← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 184

Sashe 43

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kai tayi tace "a'a Yaya" ya kalleta yace "ya akayi ya sani idan baku fad'a masa ba?" Tace "Yaya maganar Manar ne fa da tace baza ta sake zuwa skul ba shi ne ya sani,ya tambayeta me yasa tace haka,shi ne ta fad'a masa ita ba ta gane turanci,shi ne ya tambayeta ba mu da lesson teacher a gida tace masa ehh,shi ne sai yace zaima Yaah Amaar magana,jiya kuma shi ne kaga ya zo" ajiyar zuciya yayi yace "daga yau ku fad'a masa kada ya sake zuwa gidan nan" tace "Yaya" a fusace yace "ba shawararku na nema ba,umarni na bayar,idan ba'a ji ba kuma toh!" Ya mata wani kallo ya juya zai bar gurin idonsa sai cikin na Mama da ta kama k'ofa ta rik'e tana kallonsu,d'auke kansa yayi zai bar gurin cikin gadara tace "dawo ka zo" tsayawa yayi a gurin yace "Mama ina da wani uzuri yanzun" a fusace tace "ba shawararka na mema ba,zo ka wuce muje" babu musu ya wuce cikin d'akinta ta mayar da k'ofar ta rufe,tana jifansa da wani kallo tace "meye ruwanka a cikin maganar da naji?" Ya d'ago da sauri ya kalleta yace "Mama" tsawa ta masa "dallah rufe min baki.. Munafiki kawai,kullum na maka magana akan yarinyar nan sai kace min babu komai,yanzun uban me ya had'aka da shiga shirginsu uban iya?" Yace "Mama ba fa wani abu bane kamar yadda kike zato.." Kyakykyawan mari ta d'aukesa da shi,cikin fushi tace "wallahi Waleed ka fita idona na rufe,ina fad'a maka ba ka ji ko? Billahillaziiy yarinyar nan ko tare aka haifeka da ita sai ka rabu da ita,idan ba jaraba irin naka ba,mene ne had'in kifi da kaska? Ina ruwanka da shiga abunda bai shafeka ba?" Shiru yayi ya sunkuyar da kansa zuciyarsa sai tafasa take,Mama tace "na rantse da ubangijin al'arshi mad'aukakiya idan baka rabu da yarinyar nan ba zan ci ubanka da gaske,zan nuna maka other side of me dan ka gane ba kai ka haife ni ba" bai sake cewa komai ba sai ajiyar zuciyar da yake saukewa mai cike da b'acin rai,tace "ka ji na fad'a maka ko? Daga yau kuma daga yanzu babu ruwanka da yarinyar na,kai ko wuta kaga za ta fad'a ka kauda idonka,ban yarda ka taimaka ba ka kyaleta ta fad'a" saurin d'agowa yayi idanunsa sun yi wani irin jaa mai ban tsoro yace "Mama wannan wane irin k'iyayya ne haka? Me yarinyar nan tayi miki kika tsaneta? Mama Manar fa jinina ce me yasa kike son lallai sai mun rabu? Mama ki fad'a min me yasa ba kya son alak'ata da ita?" Cikin fushi tace "Waleed ni kake ma wannan tambayoyin?" A zuciye yace "me yasa bazan tambayeki ba? An tab'a k'i babu dalili? Haba Mama me yasa za kina haka? Idan da kara Manar y'a ce a gurinki kema fa saboda y'ar k'anin mijin.." Kafin ya k'arasa ta sake d'auke shi da mari,ya d'ago ya kalleta yana sakin mata murmushi mai ciwo yace "Mama saboda wannan maganar kika mare ni?" Cikin hayaniya tace "idan ka sake min maganar yarinyar nan zan maka abunda baka yi zato ba" yayi murmushi yana shafa cheek d'insa da ta mareshi har sau biyu yace "u know what Mama?" Ta masa banza bata kulasa ba sai kallon da take jifansa da shi,yace "Mama akan d'an wannan maganar kin mare ni,idan kuma kika san *INA SONTA* kuma fa? Za ki kashe ni kenan?" Mummunan fad'uwa gabanta yayi ta runtse idanunta cikin tsawa ta kira sunansa "WALEED!" Bai fasa mata murmushi ba ya gyad'a mata kai yace "k'warai Mama ina son Manar,aurenta nake son yi,na ajiyeta k'ark'ashin inuwata" tsawa ta sake masa idanunta suna fidda hawaye tace "Waleed ni kake cema aurenta kake son yi? Yarinyar da ta gama gantali da yawon bin kwararo,mazan larabawan nan duk sun gama k'wak'wuleta,wane ne bai san abunda kakarku ta kaita tayi ba kenan,irin wannan matar kake ik'irarin za ka auro min matsayin suruka? Wallahi in har ina raye baka isa ka auro min jinin Maryam ba,matar da ta yima y'ar uwata bak'in ciki ta kankane komai,ta hana k'anin ubanka auren Rabi k'anwata,wane soyayya ce za ta had'a ni da ahalinta? Wallahi baka isa ba Waleed,ka ji na rantse maka matuk'ar ina