← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 184

Sashe 105

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

#Manage please..

#Asli Smasher.
[2/20, 8:41 PM] My number 1: 36...

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*

*Subscribe and read happily without feeling any guilt.. It's ₦200 via 0060746882,Hauwa Muhammad Usman,Access Bank or MTN recharge card/VTU and then show ur evidence of payment through my whatsapp account 08165726609 to be added in the paid group.*

Ya marairaice yace "i said i'm so sorry.." Fuskarta a d'aure tak'i kallonsa tace "sai dai idan za ka gayamin shi ne zan hak'ura.." Ya lumshe idanunsa ya bud'e,a hankali yake sauke ajiyar zuciya saboda k'amshinta daya cikasa,shi kansa ya san ba k'aramin dauriya yayi ya iya tsayawa kusa da ita ba tare da ya mata komai ba,da wani murya mai cike da rauni yace "yanzu dai aure za kiyi ki tafi ki bar ni koh?" Tayi dariya tace "toh kai ma ba ka yi auren ka tafi ka bar ni ba?" Wani kallo ya dunga mata kafin yace "sai kuma aka ce miki ina son matar?" Dariya ta sake tayi sosai kafin tace "but ko ba ka sonta ai u are enjoying ur marriage,tunda kuna tare har yau baka saketa ba,wa ya san ma me kuke yi da ita.." Kallonta ya dunga yi ko k'iftawa babu,cikin sanyin murya yace "how did u know i'm enjoying my marriage?" Ta d'aure fuskarta kamar za tayi kuka tace "bayan na gani.." Da sauri yace "kika ga me?" K'in yarda ta kallesa tayi tace "meye ma ban gani ba" da sauri ya juyata ya had'ata da bango,ya tsaya gabanta sosai har suna jin numfashin juna muryarsa a raunane yana girgiza mata kansa yace "noo! Lilac i'm only trying my best na sauke hak'k'inta dake kaina,bayan wannan Allah ma shaida ne ba wani amfanin da auren yake min,ba sonta nake ba kin sani,kawai dai Mama ta takura sai da na aureta" a hankali ta d'ago idanunta tana kallonsa sympathetically tace "to me yasa baka fad'a ba ka sonta ba?" Yace "waye zan fad'i ma?" Tace "ko Hjy idan ta sani ai ba za ta bari ba tunda ba ka sonta" ya girgiza kansa a hankali yana lumshe idanuwansa yace "it's too late nace ba na so,akan haka na sani Mama za ta iya yin komai tunda zab'inta ne,ni kad'ai nasan tarin matsalar da nake ciki,but i know there's someone wanda aka halitto ni dominta,ita kad'ai ce nake ma wani irin son da ban tab'a yiwa wani hallita ba,hatta mahaifiyar da ta kawo ni duniyar nan,ba na jin sonta kamar yanda nake jin sonta,soyayyarta yana tafiya ne dai² da bugun zuciyana.. For sure ranan duk da na rasa soyayyarta,ranan zan daina numfashi.. Ki min addu'an Allah sa wanda nake so kada ta kub'uce min.." Tunda ya fara maganan take kallonsa da wani irin surprise look jin yanda yake fayyace soyayyar wata a zuciyarsa,a hankali cikin wani irin mutuwar jiki tace "who's that lucky lady Yaya?" Ya d'ago idanuwansa ya zuba mata su yana mata wani sanyayyan kallo,a hankali idanunsa cike da wadu hawaye yace "antiii.." Zaro idanuwa tayi tana kallonsa tace "ni kuma?" Ya lumshe idanuwansa ya bud'e a kanta yace "kina d'auka wasa nake maki da?" Ta gyad'a masa kai a hankali hawaye suna kawowa idanunta,a hankali yace "me yasa? Ba kya so