Sashe 152
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saurin biyo bayanta yayi yana tambayarta lafiya? Bata tsaya basa amsa ba ta nufi wani bedroom a nan k'asan,kusan tare suka shiga d'akin ta fad'a bathroom,tun bata k'arasa ba aman da take yunk'urinsa ya fara zubowa,ya k'arasa kusa da ita da sauri ya rik'eta,sanda ta amayar da kaf abunda ke cikinta kafin ya wanke mata baki da jikinta ya cire mata rigan ya d'auki towel ya d'aura mata,har wani hazo² take gani lokacin ya d'auketa suka fito,sama ya wuce da ita ya bud'e bedroom ya shiga ya kwantar da ita kan gado yana mata sannu,ita dai tunda ya kwantar da ita tayi shiru sai numfashin da take saukewa,ya zauna kusa da ita yana kallonta yace "kina jin wani abu ne?" Ta girgiza masa kanta a hankali tace "um'um! Babu abunda nake ji kawai jiri ne" yace "sannu! Allah kara sauk'i" zai mata magana wayarsa ya fara ring,ya kai hannunsa ya d'auko a aljihu,yana dubawa yaga Deejah ce take sake kiransa,d'an siririn tsaki yayi then ya d'auka ya kai kunne,da sauri Deejah dake kuka tace "Yaya baka zo ba kuma" yace "yeah! Yanzu zan zo,what happened?" Kasa magana tayi duk ta rud'e sai kuka kawai take yi,da sauri yace "I'm coming in sha Allah" ya fara katse wayar,ya kalli Manar dake kwance har lokacin idanunta a rufe ya mik'e yace "Lilac tashi mu tafi" d'an bud'e idanuwanta tayi tace "kaje ka dawo na ji sauk'i fa" wani kallo ya dunga mata yace "bazan yarda na tafi na barki ba,get up na shiryaki mu tafi" duk yanda ta so ya tafi ya kyaleta sanda taga ya dage akan bazai barta ba,dole ta tashi ta zauna tana kallonsa,ya bud'e press ya d'auko mata lightweight kaya,ya dawo yasa mata then suka fito yana rik'e da hannunta,da suka sauka downstairs,ya barta a parlor ya shiga kitchen ya had'a musu kayan breakfast d'in a basket ya d'auko ya fito,a kwance ya sameta a kan kujeran da ya zaunar da ita,ya dunga kallonta sanda ya k'arasa kusa da ita yace "tashi muje" d'an bud'e idanunta tayi ta kalleshi a wahale kafin ta fara k'ok'arin tashi,duk aman da tayi ya sa ta zama wata sai a hankali,ya dunga kallonta sanda suka fito,suka k'arasa parking space ya bud'e mata mota ta shiga,ya shiga yaga ta jinginar da kanta ta kulle idanunta kamar mai shirin yin bacci,yace "da haka kike so na tafi na barki?" Ta d'an bud'e idanunta ta kallesa tayi murmushi k'arfin hali bata dai ce komai ba,ganin yanda tayi ko magana ma ta kasa yasa ya kwantar mata da seat d'in then ya tada motar suka tafi. A hanya babu mai magana har suka k'arasa gidan,yayi horn get keeper ya bud'e masa ya wuce ciki yana d'aga masa hannu,yana yin parking ya d'an juya yana kallonta kafin ya bud'e motar zai fita,ta bud'e idonta a hankali da suka fara canjawa saboda baccin da ta fara,ya zagaya side d'inta ya bud'e mata yana kallonta,ta sauko k'afarta a hankali ta mik'e,da sauri ta koma ta zauna tana rik'e kanta,yayi saurin sunkuyawa kanta yace "what happened?" Bata d'ago ba tace masa "jiri nake gani" ya mata sannu kafin yace "let me help u" ya janye hannun rigarsa ya d'auketa,ya tura murfin da k'afa ya rufe then ya nufi b'angaren Dadda,da ya shiga bai ga Dadda ba ya kwantar da ita kan kujera yana kallonta yace "I'm coming,okay?" Ta gyad'a masa kai ya juya ya fita,sanda ya kawo mata basket da ya had'a musu kayan