← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 184

Sashe 19

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar wanda za ta tashi sama saboda saurin da take ta dunga ratsa compound d'in tana tafe tana zabga mita,ta tsaya balcony tana knocking kamar za ta b'alle k'ofar apartment d'in,Ruqayya mai aikin gidan ta bud'e mata,tana ganinta ta fara gaisar da ita da girmamawa,fuskar Dadda a tsuke ta amsa ta wuceta fuu,tun kafin ta k'arasa parlon take kwaloma Abba dake zaune kira "Yaro!" Abba yayi saurin waiwayawa ya kalleta yana sakin fuskarsa yace "sannu da zuwa Hjy" tace "yawwa" ta tsaya a tsaye tana k'arema parlon da occupants d'in cikinsa kallo,Mama ta had'e rai kamar wanda taga mutuwarta da kyar ta daure tace "sannu da zuwa Hjy" sakin baki Dadda tayi tana kallonta kamar wanda akayi pausing d'inta,for about 3 minutes tana haka then tayi mitsi² da idanu tace "ni dai yau ina ganin gulma iri²" d'auke kai Mama tayi saurin yi bata sake magana ba sanin a ko wane irin lokaci Dadda za ta iya tsigaleta yasa ta yima su Deejah alamar su bar gurin sanin,da sauri suka mik'e suka wuce sama,Abba yace "Hjy bismillah ki zauna" saurin girgiza kai tayi tace "um'um! Da ka ganni nan ba zama ya kawo ni ba,k'aran d'anka dai na sake kawo maka" Abba bai iya kallon fuskarta ba ya zubawa guri d'aya idanu yace "wanne daga ciki?" Da sauri Dadda ta kallesa tace "yo wa kake tunanin nake nufi idan ba Mamman ba? Kaima kamar baka san wanda zan kawo maka k'aransa ba?" Gyara zamansa Abba yayi yace "wani abu ya sake yi miki?" Dadda ta fara matsar idanu tace "yo akwai ranar banza da bazai je ya sani magana ba?" Abba yayi ajiyar numfashi yace "ki zauna bari na kirasa" zaunawa Dadda tayi tana girgiza k'afa,tana d'agowa za tayi magana suka had'a ido da Mama,ta tsuke fuska ta d'auke kanta ta fara mita,shi dai Abba bai ce mata komai ba yana ta gwada kiran Waleed,sai da ya masa kira ya kai biyar duka ba ya tafiya,then akace masa wayar a kashe yake,ya d'ago kansa ya d'an kalli direction d'in Dadda yace "Hjy ina ga sai dai mu bari zuwa da safe idan ya shigo" wani kallo Dadda tayi masa a fusace tace "ban gane mu bari har zuwa da safe ba? Anya ma ka kira shi kuwa?" Abba yace "na kira wayoyinsa duka a kashe" sakin baki tayi ta kafesa da idanunta,can kuma sai ta gyad'a kai tana mik'ewa tsaye tace "Allah kaimu,ai dai safiyar zai yi idanma tunaninka ka hanasa zuwa,zan dawo ne har sai na ga abunda ya turewa buzu nad'i" tana fad'a ta nufi k'ofa,Abba ya d'aga kai ya bita da kallo yace "sai da safe Hjy" bata tsaya amsa shi ba tayi ficewarta tana mita,da kallo Mama ta bita sanda ta fita ta tab'e baki k'asan ranta fari k'al dan murnan rashin samun Waleed da Abba baiyi ba a waya. A b'angaren Waleed kamar ya san abunda zai faru kenan yana fitowa daga apartment d'inta bai ma fara nufar hanyar gidansu ba ya shige motarsa ya bar gidan,wayoyinsa duka da ya san za'a iya nemansa ya danna su flight mode,ba shi ya dawo gidan ba sai after 10pm,yayi parking ya fito ya wuce cikin gidan,da sallama ya shiga though bai yi tsammanin samun mutum d'aya da yake ido biyu ba,Abba