← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 184

Sashe 39

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiru Waleed yayi yana tunanin maganar principal d'in kafin ya gyad'a kai yace "alright!" Manar dake gefe taji ya ce haka,though bata gane me yake nufi ba tayi ajiyar zuciya,duk abunda ake buk'ata shi ya biya,principal ta basu uniform da kayan karatunta,suka yima juna godiya,ta rakosu har premises d'in makarantar then suka yi sallama suka tafi,a hanya motar tayi shiru babu mai magana da d'an uwansa,ya kalleta yaga ta juya tana kallon hanya fuskarta a had'e,ya tab'e baki ya d'auke kansa,kamar wanda aka yiwa dole sai ya mata magana yace "me yake damunki?" Bata juyo ba tace "babu komai" idanunsa akan hanya yace "babu komai kike b'ata rai?" Ta masa shiru ta k'i magana,ya gyad'a kai yace "kin san ba na son iskancin nan ko?" Da sauri ta waiga tana kallonsa kamar za tayi kuka tace "ni to me nayi maka?" A fusace yace "ni zan miki magana kimin shiru bayan na san kina ji na?" Rau² idanunta suka yi ta zumb'uro masa baki tace "ni fa yunwa nake ji,ka dena min magana" burki yayi saurin takawa Manar da babu belt a jikinta kad'an kanta bai daki glass d'in motar na gaba ba yayi saurin fizgota,a tsorace ta fasa k'ara ta k'ank'ameshi,yayi tsaki ya turata ta zauna,yana mata wani kallo yace "ni za ki rainawa hankali kice min kina jin yunwa?" Kuka ne ya kufce mata ta kifa kanta tsakanin thighs d'inta a hankali ta fara sheshshek'ar kuka muryarta tana rabewa tace "to ai dai ka san ban ci komai ba muka fito" ya zuba mata idanunsa a hankali ya kai hannu ya d'agota ta fizge da k'arfi za ta koma ya mata tsawa "keep ur mouth shut kafin na mareki" d'agowa tayi tana kallonsa sai kuma ta koma can jikin k'ofar ta kece da wani kukan mai shiga rai,ya zuba mata idanunsa yana kallon shagwab'arta,sanda ya tabbatar baza ta daina ba ya tada motarsa ya bar gurin,taji sai tafiya suke ita dai bata d'ago ba bare taga ina yake shirin kaisu sanda suka shiga hospital da yake aiki yayi parking ya bud'e ya fita bai saurareta ba yace "idan kin gama kukan kya fito" yayi gaba abunsa,d'ago kanta tayi ta harareshi har ya yi nisa ta goge hawayenta ta bud'e motar ta fita,taga ba gida ya mayar da ita ba da sassarfa ta bi bayansa tana kwala masa k'ira "Yaya!" Yana jinta bai tsaya ba ya ci gaba da tafiyarsa,da muryar kuka tace "Yaya ka tsaya ni na gaji" murmushi yayi yace "kiyi sauri" tace "Allah ni dai na gaji kuma kak'i tsayawa sai sauri kake" yana shiga ward d'in da office d'insa yake ya bud'e ya shiga yana lumshe idanunsa,ta turo k'ofar da k'arfi tana shiga ta zube a k'asa ta saki sabon kuka,saurin juyawa yayi ya mata tsawa,cikin kuka tace "to ni me na maka da za kana azabtar da ni?" Ya bud'e idanunsa sosai yana kallonta ta ci gaba da kukanta,bai sake mata magana ba ya k'arasa ya d'auki lab coat d'insa yasa,ya wuceta zai fita ta mik'e da sauri a tsorace tace "Yaya ina za kaje ka barni ni kad'ai?" Yace "ban sani ba" da sauri ta biyo shi ya juya ya mata wani kallo yace "ina za ki bini?" A shagwab'e tace "to ni kad'ai za ka