Sashe 7
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ganin a gaban mahaifiyarta ne bai mata komai ba,ya bawa mother hak'uri,sanda ta nuna masa babu komai² ya wuce,yayi mata sallama ya tashi zai fita,a baya Manar ta biyosa,suna fitowa balcony ya tsaya ta d'aga kai tana kallonsa kamar za ta sake sakin wani kukan,fuskarsa a had'e yana mata wani kallo yace "ke! Babu wanda ya isa da ke? Ba ki da wanda za su fad'a miki kiji ko?" Zumb'uro baki tayi tak'i cewa komai,ya mata tsawa yace "ba dake nake ba?" Shiru tayi ta k'i cewa komai sai zumb'ura masa bakin da tayi tana k'unk'uni k'asa² ba'a ji,a fusace ya kawo mata mari tayi saurin matsawa gefe tana saake zumb'ura masa baki tace "kayi hak'uri" ransa ya mugun b'aci da abunda tayi ya dunga kallonta ya kasa magana sai can da aka jima yace "surely zan gyara miki zama a gidan nan,y'ar k'arama dake baza'a fad'a miki kiji ba,wa kika haifa a nan? Waye sa'anki?" Tace "Babu kowa" yace "babu wanda kika haifa,dole ne a fad'a miki kiji,duk ranan da na sake ganin an miki fad'a kin kwasa kinje kin fad'a mata wallahi sai na sab'a miki,za ki sha mamakina ranan,ki bar ganin kina zuwa kusa da ni zane ki zanyi sai na fasa miki jiki.." Wani kuka ta kece da shi,ya mata tsawa "hey! Hey!! Be quite before i slap u" tsit tayi ya matso inda take fuskarsa babu alamun dariya yace "idan kika kuskura kika je kika fad'a mata na yi miki wani abu,billah kika bari muka had'u sai na zaneki,kin ji me nace?" Gyad'a masa kai tayi saurin yi tana zumb'ura baki,ya maka mata harara kafin ya juya ya bar gurin,k'asa² sanda ta tabbatar ya tafi tace "Allah ya isa na" then ta nufi apartment d'in tana cika,a parlor ta tarar da su yana zaune kan kujera yana danna waya,ta harari inda yake tana zumb'ura baki ta wuce hanyar bedroom,Dadda dake bawa Ameerah labarin zamansu a Saudiyya ta bita da kallo sanda taga wucewarta kamar za ta tashi sama ta kyab'e baki tace "ita kuma wannan matar ko ita da wa take k'unci ohoo?" Bai d'ago ba yace "ni ne na mata fad'a ko ban isa ba?" Kallonsa Dadda tayi saurin yi tace "akan me? Wani gagarumin laifin tayi?" Yana ci gaba da danna wayarsa yace "sai tayi laifi za'a mata fad'a?" Tsuke fuska Dadda tayi saurin yi tace "ka ga Mamman ba na son haka,ba na son sa ido,ina ruwanka da ita da za ka saka ta gaba eh?" D'ago idanunsa yayi ya mata wani kallo yace "wai me yasa kike haka ne? Shi kenan duk abunda yarinyar nan za tayi shi ne dai² baza tayi mara kyau a tsawatar mata ba? Abunda kike yi kin kyauta kenan ko shi ne dai² a na-ki ganin?" Sororo Dadda tayi ta zuba masa idanuta ta kasa masa magana,Waleed yace "Tambayarki nake abunda ya kamata ki koya mata kenan? Haka kike so taje gidan mutane tana yi?" Wani tsuke fuska tayi tace "wane gidan mutanen za taje?" Yace "kina nufin baza tayi aure bane? Ko wani ya fad'a miki za ku dawwama tare?" Washe hakor'in makkanta tayi tace "Aihooo! Ashe gidan aure kake magana.. Sha kuruminka k'afata k'afar jikata bazan tab'a yarda ta tafi ita kad'ai ba,haka kawai ina nan zaune aje a cutar min da ita na shiga uku" kallonta Waleed ya dunga yi yace "shi