Sashe 2
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali cab d'in yake gangarawa daga saman babban titin ya sauka line da ya shiga katafaren Housing estate d'in da yake nan shiru kamar babu masu rai cikinsa,su biyu ne zaune back seat daga y'ar dattijuwar da shekarunta za su kai 70+,sai wata y'ar kyakyatawar budurwa wacce shekarunta baza su wuce 15yrs ba,duk da a zaune take hakan bazai sa a kasa gane doguwa ce ba,y'ar kewayayyiyar fuskarta dake d'auke da manyan fararen idanu mammalakan wasu irin dogayen eyelashes,ga wanda bai santa ba zai yi tunanin tana k'arawa da artificial but haka halittar ta yake,hancinta da yake nan d'an dai² a fuskarta ya sha wani had'ad'd'en ring-shaped,sai y'an k'ananun lips d'inta da suke bayyanar da murmushi da suka sha red chapstick,duk da k'arancin shekarunta kyaunta a bayyane yake sam ba abune da yake a b'oye ba,tun da suka shigo arean take lek'en hanya,yanda ta matsu motar ya tsaya,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta fita daga motar,d'auke kai dattijuwar tayi daga kallonta ta tab'e baki,kafin wani cikinsu ya samu damar magana driver ya tsayar da motar a bakin makeken get d'in gidan,ko gama gyara parking bata jira ya yi ba tayi sauri ta bud'e ta fita cikin wani irin zumud'i da gudu ta nufi get d'in gidan tana dariya,da duka k'arfinta ta hankad'a k'aramar k'ofar,ba tare da ta tsaya rufewa ba ta wuce k'ofar ya koma da kansa yayi wani k'ara mara dad'in ji,a nutse take bin ko ina na gidan da kallo,babban compound ne sosai dake d'auke da shuke² masu d'aukar hankali,kai kana ganin gidan kasan naira ta zauna,makeken tsakar gidane dake d'auke da apartments har uku,a tsakanin kowane apartment akwai tazara mai nisa,duplex ne babban gaske sai parking space dake can gefe,tsarin gini da komai na apartment biyu iri d'aya ne hatta da fenti babu ta inda suka bambanta sai d'ayan apartment d'in dake can k'arshe wanda yake flat mai kyaun gaske,wani irin kallo ta dunga k'arewa apartments d'in kamar mai son tuna wani abu,a hankali tayi wani murmushi cikin harshen larabci da y'ar siririyar muryarta ta furta "anaa halla ja'eeh.." Waiwayawa tayi da niyyar mata magana,kamar aljana ta nemeta ta rasa da sauri ta kalli hanyar get da yayi k'ara,baki bud'e cikin wani irin takaici kamar za ta fashe da kuka ta furta "O'o! Allah ga-ni (inji kishiyar mai doro),ni dai *AZUMI* ina ganin ta kaina,yarinya kullum sai girman kawai amma hankali walaa.. Ya Allah ka mana maganin abunda yafi k'arfinmu" mai cab dake sauraren mitar ta bai san sanda ya saki wani murmushi ba,yana ci gaba da sauke manyan jakunkunan dake saman motar da booth yace "kayya dai Hajiya ai yaran yanzu addu'ah kad'ai ake musu" wani k'wafa tayi mai ciwo tace "ai kuwa dai d'an nan,tou Allah shirya mana zuri'ah" yace "ameen" kafin ya gama sauke kayan tace "Malam audu kake ko?" Dariya yayi yace "a'a Hjy hala dai sunan kakanki kenan?" Tayi murmushi tace "k'warai kuwa" mai cab yayi dariya yace "ko da na ji" tace "tou kai ya ne sunanka d'an nan?" Yace "Usman" rik'e baki tayi da wani murya tana kallonsa tace "Allahu akbar.. Sunan mai gidana gareka!" Yayi murmushi yace "dara ya ci gida kenan" tayi murmushi tace "ai kuwa ya ci" mai cab sai murmushi yake bai sake cewa komai ba