Sashe 133
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin tsananin tashin hankali Waleed ya durk'usa gabanta hawaye suna zubowa idanunsa,kamar mai jin tsoron tab'ata ya kai hannu ya d'an tab'ata yace "hhhh.. Hey! Llll.. Lil.. Lilac!" Jin shiru kamar ba ta motsi ya sake cewa "Hey! Wake up.. Wake up pleaseee" kamar wanda akace ya kallo k'asanta yaga jini ya fara biyowa yana ma kansa hanya kamar wani watersheds,zaro idanunsa yayi cikin k'araji ya kira sunanta at the same time ya kai hannuwansa ya d'auketa yayi hanyar fita,Afiyah ta kalli Mama cikinta har wani juyawa yake yana bada sounds sanda ta gano jini kwance a inda Waleed ya d'auke Manar tace "na shiga uku" jikin Mama ya d'auki wani rawa ganin aika²r da suka yi,a fili tace kada dai ace sun kashe har Manar d'in,ita dai bata zo da niyyar su kashesu duka ba,cikin jikinta kawai suka zo su rabata da shi,Waleed da har ya saka k'afarsa waje hawaye sai sauka fuskarsa suke uncontrollable ya waiga yana kallon inda suke da wani kakkausan murya yace ma Afiyah "Before i get back,ki tabbatar kin bar min gidana,na sake ki saki uku.. If something happens to my wife or my kid na rantse da k'udirar ubangiji bazan bar duk wani mai hannu a ciki ba.. And then i would advise u to hide urself whenever u heard my name mentioned,saboda dole na karb'an mata hakkinta.." Yana gama fad'a bai k'ara kallonsu ba ya fice a gaggauce,ya sata a mota ya shiga ya tada motar jikinsa duk jini haka hanyar da ya biyo jini yayi layi,wani uban horn da ya dunga dannawa tun bai rufe motar ba,sanda ya firgita mai gadin gidan,yana bud'e masa yayi zooming off ya fice da mugun gudu,yana driving yana share hawaye kamar mace,even though Waleed yana cikin mutanen da Allah ya yisu masu dauriya da juriya,but ko yaya abu ya had'a da Manar sai kaga ya zama wani rago,abu kad'an yake sa shi kuka akanta,ikon Allah ya kaishi hospital d'insu,kafin ma ya k'arasa tuni ya yi waya da wani friend d'insa ya fad'a masa yana nan zuwa da patient,Dr Mahfouz ya bada umarnin a tanadar masa kayan aiki yana da emergency case,sanda Waleed yayi parking ya samu gado yana jiransa,bai ko tsaya gyara parking ba ya fito yana kokawar bud'e back seat nurses d'in da suka fito tarbarsa suma suna kici²n bud'ewa,ya samu dai ya bud'e ya d'aukota ya d'ora kan gadon,a gurguje suka wuce da ita ICU (intensive care unit),Waleed zai shiga Dr Mahfouz ya hanasa dan yanda ya gansa a birkice ya san babu abunda zai tsinana,yace yaje gida ya canja kayan jikinsa kafin su fito da ita,daga asibiti kai tsaye gidansu ya wuce,yayi parking ya fito ya nufi b'angaren Dadda,ko sallama baiba saboda wani karyewan da zuciyarsa ya sake yi,Dadda ta fito d'aki tana gyara d'aurin d'ankwalinta ta ga mutum tsaye tayi mitsi² da ido tace "wa nake gani kuma haka?" Waleed ya kasa tanka mata ya juya da sauri zai fita tace "tou ai dama idan ba kai d'in ba wa zanwa magana ya min banza" ko kula da yanayinsa bata yi ba,yana fitowa ya nufi b'angaren iyayensa,ya haura sama ya bud'e bedroom d'in Aunty,samunta yayi suna waya da Ameerah akan maganar bikin Amaar da ake shirye²,bai iya yin sallama ba sai hawayen da yake sake gogewa ya zauna kan kujeran gaban mirror,kallo d'aya Aunty tayi masa taji gabanta ya fad'i,da