na? Ban kai matsayin da za'a so ni ba?" Ta girgiza masa kai da sauri,yayi d'an murmushin yak'e wanda hausawa ke cewa ya fi kuka ciwo yace "i don't know why kika kasa ganewa tun farkon" hawaye suna biyo cheeks d'inta ta kwantar da kanta a k'irjinsa maganarta a sanyaye tace "u are very handsome,gentle,tall,huge,besides u are cute,babu macen da za ta k'ika.. So stop being afraid Yaya,baza ka rasa ni ba,k'ila kaga a yanzun wani k'addaran ya ratso,duk da two days yayi saura a d'auramin aure,ina sonka but ur wife i so much dislike her,ina jin kishinta har cikin raina,ni dai nasan ma ka fi k'arfinta,ba ka sonta,ita kad'ai take rawan kanta har take ma mutane wulak'anci,kuma ita kad'ai take haukan sonka ko? Bata san ma u are only managing and.." Sai kuma ta yi shiru tana share hawayen dake sauka fuskarta,lokaci d'aya yaji wani sanyi yana ratsasa yayi wani sanyayyan murmushi,yana kallonta ya d'ago chin d'inta suka had'a ido yace "and what?" Turo masa baki tayi tace "babu komai fa.. Ni ba wani abu zan ce ba dama" ya lumshe idanunsa yana shak'ar k'amshin da ya gama huda jikinta muryarsa can k'asa yace "i'll soon enjoy my marriage.." Ta ware idanunta da sauri tana kallonsa tace "how? Da waye kuma za kayi enjoying d'in?" Ya bud'e idanunsa sosai yana kallonta yace "ina ji a jikina everything will be okay" tayi d'an murmushi bata ce komai ba suka yi shiru for a little bit,kafin ya kalleta yana sauke ajiyar zuciya yace "za ki iya aure ki barni?" Dariya tayi sosai tace "kai ma ba ka yi ba ka barni?" Yace "ai ina zuwa kullum na ganki" da sauri tace "a'a ni ba gurina kake zuwa ba,gurin Dadda kake zuwa" yana kallon eyeballs d'inta a hankali yace "believe me saboda ke nake zuwa nan,duk sanda na zo ban ganki ba ba-na iya bacci ranan" kamar za tayi kuka take kallonsa tace "amma kuma ai hakan bai hana kayi tafiya ka barni ba,har number na ka sa a blacklist fa,kuma yanzu kace saboda ni kake zuwa?" Ya sauke idonsa kan lips d'inta bai ce komai ba,tayi murmushi tace "ka ga da matarka tana sona ko bayan na yi aure sai in dunga zuwa gidanka sosai.." Bai jira ta kai k'arshen maganar da take son yi ba,yayi saurin grabbing lips d'inta saboda yanda maganar aurenta ya damesa,idan akwai abunda ya tsani ji d'aga gareta kalmar idan tayi aure ne,lumshe idanunta tayi saurin yi a hankali suka sauke ajiyar zuciya,ya kai hannunsa ya d'afe bangon da ya jinginar da ita,da d'ayan hannunsa ya d'aga hijab d'inta yana shafa smooth skin d'inta yana kallonta,a hankali ta kai hannunta ta zagaye wuyansa da su,har d'age ta k'ara saboda dad'in sucking lips d'insa take mugun ji,tun ranan farko da ya fara kissing d'inta take jin bak'on yanayi yana ziyartarta muddin za su kasance su kad'ai a guri,shisa tun farkon ta so dakatar da shi,but yanzun kam Allah ma ya sani ba ta jin za ta iya daurewa yazo kusa da ita ko ya nemi wani abu ta hanasa,ita akanta she's in need bare kuma shi da yake fad'i mata an haliccesa da laruransa ne kad'ai dominta,me zaisa baza ta bashi ba,itafa ji take ma ko cewa yayi zai having d'inta za ta amince saboda tausayinsa da soyayyarsa da yake d'awainiya da ita cikin kwanakin,sun