har ya gama sauke kayan,yace "tou Hjy zan tafi ni" kallonsa tayi saurin yi tace "yawwa! Ko za ka d'an jire min kayan na lek'a ciki na samo y'an jikoki na su kwasar min,wallahi duk na gaji ko tsinke ni dai ba na iya d'auka a nan,tafiya ce muke ta yinta za'ayi baza ayi ba,sai da na gaji da zaman jira kafin shegen jirgin ya kwaso mu,da muka d'auko hanya kuwa ni gani nayi kamar za'a bar duniya da mu" mai cab yayi murmushi yace "toh Hjy! Allah sa baza ki dad'e ba dan sauri nake" kyab'e baki tayi tana masa wani kallo a kaikaice tace "yo to duk saurin da kake ai dai za ka jira na fito ko? Baka tafi ka barmin kaya b'arayi su sace ba" yayi murmushi yace "tou a fito lafiya" tace "yawwa! Ko kaifa" shi dai bai sake ce mata komai ba,bata sake masa magana ba itama ta wuce tana d'ingisa k'afa ta barshi nan tsaye,da get keeper d'insu ta fara had'uwa yana tsaye bakin k'ofar d'akinsa yana sababin tsoratasa da akayi,ta masa wani kallo jin yana zage² ta had'e rai da fad'in "kai da waye haka kuma Yaro?" Da sauri ya fiddo idanu yana yana kallonta yace "Hajjaju ku ne tafe?" Sanda ta tab'e baki ta d'auke kai tace "to ko mu koma ne ba'a son ganinmu?" Yaro ya sosa backhead d'insa yana sakin murmushi mai kama da na yak'e yace "wane mutum Hajiya? Barka da zuwa,an zo lafiya?" Ci gaba da tafiya tayi a dak'ile ta amsa masa "lafiya" daga haka ta wuce ta barsa tsaye,sanda ya tabbatar ta wuce yana lek'en hanya yace "annoba ta dawo,Allah sa da wuri za ku koma!" Sanye take da Arabian gown da mini hijab bak'ak'e da ya tsaya iya wuyanta,zaune a balcony ta hangosa saman farin plastics chair yana amsa kira a waya idanunsa akan laptop dake ajiye saman wani k'aramin table yana operating,matashi ne dogo sosai kyakykyawa wanda bazai haura 30yrs ba,kana kallonsa ka ga bafulatani usul,tana yi masa wani kallo ta ware manyan idanunta cikin k'arajin murna sanda ta tabbatar shi ne a gurin ta kwala masa kira *"Yaya!"* Then ta kwasa da gudu tana dariya ta nufosa,kamar a mafarki ya jiyo maganarta ya d'ago kansa daga kan computer dake gabansa suka yi idanu hud'u,mamakin ganinta a dai² lokacin yasa shi ware sexy eyes d'insa dake d'auke da wasu irin dogaye kuma zara²n eyelashes,gashin girarsa da suke cikakku masu duhu kamar anyi masa curving a d'age ya dunga mata wani kallo,fad'awa jikinsa tayi ta saki dariya cikin harshen larabci ta furta "na yi kewarka sosai Yaah *WALEED!"* Wani kyakykyawan murmushi ya samu kansa da yi ba tare da ya yi mata magana ba ya rungumeta firmly had'e da lumshe idanunsa cikin wani irin shauk'in kasancewarsu a hakan,within 3 seconds murmushin dake kan kyakykyawar fuskarsa ya dunga disashewa sanda yayi turning zuwa yanayin b'acin rai mai wahalar fassaruwa yayi saurin bud'e idanunsa,babu zato ya hankad'eta daga jikinsa,fad'uwa tayi a k'asa dai² lokacin dattijuwar ta sawo kai idanunta suka hango mata abunda ke faruwa,cikin wani irin b'acin rai ta dunga tahowa inda suke ba tare da ta yi magana ba,k'ara ta fasa kafin ta saki wani kukan da kamar ana zare mata rai ta fara birgima tana turje² a k'asa,Waleed yayi saurin mik'ewa yana aika mata mugun kallo ya fara tattare belongings d'insa zai bar gurin,fahimtar abunda yake shirin yi yasa ta ci gaba da kuka bil'hak'k'i,takaici ne yasa shi d'agowa zai yi magana idanunsa suka hango masa tahowarta a mamakance da wani murya yana zaro idanunsa ya furta *"DADDA!"