace "ameen mother,thank u,sai da safe" tace "Allah ya mayar da kai gida lafiya,ya bamu alkhairi" yace "ameen" then ya fita. A hanya yana tafiya shi kad'ai yake tunanin maganganun mother,tabbas ya san gaskiya ta fad'a masa,and dama mai sonka tsakani da Allah shi kad'ai zai ga kana aikata kuskure ya gyara maka,mak'iyi kuwa kullum cikin dakon yaga kayi ba dai² ba yake saboda ya samu abun magana akai ko ya maka dariya,ko sanda ya k'arasa gida yanayinsa kad'ai Manar ta kalla ta fahimci mother ta masa maganar,and da alamun nasara kuma,ta masa sannu da zuwa,ya amsa yana kallonta,sai dai bai ce mata komai ba har suka zo kwanciya,taga ya k'i sakin jikinsa da kyau tace "Master what happen to u?" D'an girgiza mata kai tayi ya lumshe idanunsa yace "nothing" ta dunga kallonsa ta kasa gasgata maganarsa na babu komai,sanda ta fara lalubosa kafin ya dawo nutsuwarsa...