breakfast ya ajiye ya had'a mata komai yace "kiyi breakfast in zuwa" tace "okay!" Ya fita ya wuce b'angaren Mother,da yayi knocking yaji shiru ya wuce b'angarensu,yana bud'e k'ofa Dadda ya fara hangowa tana share fuska,gabansa ya fara fad'uwa,a haka ya daure ya k'arasa shiga yayi sallama a hankali kamar yana jin tsoro,yana sake bin occupants d'in parlon da kallo,Aunty da Mother suka amsa masa da fuskar damuwa,ya shiga ya zauna ya gaishesu,Dadda dai bata amsa ba sai kukan da ta sake kecewa da shi,ya kalli Aunty jikinsa a sanyaye yace "me yake faruwa?" Aunty dai kallonsa take ta kasa magana,kana ganin idanuwanta za ka san ta ci kuka har ta godema Allah,Dadda ta d'aga murya tana share hawaye tace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Um!³" sai gyad'a kai take ta kasa cewa komai,Waleed ya sake tambayar lafiya? Dadda ta fyace hanci tace "ai kai dai Mamman muna cikin gagarumin tashin hankali wallahi" yace "tashin hankali akan me?" Tace "iiiihhh! Idan ba tashin hankali ba me za'a kira wannan abu da ya faru? Irin wannan babban masifa da Halima ta d'auko ma kanta" jikinsa har tsuma yake yace "ki min bayani dan Allah,na kasa gane me kike nufi?" Dadda har da gyara zama tayi tace "tou ni dai dama kaje ka d'auko uwar taku,tazo taga abunda y'ay'an so suka aikata" ya fesar da wani iska yace "ni kink'i ki min bayani,kin tsaya rarraba magana" Dadda dai daga haka ta k'i ce masa komai,sanda ya fusata kawai ya mik'e ya nufi sama,ya tura k'ofar bedroom d'insu Deejah yayi sallama a ciki,Deejah ta d'ago da sauri jin maganarsa,suna had'a ido ta kece da wani kuka mai ban tausayi,ya shiga yana kallonta a d'an tsorace,kafin yayi magana idanuwansa suka gano masa jariri kwance cikin zani an nad'esa fuskarsa a waje,kyakykyawan gaske kamar jinin larabawa,idanuwansa kamar za su fad'o ya dunga kallon jaririn dake bacci,kamar wanda aka sarewa k'afafu ya dunga tafiya ya nufi yaron,ya tsaya daf da shi jikinsa was vibrate,ya nuna yaron yace "wannan fa a ina aka samosa?" Deejah sai kuka take ta kasa magana,wani tsawar da ya mata yasa ta nutsuwa,ba ita kad'ai ba hatta Diyanah dake toilet sai da kayan cikinta suka hautsina tsabar tsoro,ta dafe k'irjinta wasu hawaye suna saukowa fuskarta,taji ya sake ma Deejah tsawa yace "ba dake nake ba kika min shiru?" Jikinta yana b'ari tace "Yaya ba nawa bane fa" wani zaro idanuwansa yayi yace "na waye?" Tace "Diyanah!" Saurin matsawa yayi ya jingina da bango yana fad'in "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. allahumma ajirnii fiiy musibatii wa'aklufnii khairan minha" Deejah ta rik'e kanta sai kuka take,da sauri ya sake matsawa kusa da yaron ya zuba masa idanu,ya kai hannunsa yayi sauri ya d'aukesa,wasu irin hawaye masu d'umi suna saukowa fuskarsa,ya jima sosai yana kallon yaron kafin ya ajiyesa ya fita,Diyanah tana jin fitarsa ta bud'e k'ofar ta fito,da ya sauka downstairs bai iya yima kowa magana ba ya fita daga gidan ya wuce b'angaren Dadda,ya samu Manar kwance tana bacci ko abincin bata ci ba,yanda ya ajiye mata haka ya tarar da shi,kasa k'arasawa kusa da ita yayi ya juya ya fita da sauri,ya tsaya balcony ya kira Mama a waya,a hankali yace tazo gida yanzu inji Dadda tana son ganinta,ta dunga tambayarsa lafiya,yak'i fad'a mata yace kawai shima haka tace