← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 184

Sashe 61

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tasallah dai bata kuma cewa komai ba duk mitar da Dadda take ta yi mata shiru kamar ba ta nan,Azaan ya mik'e tsaye yace "Dadi sai da safe.." Da sauri ta kallesa tana washe masa baki tace "to Mamman Allah tashe mu lafiya" ya fita da sauri,Amaar ya bi bayansa. Kai tsaye parking space ya nufa,yana rik'e da hannunta ya bud'e back seat ya jefata ya rufe ya bud'e front ya shiga ya tada motar ya fice daga gidan da mugun gudu,can k'arshen street d'in ya kai yayi parking,da yake gurin babu lampposts saboda incomplete buildings da suke gurin sosai yake da duhu,ya kashe fitilun motar idan ba kana kusa da su ba baza ka san a kunne motar yake ba,ya bud'e ya fita ya shiga back seat jikinsa har wani tsuma yake tsabar b'acin rai yayi locking motar,Manar dai sai kuka take kanta a tsakiyar thighs d'inta,a hankali ya kwantar da kansa jikin seat ya kulle idanunsa,for about 5 minutes ya kasa ce mata komai sai da ya gaji dan kansa ya kai hannu kan shoulders d'inta zai kamota ta fizge ta koma jikin k'ofar motar tana sharar k'walla,yayi shiru ya kasa ce mata komai sai ajiyar zuciya yake saukewa,a hankali cikin sanyin jiki yace "ki bar kukan nan muyi magana please" da muryar kuka tace "ni ka mayar da ni gida" ya gyad'a kansa yace "zan mayar da ke,but before then kiyi shiru magana nake so muyi" tace "ni bazan yi magana da kai ba" yace "really?" Ta gyad'a masa kai tace "ni dai ka mayar da ni gida,me za ka fad'a min?" Yace "me yasa bakya jin magana ne? Kin fi so kina b'ata min rai ko?" Ta d'ago idanunta da sauri ta zuba masa su,though ba ta ganinsa clearly amma tana iya ganin shade d'insa kuma tana jinsa,ta zumb'uro baki tace "ni to me nayi maka?" Yace "maganar me kuke da Azaan d'azun?" Tace "kamar ya?" Yace "kamar yadda kika ji na tambayeki!" Tab'e baki tayi tace "babu komai" yace "k'arya kike" da wani muryar shagwab'a tace "ni to me nace masa?" Yace "kada ki rainawa kanki hankali,kina tunanin ban ji me kuke fad'a ba? Ke y'ar kamarki da ke har kin san cewa namiji kina sonsa?" Gwalo idanu tayi,yace "ko ba haka kika ce ba?" Tayi shiru bata amsa shi ba,tsawa ya mata yace "ba dake nake ba?" Ta zumb'uro baki tace "to ai ba ni na fara cewa ba,shi ne ya fad'a" cike da kishi yace "sai kika amsa masa da kina sonsa kema ko?" Kallonsa ta dunga yi tace "to ni Yaya me zance?" Yace "why not baki ce ba kya sonsa ba?" Wani kallo ta bisa da shi tace "Yaya ka san me kace kuwa?" Yace "I knew.." Ta dunga kallonsa ta kasa d'auke idanunta,yace "bar kallona" ta zumb'uro baki tace "ni yaushe ma na kalleka?" Yace "daga yau idan ya sake fad'a kice ba kya sonsa" da sauri tace "ni wallahi bazan ce ba,naga ai kaima da nace ka fasa aurenta cewa kayi no way,nima no way.." Dank'ota yayi bai bari ta kai k'arshe ba numfashinsa yana sauka kan fuskarta yace "ba shawarar ki na nema ba umarni na bayar,idan kika sake na k'ara ganinki tare da shi zan b'ata miki rai,kin ji me nace?" Murgud'a masa baki tayi tace "ni wallahi Yaya ina sonsa,akan me za kayi aurenka ni ka hana ni yi?" A fusace da wani murya yace "saboda ina son ki dole na tsareki,na hanaki kula kowa!" Tamkar saukar aradu haka taji kalamansa sun dirar mata,cikin dak'ik'u kad'an komai ya tsaya mata cak,har ji take kamar jijiyoyin dake kaiwa jikinta sak'o duk sun tsinke,da kyar ta iya furta "Yaya ka san me kace?" Yace "na sani" tace "ni Yaya ba ka so na" yace "ina son ki" tace "Yaya ka manta wanda kace min kana so? Ni ba ni bace" ya zuba mata idanunsa yana kallonta ya sassauta muryarsa yace "me yasa kika ce haka?" Tace "ai na san haka ne,kuma ko bayan haka ma ni Yaya Azaan nake so" wani mahaukacin cafka ya kaiwa bakinta,ta dunga k'ok'arin k'wacewa amma bai bari hakan ya faru ba,sai da ya tabbatar ta ji a jikinta kafin ya saketa ya koma ya kwantar da kamsa jikin seat yana sauke numfashi ba k'aramin tayarwa da kansa hankali yayi ba,ya