dake zaune parlon yana kallon news a Aljazeera ya amsa ba tare da ya juya ya kallesa ba,Waleed ya d'an kalli direction d'insa yanayin zamansa kad'ai yasa gabansa fad'uwa tun ma bai yi masa magana ba,ya danne ya k'arasa shiga ya gaishesa zai wuce sama Abba ya kirasa "Waleed!" Juyawa yayi at the same time yana amsawa,Abba yace "daga ina ka fito dai² lokacin nan?" Kansa a k'asa yace "Abba! Na je duba wani friend d'ina ne ya yi accident" d'ago kai Abba yayi ya kallesa yace "dubiyan ne kuma sai kamar wannan lokacin kake dawowa gida? Me yasa baka kwana can ba ka tayasa jinyar?" Shiru yayi da farko sai da Abba ya gama masa fad'a sannan yace "i'm very sorry Abba,amma ba yanzun na dawo ba,na tsaya bakin titi wajen mai kiosk" Abba yace "saboda ka san ka yi laifi a gida ko? Shi yasa ka bari sai yanzun ka shigo,tunaninka duka munyi bacci ko me?" Saukar da kansa ya sake yi,Abba ya gyad'a kai yace "kaje! Za mu had'u da safe,tunda kai ba ka jin magana,jeka Allah tashe mu lafiya.." Jikinsa a sanyaye ya yiwa Abba sallama ya wuce sama. Da safe as she say tun kafin 7am Dadda ta fito daga d'aki taga Manar kwance kan pray mat,har ta wuce ta dawo ta fara mata magana,Manar da ba nauyin bacci ne da ita ba ta bud'a idanunta tana kallon Dadda cike da b'acin rai,Dadda tace "yawwa sai ki had'a mana abun kari kafin naje mu gama na dawo ko?" Da sauri Manar ta tashi ta zauna tana kallonta tace "ina kuma za ki da safiyar nan? Ko fa tashi babu wanda yayi yanzu" wani kallo Dadda ta wurga mata a fusace tace "yo to ni ina ruwa na da babu wanda ya tashi,idan naje ni kuma ce miki aka yi barinsu zanyi suyi ta baccin asarar nan?" Manar tace "dan Allah dai ki bari har rana ya gama fitowa" wani kallo Dadda ta dunga mata a kaikaice kafin tayi gaba tana fad'in "ke dai wannan yarinya ina ga ba ki da hankali ko d'is,idan ba haka ba ina k'ok'arin k'watar hak'k'i na kice na zauna har rana yayi,saboda ga asararriya wacce uwata tace min jeki kya gani ko dan kin maida ni sakarya?" Har ta fita bata fasa mitar da take ba,Manar ta tab'e baki ta koma ta sake kwanciya abunta. Tana tafe tana mitar maganar da Manar tayi har ta tsaya balcony,za tayi knocking kenan Amaar ya bud'e k'ofa zai fito,yana ganinta yayi murmushi yace "Hjy Dadda barka da safiya" washe masa baki tayi tace "ka tashi lafiya?" Yace "alhamdulillah!" Tace "fita za'ayi ne?" Yace "a'a zanje na amshi sak'o bakin get na dawo" tace "aihooo! To sai ka dawo" har ya yi gaba tace "uban naku yana nan ko ya fita?" Bai tsaya ba yace "yana nan" gyad'a kai tayi ta juya ta shiga,bata tarar da kowa a parlon ba,ta zauna shiru tana jiran taga wani ya fito,kusan mintunanta sha biyar a gurin sai ga Abba ya fara sakkowa cikin shirin fita office yaga mutum zaune ya k'arasa,fuskarsa cike da mamaki ya dunga kallon Dadda kafin yayi magana "Hjy" Dadda dake zaune gyangyad'i ya fara d'aukarta tayi firgigit ta farka tana ganin Abba tayi salati,Abba dai sai binta yake da kallon mamaki,ya daure yace "Hjy ba dai a nan kika kwana ba?" Tace "a'a ni kuwa ya za'ayi nazo na kwana nan da girma na? Sammako dai nayo kada d'an banzan ya fice baka