sauri suka yi sallama da Ameerah tace za su k'arasa maganar later,tana sauke wayar daga kunnenta tace "Waleed lafiya?" Ya d'ago a hankali ya bud'e bakinsa zai mata magana wasu hawayen da suka gangaro fuskarsa suka hanasa fad'an maganar,Aunty cikin tashin hankali tace "subhanallahi! Waleed me aka maka? Ina Manar? Kai da waye please ka sanar da ni?" Kuka sosai ya fashe da shi ya rufe fuskarsa da both palms d'insa,Aunty ta taso da sauri ta rik'o hannunsa ta sauke daga fuskar ita kam tana ganin tashin hankali,wai kamar Waleed shi ne ya shigo mata babu ko sallama kuma yake kuka haka,ta d'ago fuskarsa da wani irin rauni a maganarta tace "wani abu ne ya samu Manar d'in?" Kai kawai ya iya gyad'a mata da sauri kuma sai ya mik'e zai fita,Aunty tayi sauri ta rik'osa tace "tou taya zan san me yake faruwa baka fad'a min ba kuma?" Da kyar ya daure ya iya mata bayanin abunda ke faruwa "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Was the first word da ya zo bakinta tana tafe hannu da jinjina girman maganar,a gaggauce ta juya ta d'auki hijab da wayarta tace masa "muje da sauri" suka fito tare lokacin tana yiwa Abba waya tana fad'a masa za taje hospital Manar babu lafiya,Abba yace babu matsala ta dubata kafin ya baro office ya shigo,da suka fito tace yaje yayi wanka ya canja kayan jikinsa kafin ta yima Hjy Dadda bayani,idan ya gama ya jirasu a mota,da kyar ya yarda ya shiga d'akinsa na gidan,Aunty ta fita ta wuce b'angaren Dadda da sauri,tunda ya fito wanka ya d'auki wasu kayan yasa ya fito ya bud'e motarsa ya rasa me yake masa dad'i,yana zaune cikin motar ya had'a kansa da steering wheel yana sauke ajiyar zuciya da tunanin ko a wane hali take yanzun? Ya jiyo hayaniyar Dadda tana kururuwan "idan na yarda na kyalesu Allah ya d'au raina,shi kenan sun kashe min jika,Manar d'in ta mutu ko? Ku fad'a min gaskiya.." Sai kuma ta rushe da matsanancin kuka,Mother dai tunda Aunty ta fad'a mata maganar ta kasa magana sai Aunty ke bata baki tana cewa "kiyi hak'uri Hjy har muje muga halin da take ciki" sanda suka shiga ya d'ago idanuwansa da suka yi ja ya gaisar da mother,jikinta duk ya yi sanyi ta amsa tace "ya mai jiki?" Kasa amsawa yayi sai hawayen da ya goge dan gani ma yake kamar idan yace da sauk'i ya zalunci Manar d'in,sanda suka baro gidan motar ta yi shiru babu mai magana Dadda kad'ai take mita,idan tayi² sai kuma ta fara share hawaye tana rantsuwan duk abunda ya samu Manar baza ta yafe ba sai ta you k'aran mutum,shigar su hospital d'in bayan yayi parking sun fito suna shiga ward d'in ya yi dai² da lokacin da Dr Mahfouz ya fito neman Waleed,yana hangosa ya rik'o hannunsa da sauri yace "dama kai na fito nema,yi sauri muje" yace ma su Aunty yana zuwa yabi Dr Mahfouz office d'insa,a can Dr Mahfouz ya masa bayanin komai har miscarriage d'in da ta samu,and then due to koma wane irin matsala ne ya faru da yayi sanadiyyar zubewar cikin shi ya janyo mata dogon suma,but sun shawo kan matsalar sun wanko abunda bai k'arasa fita ba,sanda ya gama yi masa bayanin komai,wasu irin sababbin hawaye suka sake saukowa fuskar Waleed,tunaninsa ya tafi akan yanzu shi kenan sun masa asarar cikinsa? Ya fita kenan? Tunda Dr Mahfouz ya gama masa bayanin yake zaune ya kasa kwakwkwaran