d'auki lokaci mai tsayi tare kafin yayi saurin zare lips d'insa,cikin wani irin tsoron da lokaci guda ya shigesa yayi baya yana sake kallonta,shin idan wani ya gansu me zaice? Tunda ba wani keb'antaccen guri suka samu ba,taimako d'aya Allah ya musu shi ne kawai da ya kasance dare ne lokacin,in bayan haka ya san komai zai iya faruwa,bata iya ce masa komai ba ta wuce ta nufi b'angaren Dadda kasancewar can ta fito da niyyar zuwa,ya bi ta da kallo har tayi nisa,ya d'an lumshe idanunsa ya bud'e,kanta a k'asa take tafiya tun bata k'arasa balcony ba k'amshin scent's d'in Azaan suka tabbatar mata yana gurin,da sauri ta d'ago kanta gabanta yana tsananta fad'uwa,suka yi ido hud'u da shi yana amsa waya,ta d'auke kanta ta d'anyi gaba,kamar wanda akace ta waiga taga still bai bar kallonta ba,ta zaro ido tana watsa masa hannuwa tace "why are u staring at me?" Bai ce mata komai ba yana kallonta,a hankali yayi magana da hindu then ya katse wayar ya tako zuwa gabanta kad'an yana sake kallonta,ita dai duk ta rikice ganin yana zagayata tace "Yaya! What are u doing?" D'an tsayawa yayi yana binta da wani kallo yace "wane scent ne kika sa?" Sai da tambayar yasa gabanta ya fad'i ta fara in'ina,yace "kamar na san k'amshin somewhere.." Da sauri ta kalleshi ta kasa cewa komai,ita kanta tana jin bak'on k'amshin a jikinta and ta fi kowa sanin inda ta samosa,ganin ta kasa masa magana ya tab'e baki ya juya yace "goodnight.." Da kallo ta bisa hawaye cike a idonta,har ya bar gurin then shige ciki da gudu,Waleed dake tsaye har sannan inda ta barshi jin alamun footsteps ana tahowa daga bangaren Dadda,yana bud'a idanunsa suka had'a ido da Azaan dake tahowa zai wuce,yana tafiya yana kallonsa har yazo daf da shi,a hankali kamar bai son yin maganar yace "good evening" Waleed ya sake kallonsa for the second time da kyar ya daure yace "same to u" Azaan yace "ya family?" Waleed yace "alhamdulillah" daga haka Azaan ya d'an gyad'a kansa yace "goodnight.." Ya wuce ya nufi part d'insu,Waleed yayi ajiyar zuciya cike da tausayin kansa kafin shima ya juya ya bar gurin. Mama zaune cikin bedroom tana jiran shigowar Afiyah but har kusan hour guda babu alamun za ta shigo,shirun da yayi yawa yasa ta mik'e ta tsaya jikin window tana lek'awa,lokacin Manar ta fito apartment d'insu sanye da k'aton hijab d'inta dake sharar k'asa ta nufi bangaren Dadda,idanun Mama a kanta ta bita da wani kallo tana sakin murmushi,ta d'anyi nisa taga ta tsaya da wani suna d'an magana,da yake gurin ya d'anyi duhu ba sosai take iya hango fuskar waye ba,taita kallonsu tana dariya,duk abunda ya faru tsakaninsu kusan a kan idanunta ne,tayi wani dariya a fili tace "tukuna ma yarinya,baki fara bin maza ba,sai kinji ance an fasa aurenki,mugun fatan da na maki,sai ya biki da yardan Allah.. Sai kin zamewa uwarki bak'in cikin da zai kaita k'abari ba tare da ta shirya ba.." Wayanta da yayi k'ara yasa ta juyawa da sauri ta d'auko kafin ta dawo har Manar ta bar gurin,dai² nan kuma Azaan ya taho b'angaren ta kalleshi sosai tace "is that really him? Dama yaron nan ne a gurin suke iskanci da ita?" Da sauri tayi answering call