wanda zai auretan mahaukaci ne amma?" Da sauri ta maka masa wani kallo tace "A'uzhubillahi! Kuji min wani magana gurin wannan mutumi.. Aniya bil'aniya,aniyarka ta bika,in sha Allahu ba dai jikata ba,bakinka ya sari d'anyen kashi.. Sai dai ka auri mahaukaciya amma ba dai *ZAINAB* d'ita ba.. Sha Allahu mijin da takwarata za ta aura kaf zuri'ar mu ma babu wanda za ta samu kamarsa.." Kallonta kawai ya tsayi ba tare da ya sake cewa komai ba ya mik'e ya kama hanyar fita,ta rakasa da mugun harara tace "Allah raka taki gona,ni dama ban nemeka ba,kai ka kawo kanka ehee! Mutumi babu abunda ya iya sai fatan tsiya!" Tsayawa yayi gurin ya juyo ya kalleta yace "haka kika ce kou?" A fusace tace "na fad'a ubana sai a san yadda za'ayi da ni" gyad'a kai yayi ya juya yace "za ki neme ni da kanki" a fusace tace "ni wallahi babu abunda zaisa na nemeka,dama magana kake zuwa ka sa ni,dan ka daina zuwa dubunka za su zo" fita yayi da sauri fuskar nan a d'aure ya wuce zai nufi apartment d'insu,tun bai k'arasa barin part d'in ba ya hangota tsaye jikin window daga ita sai wani gantalallen singlet na mata fari kar da ya kama jikinta,bisa tsautsayi idanunsa suka sauka kan k'irjinta da suka d'an tasa nipples d'inta da suke nan erected sun fito sunyi rad'a² a jikin rigar babu alamun akwai wani rigar a ciki,saurin kawar da kansa yayi zai wuce ta kwalo masa kira "Yaya!" Cak ya tsayawa a gurin ba tare da ya sake kallon direction d'inta ba yace "what happened?" Zumb'uro masa baki tayi ta rungume hannuwanta a k'irji tace "kayi hak'uri!" Bai ce mata komai ba ya ci gaba da tafiya,a shagwab'e ta d'aga murya tace "to ai dai na ce ka yi hak'uri" wani mugun kallo ya waiga ya mata,idanunta suka yi rau² da gudu ta juya ta bar gurin,yana jiyo sautin kukanta ya tab'e baki ya wuce ya bar gurin da sauri. Da dare lokacin ya shigo gidan,yayi parking ya fito ya rufe motar ya wuce apartment d'insu,yana shirin shiga part d'in ya jiyo sautin kukan mahaifiyarsa da sauri ya k'arasa shiga,ganin da yayi ba ita kad'ai bace a parlon yayi sallama,mutumin dake zaune wanda a shekaru zai kai 65 years ya d'ago ya amsa masa,ganin mahaifinsa a gurin yasa shi sauke ajiyar zuciya ya k'arasa a hankali ya zauna ya gaisar da shi,cikin kuka Mama dake zaune gaban mutumin tace "ni dai gaskiya Alh ka yima matarka magana,babu ruwanta da ni a gidan nan,tayi harkarta nayi tawa,dama ba shiga shirginsu nake ba" numfashi ya sauke yace "na tambayeki abunda ya had'a ku kink'i fad'a,me kike so nayi miki kuma?" Matsar hawaye ta ci gaba da yi tace "ai ba sai na fad'a maka abunda ya had'a mu za kayi hukunci ba,ni dai kawai ka raba ni da ita" idanunsa akanta bai bar kallonta ba yace "alright! Sai a bar maganar tunda ba kya so na san abunda ya had'a ku ko?" Da sauri tace "kamar ya abarshi? Baza ka mata magana ba kenan kake nufi?" Yace "haka nake tunani" ranta a mugun b'ace tana kallonsa da idanunta da suka yi ja tace "ai dama na san haka za kace,duk abunda zai faru a gidan nan ba ka tab'a goyon baya na,kullum akayi abu ni ce mara gaskiya,kamar wata jaka ni ake laftawa laifi ko da ba ni