masa ya kirata amma bata fad'a masa dalilin ba,duk da jikin Mama ya bata ba lafiya ba,ta daure tace tana hanya in sha Allah yanzu,ya katse wayar yana sauke numfashi,then ya juya ya koma parlon. Kafin yamma maganar ya isa kunnen duk wanda ya dace ya sani,Mommella,Amaar,Azaan,tare da Ameerah da Rania har sun sauka k'asar,Mama ma tuni ta zo aka labarta mata abunda ya faru,suka kuma gani da idanuwansu,Ameerah dai babu hawaye ko d'is a fuskarta dan a lokacin da suke zaune parlon Dadda ma da taga Manar tana kuka,kallonta kawai ta dunga yi kafin ta tab'e baki,tun da taji abunda ya faru ta d'agama kanta hankali,Ameerah da ta gaji da kallonta tace "dan Allah malama ki mana shiru haka,haba da Allah ke yanzu har kin manta abunda suka dunga fad'a akanki? Shi ne kuma za ki damu kanki? Wane magana ne basu ce ba sanda Hjy ta d'aukeki kuka je Saudi? Cewa fa suka dunga yi karuwanci tasa kiyi,ta fake da neman kud'i ko har kin manta?" Karaf maganar ya sauka kunnen Dadda da Mommella da suke shigowa side d'in,Mommella ta kunduma wani zagin da basu tab'a jin ta yi ba,ta shigo a fusace tana kallon Ameerah tace "me yasa baki fad'amin ba tun lokacin da akayi?" Ameerah tace "Mommella lokacin fa tun da suka dawo ne akayi" Mommella cikin tsananin b'acin rai tace "ko yaushe ne akayi ma,da na san da wannan maganar ai wallahi yau da saina maidawa Hjy Asama'u martani.. Har mu za ta kalla ta fad'ama wannan maganar? Uban meye bamu sani ba kan irin abun kunyar da k'anwarta da uwarta suka yi,a hakan kuma aka so lik'ama d'an uwana Allah ya tsaresa" Dadda dai zaro idanu tayi tana kallon Ameerah nan take ta kece da sabon kuka tace "amma dai wannan y'a kin cuce ni da baki sanar min ba tun farko,ai da ban b'ata hawayena ba a banza.. Amma ko yanzu lokaci bai k'ure ba,wallahi saina maidawa Asama'u martani.." Ta juya da sauri ta fita,kamar za ta fad'i ta nufi b'angaren su Aunty. Tana shiga ta fara kwaloma Mama kira, tun daga downstairsMama dai kuka kawai take ta saka Diyanah a gaba da jaririn,gaba d'aya ma ta kasa kallonta,Dadda ta b'anko k'ofar d'akin ta shiga,tana nuna Mama da hannu tace "amma ke dai wannan² mata sai Allah ya mana sakayya tsakanina dake" Aunty da ta biyo bayan Dadda ta fara ba ta hak'uri,Dadda tace "anya Fatima kin san irin sharrin da matar nan tayi min kuwa? Ashe k'aryar da ta zauna tana gindayawa da munafurci kenan a bayan idanuwana tana cewa na d'auki Manar na kaita karuwanci!" "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Was the first word da yazo bakin Aunty ta dunga kallon Dadda,trying hard not to believe,Aunty tace "a ina kika ji wannan maganar Hjy?" Dadda tace "wallahi³ kinji dai na maki rantsuwa ta fad'i maganar nan,idan k'arya nake mata kuma ga ta nan ki tambayeta" Aunty ta dunga girgiza kai tace "amma kuma Hjy sai yau maganar zai taso?" Dadda tana yiwa Aunty wani kallo ta hak'ik'ance tace "iiiihhh! Tou yauma d'in ba kamawa yayi ba aka tadosa dan mayar da martani" Aunty tayi shiru bata k'ara magana ba,Dadda ta juya ta fara mita,tace "alhamdulillahi! Ni dai na San kou yanzu na godema Allah da yasa Manar Bata d'auko min abun kunya ba har na aurar da ita" Mama ta sunkuyar da kai k'asa kunya kamar zaisa ta nutse a gurin,Dadda ta gama zazzaga fad'anta ta tafi. Sanda su Abba suka shigo gidan