Sashe 181
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
kamata muji inda maganar yake" Manar kam wani zaro idanu tayi ganin yana kashe mata ido d'aya yana mata kiss a b'oye,lokaci d'aya kwakwalwarta ta fassaro mata abunda yake nufi,da sauri ta d'auke kai tana turo baki,yayi murmushi yana kallonta yayi bismillah ya fara cin abincinsa yana sakin murmushi,yana sauraren hiran da suke,har ya gama yayi hamdala,Deejah tazo ta kwashe kayan ta kai kitchen,Manar ta biyota a baya tana harararsa ganin wani mayen kallo da yake mata,Deejah ta had'a kayan za ta wanke Manar ta matso za ta tayata suyi tare,Deejah tace "a'a dan Allah kije ki huta,naga girkinma ke kika yi fa" Manar tayi dariya tace "tou bak'on guri na zo da za ki hana ni yin aiki?" Ta fizge sponge d'in da sauri tace "go gefe madam" da k'arfi Deejah tace "Mama dan Allah ki kira Manar ta kyaleni nayi wanke²n,kin ganta wai lallai ita za tayi" da sauri Mama ta tashi ta nufi kitchen d'in tana cewa "haba Manar ki barta tayi mana,kin hana mu yin girki kuma wanke²n ma baza ki barshi tayi ba?" Manar tana murmushi tace "ki kyaleta kawai Mama na kusa gamawa ma ai kayan ba su da yawa" babu yanda Mama bata yi da itaba amma ta k'i bari,dole ta koma parlor har suka fito,lokacin ana kiran isha'a Waleed ya mik'e zaije sallah yace "get set Lily idan na dawo za mu tafi" ta gyad'a masa kai tace "tou! A dawo lafiya" ya fita yana cewa "Allah sa.." Sanda aka idar da sallah ya nufo gidan,suma lokacin duk sun idar da sallah suna dai zaune parlon suna hira,yayi sallama ya shigo,suka amsa masa,yana tsayen bai zauna ba yace "muje kada muyi dare" Deejah ta tashi tana d'aukan veil d'inta,Manar kam da kyar ta tashi,Waleed yace "Mama za mu koma,sai mun sake dawowa kuma" Mama dake kallonsu cike da alhinin barinta da za suyi,wuni d'ayan da suka mata jinsa take wani so special,saboda yau ta wuni cikin jama'a kuma tana jin gwarancin jikokinta,ba kad'anba kasancearsu tare ya d'auke mata kewa,ta kalli Waleed tace "ayyahh! Waleed baza ka barminsu su kwanarmin ba?" Da sauri ya juya ya kalli Manar kwakwalwarsa tana kawo masa tunanin ko dai bayan fitarsa sunyi maganar da Mama,sai kuma dai ya d'auke kai yace "za mu dai sake zuwa Mama yanzu bamu zo da shirin kwana ba" ta d'an gyad'a kai tace "tou shi kenan.. Na gode sosai,a gaisar da mutanen gidan idan kunje" ya amsa yayi gaba,suka biyosa a baya,sanda ya fita ya bud'e motar yace "oops! Mama na manta da sak'onki a mota" tace "sak'ona in ji wa?" Yana murmushi yace "mazajenki" tayi murmushi itama tace "a'a ni mijina d'aya,da shi kad'ai nake auren tunda shi ya yarda da ni" Manar tayi murmushi tace "ayyahh! Mama shima Alhassan wata rana da kansa zai zo inda kike" Mama ta gyad'a kai tace "tou Allah sa,ya ara mana tsawon rai" suka amsa kafin suka yi mata sallama suka shiga mota,Deejah tace "Mama sai an kwana biyu zan tambayi Abba nazo nayi kwanaki" Mama tace "tou Allah sa Abban naku ya amince" Deejah tace "in sha Allah ma zai bari" suka k'ara mata sallama,bayan Waleed ya shigar mata siyayyan da ya mata d'azu da ya fita,tana ta masa godiya da sawa rayuwarsu da yaransu albarka suka tafi tana d'aga musu hannu cike da kewarsu,direct sanda suka fara sauke Deejah a gida basu tsaya shiga ba suka wuce gida,yayi parking ya fito rungume da Alhassan,ya bud'e mata k'ofar ta fito d'auke da Alhussain suka k'arasa ciki,washe gari suka ma Diyanah zuwan bazata,Manar,Ameerah,Rania da Deejah,sai mazajensu da suka kaisu,ai kam ta ji dad'in ganinsu sosai,ta rasa inda za ta ajiyesu,haka surukanta ma sai nan² suke da su,sun sha hira sosai,a nan Dr Mahfouz sai satan kallon Deejah yake,sanda za su tafi kaf iyalin gidan Alh Baffanyo suka musu rakiya gurin motocinsu,Dr Mahfouz yana ma Waleed tsiya,Waleed yace "ka dai bini a sannu,idan ba haka na zan maka tsiyan da yafi wannan.. Ka san kuma zan iya" da sauri Dr Mahfouz yace "afuwan! Babban Yaya" Azaan yace "a'a nifa ban gane wani babban Yaya ba,muma duka ai yayye ne! Ko dai ko dai?" Akayi dariya,Amaar yace "atou! Ni dama tun d'azun na gano akwai wata a k'asa,shiru dai kawai nayi" a nan ma sanda suka tab'a barkwanci kafin suka yi sallama suka tafi. Wasa² sai da suka samu kimanin sati biyu a Nigeria,sun yi zumunci sosai,ko gidan Mama ma bayan wancan zuwan da suka mata sun koma,sun mata kwana biyu saboda alk'awarin da ya mata,cikin satinsu na uku suka fara shirin komawa India,ranan da za su tafi sanda mutanen gidan suka ji ina ma su zauna kada su koma,but haka nan dai akayi bankwana jirginsu ya mik'a. Bayan watanni biyu da komawarsu soyayya tsakanin Dr Mahfouz da Deejah ba'a cewa komai,dan lamarin da gaske ne,a lokacin kuma tuni ma har an saka ranar aurensu,Diyanah kam babu wanda ya kaita farin cikin za su zauna gida d'aya da y'ar uwarta,ita gaba d'aya ma hidiman ya had'e mata,Afreen k'anwarsu Dr Mahfouz ma da ba ta k'asar tuni ta iso da yaranta biyu maza,nan suka fad'a hidiman bikin babban Yayan nasu,su Manar kam sa cikin satin bikin suka k'araso,nan suka had'u basa nan basa can,tun da aka shiga satin biki,hidima kawai ake a duka b'angarorin biyu,ranan da suka yi dinner kaf d'insu anko suka sha na red d'in lace,mazan suka zuba farin shadda an masu aiki da bak'in zare,ya subhanallah kada kuso ganin wannan family da suka had'e kai,abun har ba'a cewa komai,Mama ma dai ta zo da kyar dan mugun kunyar shiga cikinsu Mother take,su kam a garesu sun nuna mata komai ya wuce,a haka aka yi biki aka watse,satin Deejah d'aya a d'akinta Alh Baffanyo ya shirya musu zuwa honeymoon,lokacin da suka dawo kuma bayan sun huta,ya kirasu yace ya sallamesu kowa ya d'auki matarsa su koma gidajensu tunda yanzun ya fahimci Farhan ya jima da yin hankali,ya daina yawon dare,daga gurin aiki sai gida,ko abokan ma tuni ya watsar da su,matarsa da d'ansa sune abokansa,idan ya taso ya d'auki little Daddy yana masa wasa suna dariya. Su Manar kam sai da suka k'ara sati d'aya bayan bikin su Deejah kafin suka koma India.