← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 184

Sashe 64

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama tace "ehh! Lallai fa Asama'u sai yau na yadda kwakwalwarki ta tab'u,idan ba haka ba ni za ki kalli tsabar idona kice na bari? Naga dai motoci na Yaro da Muhammadu ne ko?" Mama ta rasa me ma za ta cewa Dadda,Dadda tace "sai dai su matan su jira idan na ji zan iya aka kaimin k'awayena sai a kaisu,amma kuma suma ba duka ba gaskiya,saboda Allah fa sai dai wasu suje su tare d'an sahu ya kaisu,saboda wannan idan suka shiga motocin nan baza suje ko ina ba taya za tayi bindiga.." Wata cikin k'awayen Mama da maganar Dadda ya b'atawa rai ta kalli sauran cikin fushi tace "dan Allah Hjy Saddiqa kuzo mu tafi,cin mutuncin da tsohuwar nan take ya yi yawa,akan me za mu tsaya ne ana ci mana fuska,zuwa d'aukan amarya sai kace dole?" Dadda ta kalleta tace "da bai zama dole ba,dama wa ya gayyato ki? Kuji mata dai da wani zance,idan kin ji haushi me yasa baki zo da naki motar ba?" Matar za tayi magana Mama tayi saurin tarar numfashinta "kuyi hak'uri dan Allah Hjy Saratu,muje ciki please" wacce aka kira Hjy Saratu ta kalli Mama tace "wallahi Hjy Asama'u ba don ke ba da ko kallon mu akace tsohuwar nan tayi ba ta iyawa,amma saboda ta samu mun mata shiru har wani magana take yab'a mana,ita a wa? Za ta kallemu ta fad'a mana magana bamu yagata ba?" Hangame baki tsofaffin suka yi wata tace "ikon Allah! Anya y'ar nan kin san darajan furfura kuwa?" Hjy Saratu cikin fusata tace "kinga Baba ban sa dake ba,ki rabu dani kafin na gaya maki magana" Dadda tace "k'awar tawa kike cema haka?" Hjy Saratu tace "an gaya mata,ko ke ba kyaleki zan ba idan kika fad'a min,dan kunga ana muku shiru sai ku nemi rainama mutane hankali.. Da Allah kuma mu wuce mu tafi inda muka fito,ko dole ne zuwa d'aukan amaryar?" Dadda ta fara sharar kwalla tana runtuma ihu,tace "yau na ga abunda ya ishi kakata laraba.. Iyayenmu suna ce mana y'ay'an k'arshen zamani,ashe basu ga komai ba yanzu ne zamanin yazo k'arshe.. Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Manar dai dariya kawai take har da rik'e ciki,mother da ta shigo d'akin ta ganta jikin window tana dariya tace "ke lafiyarki kuwa?" Ta juya da sauri tana goge k'wallar data zubo mata tace "mother zo kiga Hjy!" Saurin k'arasawa mother tayi tace "me ya faru da Hjyr?" Dai² lokacin Dadda tana kurma wani uban ihu,mother ta zaro ido ta juya da sauri ta fita,Manar ta bi bayanta tana dariya,Momella dake zaune parlor ita da Aunty tunda suka ji mother ta ce baza ta d'aukan amaryar ba suka zauna nan suna hira,wucewar mother cikin sauri Aunty tace "mother lafiya kuwa?" Mother da har ta je k'ofa tace "ina fa lafiya" tayi waje da sauri Aunty da Mommella suka biyota a baya,cincirindon mutanen da suka gano tun daga nesa ga muryan Dadda sai tashi yake tana fad'a Mommella tayi saurin ratsawa tsakiyar gurin ta rik'ota tace "Hjy lafiya?" Dadda tana matso wasu hawaye tace "ina fa lafiya Hafsatu,da raina da lafiyata,ina matsayin kakar Waleed wata shegiya za ta kirani mai wanke²,idan ban hana zuwa d'aukan amaryar ba Allah tsine min,in yaso iyayenta suka gaji sai su