barni kuma?" Yace "wani abu ne zai cinye ki idan kin zauna?" Tace "to ai tsoro nake ji" ya juya zai fita yace "idan kika biyo ni jikinki zai gaya miki" ta zumb'uro masa baki hawaye sun cika mata ido tace "ni dai ka mayar dani gida yunwa nake ji" yayi gaba abunsa yace "kafin na dawo na tarar kin mutu k'arewan yunwa.." Yana gama fad'a ya fice ya rufe ta a ciki,k'wafa tayi ta koma ta zauna ranta a b'ace,almost one hour sannan ya dawo ya tarar da ita a kwance kan kujera tayi kuka har ta gaji baccin wahala ya d'auketa sai ajiyar zuciya take saukewa,ya kalleta ya k'arasa wajen table d'insa ya fara zare lab coat d'in kafin ya zauna kan kujeran,ledar dake ajiye kan table d'in mai d'auke da tambarin Galaxy friends and delivery yasa shi d'agowa da sauri ya kalleta kafin ya zaro pack d'in ya duba,yaga ko tab'awa bata yi ba,ya kalleta da tunanin tun lokacin da aka kawo take bacci ko kuma fushi tayi tak'i ci,ya ajiye ya tashi ya isa gurin da take a hankali ya tsuguna kusa da fuskarta in a way style ya kai hannunsa fuskarta yana shafa side d'in fuskarta,sake gyara kwanciyarta tayi tana sauke numfashi,ya d'anyi tapping fuskarta a hankali ya kirata "Manar!" Kamar ta jisa tayi masa murmushi tace "shhhiii!" Ya zuba mata idanunsa cike da mamaki ya sake kiranta,hannunta ta kai ta rik'osa gaba d'ayansa da muryar bacci tace "nifa ba na son komai,bazan ci ba.." Ta b'ata rai a shagwabe ta zumb'uro masa baki tace "fushi ma nake yi da kai ai,kayi tafiyarka ka barni,bayan na ce ma yunwa nake ji" ta fara sheshshek'ar kuka duk a cikin baccin tace "kuma sai na fad'awa Abba nace har gurin aikinku ka tafi da ni kayi ta min fad'a kana min tsawa.." Wani murmushi yayi da ya fahimci bata san me take ba,ya zareta da kyar daga jikinsa ya tashi ya koma kan kujeransa ya fara duba files da suke gurin,bai fi mintuna goma ba da barin kusa da ita ta farka da kuka,ya kafeta da idanunsa yana d'aure fuska yace "meye matsalarki?" Tace "Yaya yunwa fa nake ji ka mayar da ni gida" harara ya aika mata yace "ki cire tunanin zan mayar da ke gida yanzu.. Oyah! Tashi kije ki wanke baki kizo kici abinci acici" zumb'uro masa baki tayi tace "bazan ci ba" ya d'aga shoulders yace "cikin ki ba nawa ba" harararsa ta dunga yi shi kam ya duk'ufa aikinsa,sanda ta ji uwar bari cikinta sai k'ara yake ta tashi da gudu ta shige toilet ya d'aga kansa ya bita da kallo,fitsari tayi ta wanke bakinta da fuskarta ta fito ya d'aga kansa ya bita da kallo,ta d'aure fuskarta ta wuce tana murgud'a masa baki,ta k'arasa gaban table d'in ta kai hannu za ta d'auki ledan yayi saurin d'aukewa,ta kalleshi da sauri tace "ka ba-ni" idanunsa a cikin nata yace "u loose girl.." Ta dunga kallonsa ta kasa sake masa magana,ga shi bata gane me yace ba,nan da nan idanunta suka fara kawo ruwan hawaye ta kalleshi kawai ba tare da ta ce masa komai ba ta juya ta yi ficewarta daga office d'in,saurin tashi yayi ya ajiye ledar ya biyota yaga ta kama hanya za ta bar asibitin da sauri ya dunga nufarta tana tafiya tana share hawaye bata san ya biyota ba sai ji tayi an rik'ota ta juya a tsorace taga