raye baza ka tab'a auren jinin Maryam ba,kai ko wanda suka santa baza ka aura ba bare tsatsonta.." Murmushi yayi da ya bayyana hak'oransa duk da ba ya cikin mode d'in yin hakan yace "Mama kada kija da hukuncin ubangiji,wallahi za ki iya mutuwa ayi auren.." Mummunan damk'ar da ta kaiwa wuyansa da hannuwanta biyu ta shak'esa yasa shi yin shiru,cikin gushewar hankali tace "na rantse da zatin Ubangiji baza ka aureta ba,kai ko mutuwa za kayi wallahi sai ka rabu da karuwar yarinyar nan" yana mata murmushi yace "karuwa Mama? Kina da shaidar cewa ta tab'a karuwanci? Mama ki fad'i abunda ko gaban ubangiji kika tsaya za ki iya kare kanki,kada ki fad'i abunda zai zama hujja akanki" sake shak'eshi tayi tace "dan kutumar ubanka ni kake fad'i ma haka?" Duk da yadda ta shak'e masa wuya bai hanasa zaro ido ba,yace "Mama zagi?" Cikin hayaniya tace "na yi d'in dan ubanka! D'an iskan yaro kawai,billahillaziiy zan d'aga maka nono,akan yarinyar nan ban k'i na tsine maka kabi duniya ba idan yaso kowa ya rasa.." Sosai kalamanta na k'arshe suka ba shi tsoro suka girgiza gobensa,a hankali wasu hawaye masu cike da k'unci suka fara zubowa daga idanunsa yace "Mama akan maganar za ki tsine min" ta hak'ik'ance tace "wallahi Waleed zan iya tsine maka muddin baka bar maganar nan ba" hankalinsa idan ya yi dubu ya gama tashi,ganin Mama yake kamar ta samu matsala a cikin kanta,ya daure yace "Mama kuma kina cikin hayyacinki kika fad'i haka?" Tace "hauka nake dan ubanka.." Kallonta ya dunga yi hawaye suna zubowa daga idanunsa,lokaci guda ya daina ji ya daina gane komai,duniyar kanta ji yake ta tsaya masa cak,ya zube kan k'afafunsa ya rik'o k'afafunta cikin firgici yace "Mama dan girman Allah kada kiyi min haka,wallahi idan kika ce na rabu da ita zan iya rasa numfashi,Mama ki sassauta min dan Allah wallahi dan ni kad'ai aka halicci Manar,Mama kada ki janyo abunda zaisa ki rasa ni" hankad'esa tayi daga jikinta cikin bak'in ciki tace "wallahi sai dai ka mutu Waleed,amma idan kaga ka auri yarinyar nan ba na numfashi a doron duniya.." Daga bayanta taji ance "Wannan kalmar ta ki dai² yake da na jahilin da bai tab'a shiga aji ba,bare ya zauna gaban malami,shin za kiyi jayayya da hukuncin ubangiji ne..?" Gaba d'ayansu suka juya suka kalli Aunty dake tsaye bakin k'ofar,cikin tsananin tashin hankali Waleed yace "Aunty dan Allah kisa baki ta barni na aureta.." A fusace Mama tace "na rantse da Allah baza ka aureta ba,idan ka dage kuma sai dai mu raba hanya ni da kai,daga ranar da ka aureta na yafewa duniya kai.." "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Aunty take fad'a tana jijjiga kai,cikin tsananin mamaki da tashin hankali take kallon Mama,though ta san wace ce kishiyarta amma bata fasa fad'in "yanzu Maman Waleed akan wannan maganar kike ik'irarin yafe d'anki wa duniya.? Ba-ki fa kike nufin za ki masa?" Mama ta juya ta kalleta tace "na rantse da Allah Fatima zan yafesa wa duniya muddin bai bar maganar ba.." Shiru d'akin ya d'auka tsayin wani lokaci banda kukan AC babu abunda kake iya ji,Waleed kam tuni yayi suman zaune kalaman Mama sun girgiza shi ba kad'an ba,babu abunda yake ji a cikin kansa face kalamanta da suke masa amsa kuwwa a cikin kunnuwansa,addu'ar ma bakinsa ya kasa kama kowacce iri saboda tsananin firgicin da ya shiga,a hankali Aunty dake ma Mama kallon ta tab'u ta k'arasa kusa da Waleed tana kallonsa da tausayawa tace "Waleed!" Ya d'ago kansa da sauri ya zuba mata idanu kukan ma ya tsaya ya kasa yi,Aunty ta dafa kansa cike da lallashi tace "ka yima mahaifiyarka biyayya Waleed iya yadda za ka iya,ina maka umarnin cire tunanin Manar a ranka wata rana idan da rabon ta zama mallakinka sai kaga cikin sauk'i ubangiji ya dawo maka da ita.." Kasak'e ya mata yana kallo ta ya kasa cewa komai,Mama dake gefe tana musu wani kallo banda cika babu abunda take kalaman Aunty sun mugun k'ona mata zuciya amma sam ba ta shirya kulata ba saboda ba ta da lokacinta...
Chapter 43 · 0% Book details