warware auren daga kan jika na" Mommella cikin masifa tace "wace shegiyar ce tace maki y'ar wanke²?" Dadda ta nuna matan da suke tsaye gurin tace "cikinsu nan duk da kike gani babu wadda bata fad'a min magana ba iyakar iyawarta.. Fisabilillahi zanyi gayyar k'awayena ace baza suje ganin gidan Mamman ba? Shi kenan kuma daga na yi magana sai aga bak'i na,nifa bance dukanmu sai munje ba,amma ina laifi idan su k'awayen nawa sunje,ni ko Manar bata raka ni ba idan aka kwana biyu naga inda yake zaune" ran Mommella ya mugun b'aci ta dunga masifa mother dai sai hak'uri take bawa Dadda da tsofaffin,wata cikin k'awayen Mama tayi tsaki tace "kai wannan tsohuwa ba dai tijara ba" wata dake kusa da ita tace "ai ke da ganinta kin san dama masifaffa ce" mother ta kallesu da sauri tace "Hjy ku iya bakinku,kada kuga an maku shiru kuce za ku fad'awa mutane magana,bazai yuwu ku shigo har gida kuce za ku cima mahaifiyarmu mutunci ba" matar ta d'auke kai tace "toh ikon Allah" mother tace "gaya maki dai nayi,gara ki kiyaye harshenki kada yaja maki masifar da zaifi k'arfin ki.." K'arshen dai da kyar aka samu Dadda tayi shiru bayan su Mother da Aunty sun gama saka k'awayen nata a mota,Mama ta cika tayi fam ganin an bar mata mutanenta a tsaitsaye cikin fushi ta kira Abba tana kuka tace "to Alh ni dai ga-ni gida da tarin k'awayena Hjy ta tada rigima ta hanasu tafiya d'aukan amaryar,na yi magana Hafsah da su Fatima sai zagina suke,ban san me na musu ba ni dai suka tsaneni har haka.." Da sauri Abba yace "asshsha amma abu bai yi dad'i ba! Gamu nan a hanyar gidan bari mu k'araso" tace "to" tana share k'wallar kissa,ko mintuna biyar ba'a yi ba motar Abba da Daddy suka shigo gidan,ganin taron mata Daddy ya fito da sauri suka k'arasa gurin,ya kalli mother yace "me yake faruwa?" Momella tace "wallahi matar nan da ba ta son zaman lafiya za ta tada mana rikici" Daddy yace "wace mata?" Ta nuna masa Mama dake gefe tana kuka,Abba dai kasa cewa komai yayi yace "please general muje ciki" suka nufi b'angaren Dadda tare,har sunyi gaba Abba yace ma Mommella "Hafsah ku same mu b'angaren Hjy" tace "to Yaya" Dadda dai ko kallonsa bata yi ba tace "ai dai kwa bari na gama sallamar k'awayena ko?" Daddy ya girgiza kai bai ce komai ba suka k'arasa part d'inta,sanda motocin suka fara fita daga gidan Dadda da Tasallah sai d'agawa k'awayen su hannu suke suna masu Allah kiyaye hanya,suna gama barin gidan su Aunty suka wuce b'angaren Dadda,Mama kam kasa binsu tayi sai da Abba ya sake kiranta yace "Hjy ke kad'ai muke jira kin sani kuma kink'i zuwa,kin san dai duk nan babu yaronki ko bare kisa mu jiranki?" Tace "na sani Alh ga ni nan" yayi tsaki ya kashe wayarsa,Daddy ya kalleshi yace "calm down brother" kamar jira Abba yake ya fara fad'a "haba da Allah,matar nan ta gama kaini k'arshe ne,ko wane lokaci ita kenan kai k'ara,da ka fara k'ok'arin bibiyar al'amarin kuma sai kaga ita ce ba ta da gaskiya" Daddy yace "kayi hak'uri please,sha'anin ne sai ana hak'uri" shigowar Mama kanta a k'asa yasa Abba dakatawa ya dunga binta da wani kallo yace "me ya faru ne wai?" Mama ta kasa d'aga ido ta kallesu,sai da ya mata tsawa ta fara magana cikin