* Sanda ya sake bud'e idanunsa yana kallon yadda take tahowa cikin tsananin b'acin rai da sauri ya juya zai shige apartment d'in,d'aga murya tayi cikin masifa tace "amma dai wannan yaro kai dai ba d'an arziki bane,Allah wadaranka ya wadaran mai hali irin naka" cak ya tsaya a bakin k'ofar yace "Allah ya dawo dake ai" cikin masifa dao² ta k'araso gurin tace "to ko za ka kore mune?" Bai tankata ba ya bud'e k'ofa,Dadda ta k'arasa inda take kwance a k'asa ta d'agota b'acin rai k'arara a fuskarta ta ci gaba da mita "yanzu idan banda bak'ar mugunta *MANAR* ba k'anwarka bace da za ka daddage ka hankad'eta? Kai da za kaga wani yana cutarta ka hana,amma shi ne tsabar iya shege yarinya daga zuwanta za ka fara zaluntarta? Wanda duk bai ji tausayin maraya ba dai,Allah ma bazai tausaya masa ba.." Juyowa yayi saurin yi yayi mata wani kallo yace "waye marayan?" Tsuke fuska tayi idanunta a kansa tace "ban sani ba" ya tab'e baki yace "kin sani mana tunda ga shi kin fad'a" tsaki tayi ta juya ta ci gaba da mita "yarinya tana murnar tazo ta ganka,kullum ba ta da magana sai tambayar yaushe za muzo Nigeria,daga zuwa ka ce bari na ci ubanki,babu tausayi ka daddage ka jefar min da ita k'asa... Yanzun da ta ji ciwo kai ko uwarka ne za kuyi jinyarta?" Wani kallo ya mata a fusace yace "wai Dadda da kike min masifa daga zuwanki,ni kinji na ce miki ina son ganinta? Ko wani yace miki ya damu da zuwanta?" K'ara volume d'in kukanta tayi,Dadda tayi k'wafa saboda haushin da maganarsa ya ba-ta bata iya ce masa komai ba,ta juya baki cikin harshen larabci ta fara yiwa Manar fad'a "kema maganinki ai,mutumin nan kin sansa ba mutunci ya cika ba,tun farko kuma sai dana kwab'e ki akansa baki ji ba,idan yaji miki ciwo kya tafi gurin uwarki kiyi jinya ni babu ruwana bazan iya wahala ba.." Sakin baki Manar tayi ta dunga kallon Dadda dake karkad'e mata jiki,bata ce komai ba ta juya ta kallesa,suna had'a ido ya aiko mata harara ya juya yayi shigewarsa ya rufe k'ofar,tab'e baki Dadda tayi ta rik'e hannunta tace "muje.. Dama kuma zan sake fad'a miki bazan gaji ba,babu ruwanki da duk wani d'an iska a gidan nan,kinji na fad'a miki,na raba ki da su,duk wanda ya takaki ki rama,kada ki kuskura ki zo min kina kuka,bazan jurewa sauraren kukan ki ba ko yaushe,idan kin ga baki iyawa mutum yafi k'arfin ki,wannan dai ki masa Allah ya isa ki gudo wajena,naga shegen da ya isa tab'a ki a gaban idanuna.." Zumb'ura baki tayi tak'i cewa komai,Dadda ta kalleta tace "kinji me nace miki?" Kamar wacce akewa dole ta gyad'a mata kai,Dadda tace "babu ruwanki da shiga shirgin su,idan baki san su ba ni nan na san da su waye muke zaune,babu wanda ban san halinsa ba,shekarun da muka yi da su ba banza ba,duk y'an bak'in ciki ne da kike ganinsu,d'an tafiyar nan da kika yi zuwa harami shi sukewa hassada,Allah ya kiraki su bai kira su ba,mak'iyinka wata rana bafadenka,kada shegen da yazo ya nuna miki so yanzu kika yarda da shi,munafukai sun fi yawa a gidan nan masu fuska biyu,sai kin kula sosai kinji na fad'a miki.." Kallon Dadda tayi saurin yi da fuskar kuka tace "har da Yaya?" Dadda ta saki baki tana kallonta da sauri