d'in ganin Afiyah ce tana fad'in "ina kika shiga nake ta jiranki kuma?" Afiyah cikin kuka tace "my in-law Waleed ya koreni,har yana marina saboda na biku mun fita.. Baki ji cin mutuncin da ya min ba,k'arshen ma cewa yayi idan ni ba mayya bace na rabu da shi ya tsaneni,mai sona ma ba ya sonsa.." Cikin tashin hankali Mama ta zazzaro idanunta tace "shi Waleed d'in ne yace haka?" Afiyah tace "kin san dai bazan masa k'arya ba tunda ina sonsa" Mama ta gyad'a kai tace "barni da shi,ai wallahi bai isa ba.. Ubansa ma ya yi kad'an ya fad'a min haka bare shi,bari ya shigo duk dare yau sai na sa shi zuwa ya dawo min dake.." Wani sanyi Afiyah taji ya tsirga mata har ranta tayi murmushi cike da kissa tace "ni dai idan da matsala ki kyalesa kawai Allah had'a kowa da rabonsa.." Mama ta katseta da sauri tace "ke ban son shashancin banza,ki barni da shi kawai" Afiyah ta gyad'a kai kamar ba ta son maganar tace "alright" suna ajiye waya Mama ta juya cikin fushi tana zagaye d'akin. Washe gari aka yi mother's day,shima dai ranan haka aka b'arnatar da kud'ad'e,maganar kyau kam Manar har ta gaji da yinsa,ranar Saturday a gida aka yi d'an walima na mata kad'ai,ranar Sunday misalin k'arfe 11am su Daddy sun fito za su wuce wajen d'aurin aure,sama ko k'asa aka nemi Waleed aka rasa,Abba ya kira line sa shiru duk a rufe,dai² lokacin Amaar da Azaan suka shigo cikin wani sabo dal d'in jaguar,Amaar yayi parking ya fito sanye da d'anyen shadda sai kyalli yake kamar shi ne angon,Azaan ya fito cikin shirinsa na zuwa d'aurin aure daga sama har k'asa farin kaya ne jikinsa,suka k'arasa inda su Abba suke after sun gaisa,Abba ya kalli Amaar yace "ka ga Waleed?" Amaar ya girgiza kansa yace "rabona da shi tun ranan Friday" Abba ya gyad'a kai yace "alright! Ku wuce muje lokaci na tafiya" suka shiga mota Amaar yayi driving d'insu zuwa masallacin da za'a d'aura auren,su Daddy kuma yaransa sukai driving d'insu suna back seat suna magana k'asa² da junansu. Misalin 12pm bayan an gama d'aura auren,tun kafin su Daddy su k'arasa gidan suka yi waya lallai duk inda Waleed yake ace masa yazo gida ya jirasu suna hanyan dawowa,sanda suka k'araso gidan tuni ma labarin abunda ya faru gurin d'aurin auren ya fara tashi sama²,suna shigowa kai tsaye suka wuce b'angaren Dadda suka mata bayanin halin da ake ciki,Dadda tayi shiru tana kallonsu ta kasa magana,sanda su Aunty suka shigo parlon,Dadda ta bisu da kallo fuskarta a d'aure babu alamun wasa,Mommella ta zauna kusa da ita tana kallonta tace "lafiya kuwa Hjy?" Dadda dake jiran k'iris ta fashe da matsanancin kuka,hankalin Mommella a tashe ta kalli yayunta tace "Yaya me aka mata? Me yake faruwa wai?" Abba yayi shiru ya kasa magana,Daddy yayi ajiyar zuciya a hankali ya d'auke kansa dan shi duk baiga abun tada hankali ba a cikin maganar da suka zo da ita,Mama ce tayi shigowan k'arshe,ta dunga bin occupants d'in parlon da kallo ta kasa zama,saboda gabanta dake fad'uwa sai da Abba ya mata magana yace "nemi guri ki zauna Hjy magana za muyi.." Then ta samu guri ta zauna jikinta a sanyaye sai bin mutanen gurin take da kallo..
Chapter 105 · 0% Book details