sanyi,ya kalli Mommella yace "wai me ya had'a ku ne?" Tiryan² Mommella ta fad'i abunda ta sani,wani haushi ya ciyo Abba yana kallon Mama cikin takaici yace "baza ki canja hali ba ke dai ko?" Ta sunkuyar da kanta k'asa tana matsar ido tace "kayi hak'uri Alh" a fusace Abba yace "wane maganar banza kenan? Kullum sai dai kice ayi hak'uri,amma baza ki daina ba.. Billahillaziiy duk ranan da na gaji ki sani hukuncin da zan yanke bazai maki dad'i ba" saurin kallon Daddy Mama tayi tana share kwalla tace "dan Allah Abban Manar ka tayani bashi hak'uri in sha Allah ma haka bazai kuma faruwa ba" Daddy da yaga ta yi kalar tausayi ya gyad'a kai ya bawa Abba hak'uri,da kyar Abba yace ta bawa Dadda hak'uri,idan ita ta hak'ura to shima ya hak'ura if not kuma zai yanke hukunci mafi tsauri,Mama cikin kuka ta matsa gaban Dadda ta rik'e k'afarta tana ba-ta hak'uri,Dadda data d'auke kai gefe ta tab'e baki ta kalli Abba tace "ni dai Yaro ba don halin wannan matar ba na hak'ura,yo Allan da ya haliccemu ma muke masa laifi ya yafe bare mu,Allah dai ya yafe mu baki d'aya.." Suka amsa duka parlon,Daddy ya fara tashi zai fita,Manar dake lab'e jikin k'ofa tana ganin Daddy'nta tayi sauri ta bar gurin tana dariya. Da dare sama ko k'asa Mama ta nemi Waleed ta rasa,duka kuma layukan wayarsa a rufe babu wanda bata kira ba amma basa tafiya,lokacin Manar ta shigo gidan cikin sand'a dan tun ranar Friday bata k'ara kwana gidan ba sai yau ta shigo ta wuce d'akinsu tana zumb'uro baki,ganin babu wanda ya ganta da sauri ta datse k'ofar ta ciki ta fara tub'e kayanta za ta shiga wanka,sanda ta gama kwab'ewa pant kad'ai ne bata cire ba,kamar wanda aka ce ta d'aga kanta suka yi ido hud'u da Waleed dake kishingid'e jikin gadon ya kafeta da wani mugun kallo ko k'iftawa baya yi,k'ara ta fasa da sauri ta juya masa baya tana kare k'irjinta,ya lumshe idanunsa da k'arfi saboda har cikin kansa yaji ihunta,then ya taso a hankali yana tafiya yana layi kamar wanda yasha wani abu ya d'auko mata towel,ya k'arasa kusa da ita ya warware towel d'in ya rufa mata,hannunsa da yake nan zafi zau yana tab'a jikinta tayi sauri d'agowa a rikice ta rik'o hannun nasa tana matsawa da tambayarsa "Yaya me yake damunka jikinka ya yi zafi?" Da sauri ya dafa bango,ta sake matsawa kusa da shi ta rik'e hannunsa tace "Yaya me yake damunka wai?" A hankali yace "i'm feeling cold" zaro ido tayi tace "Yaya fever ke damunka?" Ya d'aga mata kai,ta d'ora hannunsa kan shoulder d'inta tace "sannu.. Rik'e ni to muje na rakaka ka zauna" da kyar ya dafata suka je bakin gadon,ya zauna yana mayar da numfashi da kyar,ta juya za ta fita ya kirata "Manar!" Da sauri ta dawo kusa dashi tace "gani Yaya" yana rik'e da kansa da yake jin ya yi masa nauyi yace "help me please kije d'akina ki kawo min kaya" tace "Yaya to ka bari na kawo maka magani kasha ka ji?" Yace "no fara kawo min kayan nasa" kallonsa ta dunga yi cike da tausayi tace "Yaya ka ci abinci?" Ya girgiza mata kai yace "no! Ki samo min black tea" wani kallon tausayi ta dunga masa kamar za tayi kuka tace "to" ta juya da sauri bayan ta d'auki hijab cikin kayanta ta sa ta fita daga gidan..
Chapter 64 · 0% Book details