← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 180 OF 184

Sashe 180

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai kusan 1pm sannan suka bar gidan,sanda suka fara biyawa family house suka d'auki Deejah,kasancewar already Waleed yama Abba maganar zuwansu gurin Mama tare da Deejah,Abba ya amince masa,then suka wuce unguwar da Mama take,suna shiga line yayi parking dai² get d'in gidan,a hankali ya d'an juya ya kallesu ganin duk sun tsaya jiran yayi magana,ya bud'e k'ofar gefensa ba tare da ya kallesu ba yace "get down" ya mik'a hannu ya d'auki Alhassan dake binsa da kallo yana k'ananan kuka da mik'a masa hannu,sai da suka jira ya fara fita,lokaci d'aya suma suka bud'e suka fito suna kallon arean da yake very silent,shi ne a forefront sai Manar da Deejah da suke biye da shi,ya k'arasa jikin get d'in rungume da Alhassan yayi knocking,sai da ya sake nocking kafin suka jiyo muryan Mama na cewa "ana zuwa" wani sanyayyan murmushi Deejah tayi tana lumshe idanu,sanda Mama ta bud'e k'ofar ta d'an lek'o da son ganin waye,suka yi ido biyu da Waleed dake gaban k'ofar,Mama ta saki fuska tana kai hannu za ta karb'i Alhassan take musu sannu da hanya suka amsa,kamar yaron ya santa ya zuba mata idanu but kuma ya k'i zuwa,sai ma wani lafewar da ya k'ara yi a jikin Waleed,Mama ta bud'a baki tace "auu too! Baza ka zo gurina ba?" Deejah ta kyalkyale da dariya tace "Mama ai ba ya zuwa hannun mutane wannan,da dai Alhussain ne ko bai tab'a ganinki ba zai zo,amma wannan kou mu haka yake mana" Mama ta gyad'a kai tace "aatooo! Ya sha zamansa" sai ta mik'a hannu ta karb'i Alhussain,tare da ba su hanya tana fad'in "bismillah! Ku shigo" suka shiga suna yin sallama ta amsa musu,sai da suka shiga kafin ta biyosu a baya suka shiga parlor,Manar za ta zauna k'asa kan lallausan rug,Mama dake shigowa tace "haba Manar mene ne kuma zama k'asa,dan Allah tashi ki zauna sama kar ki b'ata kayanki" cikin jin kunya ta tashi ta zauna kan kujera,Mama tana ma Alhussain wasa tace "sannunku da hanya,kun sauka lafiya?" Suka amsa,Manar tace "ina wuni Mama,mun same ku lafiya?" Mama ta amsa da "lafiya lau alhamdulillah!" Sai satar kallon yadda Manar ta zama uwar mata take,tana tambayarta mutanen gida da yara,while a gefe d'aya sai kallon yanda Waleed ya zama,har wani special k'iba yayi jikinsa luff² kamar ka tab'asa jini ya fito,zara²n gashi a kwance a duka sassan jikinsa,sanda suka gaggaisa Mama ta mik'e ta kawo musu ruwa da lemo then abinci da ta shirya saboda zuwansu,kiran sallah dai ya sa Waleed bai zauna ba yace zaije sallah ya dawo,Mama tace "tou kai da kake bak'o ka san inda Masjeed d'in yake ne?" Yace "bazan rasa sani ba,idan na fita zan tambaya" daga haka ya kalli Manar da ido ya mata alaman sai ya dawo,ta masa murmushi ya juya ya fita,after an fito daga Masjeed ya dawo,yana yin sallama Mama tace "o'o! Kuma ka gane inda Masjeed d'in yake?" Yayi murmushi yace "tou Mama dama ai na fad'a miki" ta gyad'a kai tace "sannu da dawowa" ya amsata then ya koma ya zauna yana tasbihi,Mama ta kallesa tace "a zuba maka abincin?" Yace "ehh! Ba da yawa ba" tace "tou" sanda ya juya ya k'arema parlon kallo,yace "Mama ina suka shiga na ji gidan shiru kamar