← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 184

Sashe 135

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

a wani iri ta amsawa Aunty maganar tace tana zuwa,Aunty bata tsaya saurarenta ba ta fita,sanda ta gama nuk'u² da jan jikin kafin ta d'auki hijab d'inta ta fita,gabanta yana fad'uwa ta tsaya balcony d'in gidan Dadda tana kallon rututun takalman dake gurin,ba na mutum d'aya ko biyu ba,Abba ya d'ago a fusace zai magana ya hangota kasancewar k'ofar a bud'e yake aka barsa,fuskarsa a d'aure yana mata wani kallo yace "bismillah Hjy kada ki b'ata mana lokaci ke muke jira" Mama ta kalli yanda Abba yake magana fuskarsa babu fara'a ta k'arasa ciki jikinta a d'an sake,ta nemi guri ta rakub'e tana sunkuyar da kai,taron da ta gani ya sa gabanta mummunan fad'uwan da ta fara jin kamar fitsari yana shirin zubo mata..
Chapter 135 · 0% Book details