masa fad'a ba" Abba ya gyad'a kai yace "bari na kirasa" da sauri Dadda tace "ya dawo gidan ne?" Abba yace "Ehh! Ya dawo tun dare" baki sake Dadda ta dunga kallon Abba tace "kuma amma baka sa an kirawo ni ba tun daren?" Abba yace "bari dai nayi dama sai da safe muje har can gidan mu sameki,saboda bai dace kun fara bacci mu tashe ku ba" da sauri Dadda ta katsesa tace "ku same ni ko dai ku fice tunda ga shi har ka gama shirinka za ka fita,ba don Allah yasa na ganka ba da shi kenan ka gudu ka cuceni ni" murmushi Abba yayi cikin zolaya yace "Hjy da na yi niyyar fita ai baza ki san na tafi ba" tace "Iiiiiihhh! Saboda me ba zan sani ba?" Yace "ko da na fito yanzun bacci na sameki kina yi fa" wani kallo ta masa tace "a'a mutuwa dai kaga ina yi" murmushi ya sake yi yace "bari na taso shi" tace "toh ko kai fa" ya wuce sama yana sakin murmushin halin Dadda,bakin k'ofar d'akin Waleed ya tsaya yayi knocking,Waleed da fitowarsa wanka kenan yana shiryawa yace "who's there?" Abba yace "sai ka bud'e za ka gani" shiru yayi yana tunanin me zai kawo Abba d'akinsa kuma a dai² lokacin,ya daure bayan yaje gaban press ya d'auko jallabiya mai short hand ya zura ya k'araso ya bud'e k'ofar,kallonsa Abba ya dunga yi kafin ya juya yace "follow me" a bayan ya biyosa suka sakko,tun daga nesa yake kallon Dadda suna k'arasawa ya d'aure fuska yace "ina kwana" a fusace tace "bazan amsa ba" fakar idon Abba yayi ya d'age mata shoulders had'e da tab'e baki,ya nemi guri ya zauna yana gaisar da Abba,ya amsa yana kallonsa kafin yayi magana Dadda tayi wuf tace "yawwa yanzu naji batu.. Yaro tunda Allah yasa ka taso d'an ban zan a gaba maza ka tambayesa laifin da na masa yake zuwa yayi min d'iban albarka ko da yaushe!" Kallonsa Abba yayi yace "me ya faru tsakaninku!" Waleed dake kallon Dadda ta gefen ido yace "nothing Abba" saurin katseshi Abba yayi yace "don't tell me nothing.." Wani kallo Dadda ta musu fuskarta a d'aure tace "a'a! Ban gane wannan yare da kuke ba,ya za ku sani gaba ku juya baki kuna magana,ko dai kuyi hausa ko kuma kuyi larabci,amma dai wannan shegen yaren da babu dad'i ni ba na sonsa gaskiya kuyi wanda nake ji tun iyaye da kakanni.." Kallon Waleed Abba yayi yace "da kai nake magana ka min shiru" Waleed yace "babu komai Abba" Abba da ya kafesa da ido yace "babu komai za ta kawo k'aranka?" Da sauri Dadda tace "kuji min munafukin yaro? Dama abunda kace kenan dan kada naji? To Allah ya toni asirinka" ta juya tana kallon Abba tace "tunda bazai fad'a ba ni ai sai na zayyana maka abunda ya faru ko?" Abba ya gyad'a kai,kaf Dadda ta kwashe abunda akayi da wanda ma ba'ayi ba ta fad'awa Abba,Amaar dake dawowa bayan ya karb'o sak'on ya bud'e k'ofa,tun bai k'arasa shiga ba ya fara jiyo maganar Dadda tana fad'in "yo k'arya zan maka da girmana? Ba'a yi haka ba?" Wani kallon gefen idanu Waleed yayi mata bai ce komai ba,Abba ya zuba masa idanu sai kallonsa yake bai ce komai ba,Dadda tace "ina fad'a maka Yaro d'an nan na-ka bai ko ji tsoron Allah ba bare ya tuna ni na haifi ubansa ya daddage ya dunga surfa min masifa,ta inda
Chapter 19 · 0% Book details