ke kad'ai ne" Mama tayi murmushi tace "sun shiga sallah ne" ya gyad'a kai ya gyara zamansa,yana cin abincin suka fito,suka masa barka da dawowa,ya gyad'a kai bai k'ara magana ba sai da ya gama,suka d'an fara hira jefi²,can wajen 3pm Azaan ya kirasa,sai da yayi murmushi kafin ya amsa kiran,Azaan yace "haba Malam ina ka shiga yau babu ko d'aga hannu" Waleed yace "wallahi munje gaida Mama ne" Azaan yace "kuma babu sanarwa,ko dan kada muce za muje?" Murmushi still yayi yace "not at all! Ban dai yi tunanin haka bane" Azaan ya gyad'a kai yace "alright! Sai yaushe za ku dawo kuma?" Waleed yace "maybe da dare" Azaan ya gyad'a kai yace "alright! Sai kun dawo,a gaishe da Mama" yace "zan fad'a mata in sha Allah" sanda ya tambayi yaransu kafin suka yi sallama,ba'a jiba sosai kuma ya mik'e yana d'aukan car keys d'insa yace "Mama zanje nan kusa na dawo" cikin barkwanci Mama tace "anya Waleed kai da kake bak'o,kada fa ka b'ata kasa mu daukan mayafi mu fita nemanka" Manar da Deejah suka kyalkyale da dariya,Manar na fad'in "ka ga Yaya kada kasa mu kuka bamu shirya ba" Deejah kam sai dariya take,yayi murmushi yana ma Manar wani kallon k'asan idanu yace "ni da k'asara za'a ce na b'ata cikinta,duka shekara nawa nayi bana nan? Na je nayi shekaru na dawo ban b'ata ba sai yanzu da y'an kwanaki nayi duka?" Manar tayi k'asa da murya tace "wancan zuwan daban,ka sani kou wani abu yasa yanzun ka iya b'acewa" shi dai murmushi kawai yayi bata san ya jita ba ya nufi hanyan fita,yana cewa "sai na dawo Mama" da ido yama Manar alamun ta zo,kwab'e fuska ta fara za ta masa musu,ya juya mata ido tare da nufar k'ofa ya fita da sauri yace "Lily zo nan" kamar wanda aka watsama ruwan k'ank'ara tsabar kunyan da ya sa ta ji,Mama da taga ba ta niyyar tashi tace "tashi mana daughter kuma,ko kunya na kike ji?" Da sauri ta tashi ta biyosa,dai² get ya tsaya ya juya yana kallonta,ta tsaya tana kallonsa tace "ga ni" matsowa yayi daf da ita yana kallonta yace "me ma kika ce yanzu?" Ta juya idanu tana kallonsa tace "yaushe?" Yace "kince sai dai in wani abu yasa nayi me?" Dariya ta kyalkyale da shi tace "auu! Wai ka ji dama?" Yace "ohoo!" Ya rik'ota jikinsa a hankali yana kallon lips d'inta yace "banga abunda zai sa na manta da identity na ba,sai dai kou kece za kisa ni mantawa" tayi murmushi tace "saboda me?" Yace "idan kina ba ni dad'i yanda ya kamata da wuri zan manta da ko ni waye ma bare wata k'asa" dariya ta kyalkyale da shi tace "kai Yaya! Amma tou ya akayi duk garan da ka d'iba a baya baisa ka manta ba idan haka ne?" Yana d'an squeezing fuskarsa yace "maybe saboda baki mayar da hankali bane lokacin amma yanzun idan mu duka muka yi aiki da guminmu sai kiga na manta" wani kallo ta masa tana rufe baki tace "duk abunda nayi a bayan kace wai ban yi ba" ya k'ara d'an tab'e baki yace "ai na fiki aikatuwa girl,kinyi but d'an kad'an ne ba da yawa ba" kallonsa ta dunga yi tana gyad'a kai tace "haka ma za kace?" Ya mata murmushi wanda ya k'ara masa kyau,kyawawan jerarrun hak'oransa farare tas da su suka bayyana,yace "oops! Ba haka nace ba" tayi kicin² tace "tou da me kake nufi? Ni sake ni na tafi" k'ara rungumeta yayi yana mata dariya mai d'an sauti yace "tsaya