shi ne,yana mata wani kallo yace "ina za kije?" Hannunta ta fara k'ok'arin k'wacewa da taga baza ta iya ba tace "ka sake min hannu na tafi" yace "kin yi hauka ne?" Ta fashe da kuka tace "ni ka kyale ni,babu ruwanka da ni,ka barni na tafi gida" juyawa yayi yaga mutane har sun fara kallonsu yace "wuce muje" tace "ni ka kyale ni,bazan koma ba d'in" yin duniya yayi da ita ta k'i yarda su koma,ya shammaceta ya d'auketa ya juya ya nufi hanyar office d'insa,taga idanun mutane sai kallonsu ake da sauri ta kai hijab d'inta ta rufe fuskarta,ya tura k'ofar ya shiga ya k'arasa gurin table d'in ya d'orata a kai ya zauna kan kujeransa,fuskarsa a d'aure yace "bud'e idonki ki kalleni" kafad'a ta mak'ale masa tace "ank'i a bud'e d'in" ya zaro k'ananun idanunsa yace "ni kike cewa baza ki bud'e ba?" Ta d'aga masa kai tace "to ba fad'a kake ta yi min ba tunda muka taho,kuma baka bani abinci na ci ba" yace "na ji bud'e idon" tace "ni ka kyale ni gida zan tafi" yace "ba yanzu ba ki bari har lokacin tashi yayi" saurin bud'e fuskarta tayi a shagwab'e tace "kaiii! Kuma sai nayi ta zama a nan har dare?" Gyad'a mata kai yayi yana kallonta yace "baza ki zauna ba?" Tace "ni dai gida nake son komawa" yace "nan a dawa kike?" B'ata rai tayi ta d'auke kai tak'i kallonsa,yace "tambayarki nake" ta zumb'uro masa baki tace "to ni na san ina ka kawo ni" kallonta ya tsaya yi kamar zai yi magana sai kuna ya fasa yayi k'wafa ya d'auko ledar ya mik'a mata yace "karb'i nan" ta kalli ledar tana yatsina tace "mene ne shi?" A fusace yace "ban sani ba" matsawa tayi gefe ta b'ata fuskarta,ya mata tsawa yace "kin karb'a ko sai na daka ki? Kinga ina biye miki shi yasa za ki min iskanci?" Ta fara masa alamun kuka ya fizgota da k'arfi gaba d'aya ta fad'a kansa ta fasa masa k'ara a kunne,saurin runtse idanunsa yayi duk da ya ji fad'uwarta jikinsa hakan bai hana shi fad'in "ke meye haka?" Tace "ni me na maka?" Ya bud'e idanunsa ya kalleta fuskarsa a d'aure yace "sauka!" Tashi tayi daga jikinsa sum² tayi kamar za ta fita daga office d'in yace "idan kika fita ni da ke" ta tsaya a gurin ta waigo tace "to ni ce maka nayi fita zanyi?" Yace "ohoo miki" ta hararesa da k'arfi ta fizgi ledar ta wuce kan kujera ta zauna ya bita da kallo. Hankalin Dadda gaba d'aya ya tashi ganin wuni guda sur babu labarin Manar,yaran kuma duka sun dawo gida,duk wanda ta tambaya Manar sai yace bai san ina suka tafi ba,Ameerah ce ma ta fad'a mata tace ta gansu a skul d'insu ita da Yaya,rai a b'ace Dadda tace "to kuma daga na masa shiru sun tafi shi kenan sai yak'i dawo min da yarinya har yanzu,ko abinci fa bata ci ba ya d'auketa ya tafi gantali da ita" Ameerah tace "ai dai kin san ba zai b'atar da ita ba" cikin fad'a Dadda tace "ke dai wannan yarinya sam ba ki da hali,ni ina ruwana da bazai b'atar da ita ba? Ni dai gaskiya a yi masa waya ya dawo da ita idan ba haka ba zan je na samu uwarsa ko na d'auki mayafi na bisu" Ameerah tana jin haka ta mik'e tana dariya tace "idan kin san inda suka tafi?" Dadda take "ko ban sani ba sai na fad'awa Yaro
Chapter 39 · 0% Book details