nayi ba" wani murmushi mutumin yayi kafin ya kallo gefen da Waleed yake zaune kansa a k'asa yace "Waleed je ka kira min Aunty'n ku" amsawa yayi ya tashi ya nufi sama,yayi knocking bedroom d'in Aunty ta bud'e k'ofar,tana ganinsa tace "Waleed! Shigo mana" d'an murmushi yayi yace "dama.. Abba ne yace na kira ki" kallonsa tayi with suspicion tace "ni kuma?" Ya gyad'a kai yace "sure" gyad'a kai tayi tace "alright! I'm coming" ta koma ciki shi kuma ya sauka k'asa,ba'a jima ba sosai ta sakko tun kafin ta k'arasa inda suke take kallon Mama dake matsar idanu,ta d'auke kai ta zauna tace "ga ni Alhaji" Abba ya kalleta yace "me ya had'a ki da Hjy Asama'u?" Murmushi Aunty tayi tana kallon Abba tace "wani abu tace maka ya had'a mu?" Abba ya girgiza kai yace "i'm jist asking me ya had'a ku?" wani murmushi Aunty tayi tace "ni kam babu abunda ya had'a ni da ita,sai dai ban sani ba ko ita ka tambayeta kaji" saurin kallonta Mama tayi tace "wallahi k'arya take Alhaji" d'aga mata hannu Abba yayi saurin yi yace "ban zo kanki ba" tayi shiru tana kallonsa ranta a mugun b'ace,Abba dake kallon Aunty yace "Hjy Fatima!" Aunty tace "na'am!" Yace "i want to know me ya had'a ki da Hjy Asama'u" jimm Aunty tayi kamar baza ta ce komai ba then tace "Alhaji ni dai da ka bar maganar nan,gaba d'aya banga amfanin taso da abunda aka riga aka yisa ya wuce ba" Abba yace "ko me yasa kike so a bar maganar?" Kafin Aunty tayi magana,Mama tayi zaraf tace "saboda ta san itace mara gaskiya mana" wani kallo Abba ya juyo yana mata yace "ban ce kimin shiru ba?" Mama tayi kicin-kicin cikin jin haushi tace "amma Alhaji wannan ai ba adalci bane,kace za ka hana ni magana" Abba yace "alright! Ci gaba" ya nad'e hannunsa ya zuba mata idanu,tace "maganar gaskiya bai kamata kace za ka hana ni fad'ar abunda yazo baki na ba" Abba dake saurarenta yace "shi ne ai na baki dama ki ci gaba kou?" Tace "haka kawai ina zaune parlor ta zo ta dunga gaya min magana,ni dai ka ja mata kunne ta bar shiga harkata" kallonta Aunty ta dunga yi tsabar mamaki ma ya hanata cewa komai,sai da Abba ya kalleta yace "ke nake sauraro" numfashi ta sauke har lokacin bata yi niyyar fad'awa Abba abunda ya faru ba tace "dan Allah Alhaji kayi hak'uri ka bar maganar nan,ni wallahi ban san maganar da yasa kace nazo ba kenan" Abba yace "da kin sani baza ki zo ba?" Ta girgiza kai tace "a'a! Ya ya ma za'ayi nace bazan zo ba?" Abba yace "ke nake sauraro ki sanar min abunda ya faru" kan babu yadda za tayi ganin Abba ya dage ta fara rattabo masa jawabin kaf abunda ya faru,ran Abba ya b'aci sosai ya dunga yiwa Mama wani kallo cike da takaici yace "wato rashin zaman lafiya kike son haifar min a cikin gidana kenan? Shi yasa sai kika ga bari ki fara tara na da maganar,ina tambayarki kuma da kika san ba ki da gaskiya kika k'i fad'a" Mama tayi kicin-kicin tak'i cewa komai,ran Abba a b'ace ya dunga mata fad'a ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba sanda yayi mata tass kafin yace ta tashi ta bashi guri,b'ata rai tayi tace "ai sai dai kace matarka ta tashi kuma tunda ka san ranar girki nane yau"