mana kiji sirri za muyi" tace "ni babu wani sirrin da za muyi,kayi tafiyarka sai ka dawo" da sauri yace "a'a za muyi mana juyo kiji na fad'a maki" a hankali ta d'an juyo da fuskarta tana kallonsa,ya zuba mata idanu kad'an yana kallonta,ganin haka yasa ta d'aga masa gira tace "ya akayi?" Yayi murmushi a hankali ya matso da fuskarsa,ji tayi kawai yayi grabbing lips d'inta yana sha,a d'an tsorace ta bud'a idanu tana son kwacewa,shi kam k'ara rik'ota yayi yana sucking lips d'inta,dan kansa ya gaji ya saketa,ta galla masa harara ta lashe lips d'inta tace "kai ko kunya baka ji a zo a ganmu?" Shoulders ya d'age yace "it's my property fa.. My halal,kema ga shi nan har lashe lips kike saboda zakin da kika ji" dariya ya bata ta girgiza kai tace "yawwa! Master nace please ko za ka barmu mu kwana biyu a nan?" Lokaci d'aya fara'ar fuskarsa ta d'auke yana kallonta yace "a ina?" Tace "a nan mana gurin Mama" da sauri ya girgiza mata kai yace "a'a!" Tace "pleaseee!" Kafin ta k'ara magana ya d'ora index finger sa akan lips d'inta da fad'in "shhhiii!" Dole tayi shiru tana jujjuya idanunta akansa,yace "na barku ku kwana a nan,ni kuma na kwana a ina?" Tace "Master tou ba sai ka koma gida ba kai" yana mata wani kallo yace "kou?" Ta gyad'a masa kai tace "ehh!" Ya gyad'a kai yace "mu bar maganar nan tsakaninmu" tace "saboda me?" Strictly yace "saboda bazai yiwu ba" kallonsa ta dunga yi fuskarta ta yi rau² tace "shi kenan tou" yace "jeki ciki zanje na dawo yanzu" tace "umhn! Allah tsare hanya" ya amsa mata da "ameen.." Ya juya ya fita,jikinta a sanyaye ta bisa da kallo,sanda ya fita ta d'an lek'o sai da taga ya bar line then ta koma ciki. Sai kusan 7pm ya dawo,bayan ya tsaya Masjeed ya yi sallan isha'a ya shigo gidan,ya tarar da Deejah da Manar sai hira suke akan zuwa gidan Diyanah,Mama kuma tana zaune kan rug tana gama yiwa Alhussain wanka tana ciccilasa sama yana b'ab'b'aka mata dariya,Alhassan sarkin k'ulafuci yana lik'e jikin Manar yana ma Mama dariya kamar shi takema wasan,Waleed dake shigowa yayi sallama,suka amsa suna masa sannu da zuwa,bayan ya zauna Mama tace "Deejah kawo ma Yayanku ruwa da abinci" da sauri Waleed yace "kawo min ruwa kad'ai" Mama tana maida hankalinta kansa tace "abincin fa?" Yana kallon Manar yace "ba na jin yunwa" tace "tou ai kuma tun rana fa ina tunanin rabonka da abinci kou?" Yace "Mmm!" Mama tace "ki had'o masa da abincin.. Idan baka ci ba ni da za ka barma nayi yaya da shi?" Yayi murmushi yace "tou ki sa kad'an" Mama tace "wani cin abinci kad'an,kou dai abincin nawa ne bai maka ba? Na ga ka fara tumbi ina tunanin kou abinci ka fara ci da yawa" Manar dake musu dariya tace "har yanzu Mama haka nan yake ba ya son cin abinci,sai dai kayan kwad'ayi" Mama ta bud'a idanu tace "tou! Ashe su suka hurasa yake hawa kaman farashin k'asarmu" Deejah dake fitowa kitchen tace "sharrinta ne Mama babu wani kayan kwad'ayin da yake ci" Waleed dake tankwashe k'afa sanda Deejah ta ajiye masa plate yace "thanks.." Then ya d'ago idanunsa ya sauke cikin na Manar yace "kika sani kou ita take ba ni kayan kwad'ayin nake ci a b'oye?" Mama tayi murmushi tace "atou! Akwai dai lauje cikin nad'i,ya
Chapter 180 · 0% Book details