← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 184

Sashe 36

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsawa ta masa,idanunta gaba d'aya sun kad'a sunyi jaa tace "ka rufe min bakinka a nan gurin.. Kada ka kuskura ka furta ko wane irin kalma" kamar yadda ta buk'ata yayi shiru ya sunkuyar da kansa k'asa,cikin masifa tace "waye ya ba-ta wayar?" Bai d'ago kansa ba yace "Azaan" ta dunga kallonsa tace "wane Azaan d'in? Mutumin da ba ya k'asar" ya d'ago da sauri ya kalleta zai yi magana a fusace tace "ka san ba zan tab'a yarda ba ko?" Yace "why not Mom?" Cikin masifa tace "ni za ka rainawa hankali Waleed? Munafurcinka kuma wanne ne ban sani ba?" Girgiza mata kai yake yace "Mama!" Ta sake masa tsawa here ta dunga sirfa masa ruwan bala'i sanda tayi iya yinta ta gaji tace "billahillaziiy idan baka mayar da hankalinka jikinka ba za mu samu sab'ani da kai" shi dai ya mata shiru,tsabar mamakinta gaba d'aya ya kasa ko bata hak'uri dan kanta da ta gaji tace "tunda ka iya siya mata kace ba kai bane su kuma k'annenka fa?" Ya d'ago yace "Mama na fad'a miki fa ni ban siya mata waya ba" tace "dallah rufe min baki ni za kawa k'arya?" Ya d'auke kansa ransa a b'ace,tace "ni dai na fad'a maka ka fita harkar yarinyar nan,idan ba haka ba kuma duk abunda ya faru kayi kuka da kanka" ta juya ta nufi k'ofa tana ci gaba da bambamin fad'a,ajiyar zuciya ya dunga saukewa bayan fitarta,ya rik'e kansa da yake jin yana sarawa da hannuwansa biyu,ya jima a zaune yana tunani kafin ya tashi ya rage kayan jikinsa ya shiga bathroom,yana fitowa ya shirya ya d'auki keys d'insa yayi waje fuskarsa babu annuri,kafin ya k'arasa parking space Manar ta fito daga gidan tana tafiya kamar tana counting steps sanye cikin wani red colour d'in riga,hancinta ta mak'ala masa ring shaped d'inta,kallonta ya tsaya yi musamman lips d'inta da suka sha red colour chapstick,ya lumshe idanunsa a hankali yana jin wani irin yanayi yana mamaye jikinsa,yana bud'ewa suka had'a ido ta zumb'uro masa baki ba tare da ta kulasa ba,harara ya maka mata ya d'auke kansa ya k'arasa gurin motar ya bud'e zai shiga,gigitaccen ihun da tayi yasa shi fasawa da sauri ya saki murfin motar ya nufi inda take,ganinta a durk'ushe ya kai hannu zai tab'ata tayi sauri ta d'ago,mamakin abunda ya gani yasa shi zuba mata idanu ya kasa mata magana,ta tashi tsaye tana karkad'e rigarta ya d'aga kai ya kalleta,a hankali ta fara tafiya tana barin kusa da shi ta masa gwalo ta fashe da wani dariya,sakin baki yayi yana kallonta ya kasa mata magana,haushin raina masa hankalin da tayi yasa shi mik'ewa a fusace zai rik'ota,tana gama karantar abunda yake niyyar yi ta fella a guje,da yaga haka kawai sai ya tsaya kallonta yadda take gudun k'afafunta kamar za su tsinke ya fi komai basa dariya,ya dunga kallonta daga inda yake yana darawa,sanda ta kai balcony kafin ta tsaya tana maida numfashi,kamar ance ta waiga ta hangoshi a inda ta barshi,ya nad'e hannuwansa a k'irji yana kallonta,ta bud'e idanunta sosai tana kallonsa,dariya yayi mata wanda ya bayyana hak'oransa,ta dunga kallonsa daga inda take cike da mamaki duk a tunaninta ya biyota