← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 184

Sashe 94

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

mayar da plate da cup d'in kitchen,Dadda dai ta d'aure fuskarta har Manar ta dawo parlon tace "taso mu tafi to" tsaki Dadda taja ta mik'e ta nufi k'ofa tace "in banda walak'anci jiya mu yi magana rimi² ki shanyani dan bazan gane gidan ba,ce maki aka yi kuma bazan iya zuwa da kaina ba?" Mother na goya hafsat a bayanta bata tanka musu ba suka yi hanyar fita,Manar tace "mother mun tafi" mother ta bisu da kallo tace "Allah ya kiyaye" ta wuce kitchen ta ci gaba da aikinta. Har suka isa gidan Waleed Manar bata ce komai ba a motar,Dadda ce dai ke hira da driver,zai yi parking a waje tace "a'a d'annan yi musu hamm su bud'e maka,wancan karo daka sauke mu mai gadin k'in bud'e mana yayi sai da Mamman ya fito ya shigar da mu,maza k'arasa ladanka ka shigar da mu har ciki" murmushi kawai driver yayi yayi horn,get keeper ya bud'e musu,ya shigar da su cikin compound yayi parking,Dadda ta fito tace "sannu d'annan Allah maka albarka kai dai" yace "ameen Hjy" Manar ta biyota suka nufi entrance d'in gidan ta murd'a handle d'in,k'ofa ta bud'e ta shiga cikin parlon da sallama,Waleed dake zaune a parlon yana operating laptop tare da Afiyah da ta mak'ale masa lokaci d'aya Manar tayi wani kicin² ta d'auke kai tak'i ko kallonsu ta sake yi,Dadda dake tsaye bayanta tace "toh ya haka kuma,ke baki shiga ba baki ba ni hanya na wuce ba" jin maganar Dadda tasa Waleed d'ago kansa da sauri Afiyah ta tab'e baki ta k'i tashi sai ma kwanciyarta da ta k'ara yi a jikinsa,Dadda tana kallon Manar dake tsaye tana kallonta tace "lafiya kika tsaya a hanyar ko basa nan ne?" A hankali Manar tace "ehhh" baki sake Dadda ke kallon Manar kamar za tayi kuka tace "ba sa nan ina suka tafi da wannan safiyar kuma?" Manar tace "nima ban sani ba" Dadda tayi k'wafa tace "toh ai sai mu koma ko?" Manar ta janyo k'ofar za ta rufe idanunta a cikin na Waleed dake kallonta tun tsaiwarta a gurin,ya taso ya nufo k'ofar yana sanye da k'ananun kaya na shan iska idanunsa har lokacin a kanta,Dadda tana hangosa ta washe baki tace "ashe kuna ciki Manar tace ba kwa nan?" Yace "ku shigo" ba a son ran Manar ba ta fara wucewa then Dadda,suka k'arasa ciki suka zauna,a hankali yace ma Dadda "ina kwana?" Tace "lafiya lau,ya gajiya?" Yace "alhamdulillah!" tace "tafiyar na ka dama ba da safe bane?" Yace "ehh sai da yamma" tace "toh! Allah kaimu lokacin" yace "ameen" Manar bata kallesa ba tace "ina kwana?" Ya amsa idanunsa akanta,daga haka ta ja bakinta tayi shiru ko kallon inda Afiyah take bata yi ba ta d'auko sabuwar wayarta da ya ba ta as gift tana dannawa. Almost 4 hours suka d'auka a gidan kafin Waleed ya tashi yayi sama,Afiyah ta bisa sai wani kwarkwasa take ita mai miji tana hararar Manar,ita kam nunawa tayi bata ma san tana yi ba,ta dunga danna wayarta underneath abun ya mugun b'ata mata rai daurewa kawai take,amma ko fuskarta sai da ya nuna b'acin ran da take ciki,minti talatin Waleed ya sakko downstairs sanye cikin wasu k'ananun kaya hannunsa rik'e da trolley Afiyah tana biye da shi tana masa kissa,Dadda tana zaune ta saka plate d'in farfesun kayan ciki a gaba tana ci tana yiwa Manar magana,but sam ta k'i kulata sai kallonta take uninterested,Dadda tana kallon Waleed tace "toh har lokacin tafiyar ya yi ne" Yace "ehh!" Daga haka ya nufi hanyar fita daga parlon,da sauri Manar ta mik'e ta d'auki hijab d'inta tasa,tana kallon Dadda idanunta cike da kwalla k'iris take jira ta fashe da kuka dan yau ta shak'a sosai,tace ma Dadda "ki taso mu wuce gida haka" Dadda ta mik'e ta d'auki gyalenta bayan ta je ta wanke hannu ta fito tace "toh muje,Safiyah Allah ba mu alkhairi" suka yi waje su ukun,Afiyah tana ganin haka ta wani shagwab'e ta biyosu,har suka k'arasa parking space Waleed ya bud'e motar ya shiga ta tsaya kusa da shi tana kallonsa tace "D ko dai na sako hijab na biku sai driver ya kai ni gidan mu?" Ya tada motar ba tare da ya kalleta ba yace "i think it's not necessary sai kinje gidanku,ban yarda ki fita ko waje ba kiyi zamanki a nan har na dawo" kallonsa ta dunga yi da wani expression yace "bye.." Tana masa wani kallo tace "wallahi bazan zauna ba sai na tafi d'in,,dan ka rainawa kanka hankali ni kad'ai kake so na zauna a gidan nan kamar wata mayya.." Shi dai bai kulata ba ya rufe motarsa ya gama warming d'inta ya yima get keeper horn ya bud'e masa ya fita..
Chapter 94 · 0% Book details