motsi,kawai ya rufe fuskarsa yana kuka mara sauti,Dr Mahfouz yana bashi hak'uri,sanda yayi mai isarsa kafin ya yiwa Dr Mahfouz godiya ya fita,bai ce da su Aunty komai ba ya wuce d'akin da take special room ne ita kad'ai,ya sameta kwance a kan gado kamar mataciyya hannunta ansa mata k'arin ruwa,sanda ya kalli k'irjinta yaga tana sauke numfashi kad'an² yayi wani ajiyar zuciya ya k'arasa bakin gadon ya zauna yana kallonta cike da tausayi,ya jima sosai a d'akin dan baima san adadin lokacin da ya shafe ba kafin aka bud'e k'ofar aka shigo,bai juya ya kallesu ba suka k'arasa shigowa tare da Dr Mahfouz ya mik'a masa takardan da yayi prescribing magungunanta,ya karb'a yana kallo a hankali,Dr Mahfouz ya masa Allah k'ara lafiya,shi kuma ya masa godiya tare da su Aunty then ya fita,d'akin yayi remaining silence saboda Dr Mahfouz ya fad'a musu ba'a son hayaniya a inda take,amma Dadda sai girgiza kai take fuskarta a d'aure. In less than an hour labari ya gama zagaya family,Ameerah da Azaan sun kira sun masa jajen abunda ya faru kafin su zo,dan tunda Aunty ta sanar da Ameerah take kuka,gani take kamar ita aka b'ararma da ciki,dole sai da Azaan ya lallasheta kafin tayi shiru,haka ko Raj Jarood da Rani Naheed sun kirasa,Rania kuwa dama cewa tayi k'afarsu k'afarta sai ta je Nigeria duba Manar,Mommella ma dai tana hanya tace da suka yi waya,dan ta san dole ayi zama na musamman akan case d'in,guraren maghreb Abba ya k'araso hospital d'in tare da Amaar,Dadda dai tana d'agowa ta kalli Abba sanda suke shigowa d'akin ta fashe da wani kuka tana fad'in "billahillaziiy yau mai rabani da Asama'u sai dai Allah'n da ya halliceni,amma wallahi bazan yarda a b'arar ma da jikata ciki a sata dogon suma ya tafi a banza ba,idan na yafe musu Allah tsine min albarka" Abba ya kasa hak'uri yace "wai me yake faruwa?" Saboda har lokacin Aunty bata yarda ya san asalin abunda ke faruwa ba,it was there ta bud'a baki za tayi magana Dadda tayi zaraf tace "kana jina kou Yaro?" Abba ya kalli Dadda ya gyad'a kai yace "ina ji Hjy" Dadda ta daddage kamar a gabanta akayi ta fara rattabowa Abba bayanin kaf abunda ya faru,Abba yayi shiru ya kasa magana sai kallon Manar dake kwance bata ma san inda kanta yake ba,ya gyad'a kai yana sauke ajiyar zuciya yace "Allah ya kyauta" wani kallo Dadda ta masa baki sake tace "ban gane hausan Allah ya kyauta ba? Me kake nufi Yaro?" Abba yace "tou Hjy idan ban ce haka ba me zance?" Tace "ai kawai ka sawwak'ewa wancan matar,Allah na tuba dama idan banda mutuncin Alh Na Abba me za'ayi da surukuwa irin Asama'u? Tou yanzu kuwa tunda Allah ya sa baya raye bare muji kunya ai shi kenan maganar kunya kuma ya k'are" Aunty dai kallon Dadda kawai take,lokacin Waleed ya bud'e k'ofa ya shigo jikinsa a sanyaye yana d'auke da wani basket guda biyu,sai trolley d'in kaya ya k'arasa ya ajiye ya gaisar da Dadda da su Aunty,suka gaisa da Amaar ya masa ya mai jiki,d'an ajiyar zuciya yayi idanuwansa akan Manar da har lokacin bata farfad'o ba yace "alhamdulillah!" Abba dai sai kallon Waleed yake sympathetically ganin yanda ya rame kamar shi ne a kwance a hospital d'in ba Manar ba,ya masa Allah ya kiyaye gaba,har guraren 9pm su Abba suna hospital d'in kafin suka fara shirin tafiya,nan