ne,yayi mata wink kafin ya juya ya shige motarsa ya bar gidan yana sakin murmushi. Har ya fita bata matsa daga gurin ba,Ameerah ta k'araso gurin ganinta tsaye ta zubawa get idanu ta dafa shoulder ta kafin tayi mata magana Manar da hankalinta baya tare da ita jin an tab'ata ta daddage ta kwalla k'ara,Ameerah ta koma baya da sauri a tsorace tace "dallah meye na ihun,ni ce fa kika wani b'are baki" harararta Manar ta juya tayi tace "kuma sai ki tsorata ni?" Ameerah ta kyalkyale da dariya tace "ke dai kin cika tsoro wallahi daga d'an tab'akin nan har kin tsorata" ta harareta tace "ban sani ba" ta wuce ta shige gidan. Tuk'i yake bayan fitarsa amma da ya tuna gudunta sai ya kad'a kai yayi murmushi,cike da nishad'i ya tsaya wani eatry ya siya abunda yake buk'ata ya fito,a hanya ya sake tsayawa wani bakery ya siya ice creams then ya juya kan motarsa ya nufi gida,yayi parking yana kallon apartment d'in yayi murmushi ya fito ya d'auko ledojin ya wuce part d'in Dadda,a parlor ya jiyo maganarsu ya k'arasa ya bud'e k'ofar yayi sallama,Manar tana jinsa ta waiga suka had'a ido,da sauri tayi zumbur ta mik'e za ta kwasa a guje,ya d'aure fuska ya d'auke kansa,ta dunga kallonsa sanda ya k'arasa shigowa ya zauna yana kallon Dadda da tak'i kallonsa,yayi wani murmushi cike da tsokana yace "wai fushi kike yi har yanzu?" Kamar mai jira tace "a'a dariya nake" ya gyad'a kai yace "ohooo! Thought fushi kika yi na rarrasheki" wani kallo ta masa tak'i tankasa,ya tashi ya nufi kitchen ya d'auko plates biyu ya dawo,ta d'aga kai ta bisa da kallo tana jira taga me zai yi,ya koma inda ya taso ya d'auki d'aya a cikin ledojin da ya shigo da su ya ciro coil paper da akayi wrapping ya warware,Manar dake tsaye ta zuba masa ido tana jira taga me zai fito da shi,kamar ya san me take ya d'ago ya had'e rai,ta b'ata rai itama ta wani d'auke kai kamar ba kallonsa take ba,yayi murmushi a ciki ya bud'e,zazzafan k'amshi ya cika gurin,ya juye ya ciro ice creams manya biyu daga d'ayan ledar da wani fura dake cikin roba shima,plate d'aya ya d'auka ya kai gaban Dadda da robar furan ya zauna yayi flexing legs d'insa ya d'auko yankan hanta d'aya yace "bud'e bakinki na baki" ta kalleshi ta kalli plate d'in hantar tayi murmushi tace "Allahu akbar.. Allah jik'an Malam ya masa rahama" Waleed yayi murmushi yace "ameen Hjy ta.." Tace "lokacin yana raye sai abunda nace ina son ci.. Dan wannan hantar kuwa ai sai na ture faranti" murmushi ya sake yi ya gyad'a kai yace "muci to sai ki ba-ni labari" tasa hannu ta fara ci,Manar dake tsaye ta tab'e baki ta juya za ta bar gurin Waleed ya kalleta ta gefen ido bai mata magana ba,sai da ta shige ya tab'e baki ya d'ago yace ma Dadda "ita wancan ba ta ci ne ta shige d'aki?" Dadda ta girgiza kai saboda dad'in dake hauramata cikin ka,sai da ta gama had'iye na bakinta tace "kai ma dai kamar wani baka san ba ta son hanta ba?" Shiru yayi ya zuba mata ido,ya d'aga girorinsa yace "Ohh! Na manta" ta ci gaba da cin abunta,sanda suka cinye ta d'auki fura ta kora,tana gamawa tayi hamdala tace "Allah maka albarka.. Yanzu da irin haka ne tsakaninmu har wani ma ya ji kanmu da kai?" Yayi