dafe kansa yana jin rashin kyautawarsa gareta,ita kam a nata gefen gaba d'aya wani mugun shork ta shiga,she can't believe wai Yayan nata ne yayi kissing d'inta kamar haka,duka ya gama kashe mata jiki,tunda ta samu ya saketa ta koma gefe take jin jikinta yana mata wani irin yamm kamar dai unseen k'wari suke bin jikinta,wani irin kuka ne ya sake k'wace mata for the second time,yayi saurin rik'ota ya k'ank'ameta shi kansa bai san ya akayi hakan ta faru ba,kawai ji yayi kamar daga sama yana kissing d'inta,ya rik'eta sosai wasu hawaye suna zubo masa,da muryar nadama yace "please Manar forgive me.. I don't actually know me yayi crossing mind d'ina har ya janyo haka ya faru,forgive me please,this was not intentional" kamar wanda ake fitarwa da rai ta dunga kai masa duka tana kuka,tace "ka mayar da ni gida ni.. Ba na son ka kuma" ya runtse idanunsa da k'arfi yana jin inama ace haka bai faru ba tsakaninsu,da kyar ya iya control d'inta ta rage kukan da take,ya fita ya koma gaba jikinsa duk ya yi sanyi ya tada motar,da reverse ya dawo dai² get d'in yayi horn get keeper ya bud'e masa,ya shiga yayi parking yana kallonta ta mirror jikinsa a mugun sanyaye yace "shi kenan ki je gida Manar,but ina so ki sa a ranki duk abunda ya same ni u don't have to blame anyone but ur self.." Yana fad'an haka yayi unlocking motar,da sauri ta bud'e ta fita,tana ganinta waje ta kwasa a guje,bata tsaya ko ina ba sai gidan mother. Azaan dake tsaye gaban window bedroom d'in Amaar ya ga sanda take fitowa daga motar Waleed ya zubawa gurin ido har sanda ta shige apartment d'in mother,Amaar dake zaune yace "ka manta da maganar Baba Tasallah brother,ko bayan haka me yasa kake zargin Waleed yana son Manar?" Wani juyawa Azaan yayi ya kalli Amaar yace "haba Amaar ya kake tunanin zan d'auki maganarka? Idan ka ce Waleed ba son Manar yake ba,think baka tab'a kallon al'amarin a dai² ba.. Kada ka manta tun muna yara ba jituwa muke ba,kuma duk hakan ya samo asali ne a sanadiyyar Manar,why not bazan ce Waleed yana sonta ba? Kai baka tab'a ganin kishin da yake idonsa ba,gaba d'aya he don't want see me around her,ba ya k'aunata ba ya k'aunar ganina da ita tun sanda muke yara,ya kake tunanin zan d'auki al'amarinsa ehhh?" Runtse idanunsa Amaar yayi yace "calm down Azaan,na fad'a maka Waleed ba son Manar yake ba" a fusace Azaan yace "k'arya ne wannan Amaar,idan ba ya sonta me ta masa yanzun da ya fita da ita? Me yasa kuma ba ya son ganinmu tare?" Amaar yace "ko ma dai mene ne ka manta kawai,kaima za ka tabbatar da hakan nan gaba" wani murmushi Azaan yayi yace "okay! But yana da kyau kaje ka fara tambayar d'an uwanka,for sure zai tabbatar maka maganar da na fad'a" Amaar ya bud'e baki zai yi magana,Azaan ya dakatar da shi da sauri yace "enough Amaar.. Ka fara tabbatar da maganar daga garesa kafin ka fad'amin wani maganar.." Yana fad'in haka ya wuce ya barshi nan zaune,ya shige bathroom zuciyarsa sai azalzalarsa take. Tunda ta shige bedroom d'inta na b'angarensu take rafzar kuka,she can't even believe wai Yaya yana sonta,how comes? Tun farkon bai tab'a fad'a mata ba sai yanzu? Kuma ko bayan haka ita fa Azaan take so,kuma shima ta tabbatar yana sonta,dan haka tai ta k'aryata zuciyarta akan Yaya ba sonta yake ba kawai ya fad'a mata haka ne saboda wani dalilinsa,sanda taji alamun ana tab'a kofar da sauri ta mik'e ta shige bathroom ta kunna shower,mother da ta lek'o yi mata magana tana jin alamun saukar ruwa tace "Manar idan kin fito Daddy na son ganinki" ta juya ta fita,jingina tayi da k'ofar bathroom d'in a hankali tana sauke ajiyar zuciya,da kyar ta tattara sauran nutsuwarta ta cire kayanta da take jin k'amshin Waleed ajikinsu ta watsa loundry,ta k'arasa k'asan shower ta tsaya ruwa yana sauka jikinta tana sauke ajiyar zuciya mai k'arfi,sosai ta sab'e jikinta kafin ta fito ta saka nightwears d'inta riga da wando ta d'auki k'aton hijab tasa akai then ta fita amsa kiran Daddy'nta..
Chapter 61 · 0% Book details