murmushi ya koma kan kujera yace "saura labari na" tayi dariya tace "yanzu kuwa za ka ji su sai ka ce ya isa.." Labarin zamansu a Saudiyya ta fara masa tave "ai na fad'a maka zama Saudiyya ba dai dad'i ba.." Ya gyad'a kai yace "haba?" Tace "da gaske ma kuwa.. Komai baja-baja kake samunsa,shi yasa idan muka je harami babu abunda muke sai ibadah. Wata rana kawai muna cikin tafiya ba sai ga askar ba" yace "askar?" Tace "ehh! Kan kace me mutane sun fara gudu,radadada kowa sai gudu,ni dai ban san ya akayi ba kawai sai gani na nayi a gida ina mayar da numfashi,nake fad'a maka ban sani ba ma ko suma nayi a lokacin,ko wani ya kawo ni,na kalli Hjy Tasallah nace "wa ya kawo ni gida?" Y'ar kan uban yarinyar nan tana kallo na kawai sai ta kwashe da dariya,Hjy Tasallah tace "wa kuwa zai kawo ki idan ba k'afafun ki ba" na kalleta nace "aradun Allah bani iya dawowa gida da kaina" tace "to ai shi kenan tunda kinyi min musu" nake fad'a maka yarinyar nan ta zauna ta dunga min dariya,sai daga baya take fad'a min wai "Dadda kinyi rabin gudun ki a duniya" na tambayeta "wane gudu kuma Allah na tuba zan iya yi ni?" Tace "wallahi yau dai kinyi" nace "ni d'in?" Tace "ehh! Kinyi rabin gudunki dai" ni dai kamar zanyi kuka dan haushi nace "wai wane irin gudu ne nayi?" Kawai ta sake fashewa da dariya tace "rabin gudun famfalak'i mana" wai ashe da ina gudun ceton raina ne hijabina ya cika da iska.." Dariyar Amaar da Ameerah yasa Dadda juyawa ta kalli gurin da suke,ta gansu zaune kan kujera bata san yaushe suka shigo ba Ameerah har da kwanciya,Waleed kam tab'e baki yayi yace "kuma yanzun wannan labarin yayi miki kama da wanda nake so?" Ta kalleshi da sauri tace "yo kai dai ba labari kace na maka ba" yace " ba irin wannan nake so ba" tace "Iiiiiihhh! Wane iri kai d'in kake so?" Yace "mai dad'i dai haka" kallonsa ta dunga yi can ta tab'e baki tace "kai ni rabu da ni bacci nake ji,ku dai da ba'a raba ku da surutu sai kuje kuyi ta yi" wani murmushi yayi yace "ai biyana za kiyi" ta kalleshi tace "me na ci maka da zan biyaka?" Ya d'aga mata gira yace "nufinki nama da furan da na kawo miki a banza kika ci?" Tace "Iiiiiihhh! Daman biyanka kake nufin zanyi?" Yace "Uhn! Ke nufinki da bati kika ci?" Kamar za tayi kuka ta kalli Amaar tace "yanzu fisabilillahi d'an fodiyo dan wani cikinku ya siya min abu na ci sai kuma ace na biya? Dukiyarku ba ni da hak'k'i a cikinsa?" Amaar dai dariya kawai yake yi ya girgiza kai yace "a'a Hjy ta,ya ma za'ayi ace ki biya ko duka dukiyar kika cinye ai kin ci bulus" ta gyad'a kai tace "Uhn! Ka ji batu Malam" Waleed ya d'aure fuska yace "da gaske fa nake yi sai kin biya ni" ta kalleshi da sauri tace "to ba sai ka k'wata ba" yace "haka muka yi da ke?" Dadda ta hak'ik'ance tace "yo ko bamu yi ba da yanzu dai kam munyi,naci dubu sai ceto" murmushi yayi ya mik'e yace "za ki biya ni ne wani lokacin yanzu dai na yafe miki" tace "yo ko baka yafe ba ma yaya za kayi da ni?" Hanyar kitchen ya nufa ta bisa da kallo har ya tura k'ofar bata daina masa mita ba,Amaar ya kalleta yana sakin murmushi yace "a'a fa Hjy dan dai kawai ya ce ya yafe
Chapter 36 · 0% Book details