← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 153 OF 184

Sashe 153

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

tare da Daddy da yamma suka zauna downstairs,Daddy yasa a kira masa Diyanah,ta fito sanye da babban hijab,idanuwanta sunyi ja tsabar kukan da tayi,ta zauna k'asa kanta a k'asa tana share hawaye,Daddy ya kalleta da kyau yace "Halima!" Jikinta har tsuma yake tsabar firgicin kiran da ya mata,here ta fashe da sabon kuka,Daddy yace "ba kuka na kiraki ki mana ba,kin gane kou?" Ta gyad'a kai,Daddy yace "waye ya maki ciki?" Ta dunga girgiza kai tana rufe bakinta,Abba dai baice komai ba kallonta kawai yake tsabar shork d'in da yake ciki,Daddy yace "baza ki fad'a ba?" Ta girgiza kai,yace "uhn! Kou kina so a barki haka har duniya ta san abunda ya faru da ke?" Nan ma ta girgiza kai,yace "uhn! Maza ki sanar min waye shi? Dan waye kuma?" Tana kuka tace "Uncle d'an gidan Alh Idris Baffanyo ne" Daddy yace "wane Baffanyon?" Tace "former minister of finance" Daddy ya dunga gyad'a kai yace "kin tabbatar maganar da kika fad'a haka yake?" Tace "ehh Uncle" yace "alright! Je ki kawo min Babyn" tace "tou" ta tashi jikinta a mugun sanyaye ta haura upstairs,sanda ta d'aukon Babyn dake bacci ta kawowa Daddy,ya karb'esa yace "Brother muje" a tsorace Diyanah ta dunga kallon Daddy hawaye suna saukowa fuskarta,sai dai ta kasa magana har suka fita daga gidan,a waje suna fita suka had'u da Waleed da tun bayan da ya san maganar,sanda ya tafi massalaci bai k'ara dawowa gidan ba sai lokacin,Daddy yace "son ka biyo mu za muje unguwa yanzun" ya amsa yana kallon jaririn dake hannun Daddy an nad'esa cikin towel na jarirai,suka shiga mota Waleed ke driven,Daddy yace "gidan Baffanyo za ka kaimu" yayi saurin kallon Daddy ta mirror yace "Uncle wane Baffanyon?" Daddy yace "wanda dai ka sani" Waleed dai sai mamaki yake a haka ya kaisu gidan dake cikin GRA,yayi parking bakin get,suka fito daga mota su uku,Daddy akan gaba sai Abba da gaba d'aya ya koma dumb,suka tsaya dai² get Daddy ya kalli mai gadin gidan dake zaune kan bench da radio d'insa yana saurare,suka masa sallama ya amsa,Daddy yace "gurin mai gidan muka zo.. Allah sa yana nan" get keeper da yaga ba k'ananun mutane bane yace "yana nan Alh,bari a muku sallama da shi" ya tashi da sauri ya shiga ciki,not too long ya fito yace "yace a shigar da ku ciki" Daddy yace "madalla" suka bisa a baya zuwa ciki,babban gida ne na gaske,fad'an tsaruwarsa da irin uban kud'in da aka narka wajen ginasa ma b'ata baki ne,suka wuce har parlon da aka musu iso suka zauna,mai gadi ya fita ya sanar da uban gidansa an shigo da su,Alh Baffanyo ya fito cikin shigar alfarma,sanda ya shiga parlon yana kallon su Daddy ya saki fuska yana fad'in "General of the army a gidana,ko dai mafarki nake?" Daddy dai bai nuna masa komai ba har suka gaisa,Alh Baffanyo sai kallon hannun Daddy yake yace "ina fatan dai lafiya?" Daddy yace "ita ta kawo mu gareka" Alh Baffanyo yace "uhn! Ina saurarenka" Daddy ya mik'a masa jariri without ya masa bayani,Alh Baffanyo yace "ban fahimceka ba Alh Muh'd,jaririn waye wannan?" Daddy yayi wani murmushi yace "idan ka karb'esa za ka gane ko d'an waye" Alh Baffanyo sai kallon Daddy yake sanda ya karb'i yaron a tsorace ya zuba masa ido yana kallonsa,jikinsa har wani b'ari yake yace "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Daddy ya kalli Abba da Waleed yace "ku tashi muje,Alh Allah ya raya,mu za mu koma,dama abunda ya kawo mu kenan" da sauri Alh Baffanyo yace "dan Allah General ku tsaya mu sasanta kafin maganar ya zagaye gari a san halin da muke ciki.. Ina ga wannan ba abune da za mu tsaya jan zance akansa ba,kamata yayi ace mu rufawa juna asiri da yaranmu" wani girgiza kai Daddy yayi yace "wane irin sasanci kake buk'ata muyi?" Alh Baffanyo yace "dan Allah kuyi hak'uri na san abunda aka muku ba'a kyauta ba,amma dan girman Allah ku saurare ni kuji hukuncin da zan yanke" Komawa Daddy yayi ya zauna yana kallon Alh Baffanyo yace "me kake so ayi?" Alh Baffanyo yace "idan har za ku amince,me zai hana muyi gaggawar had'a iyayen yaran aure a b'oye,ka ga mun rufawa kanmu da yaranmu asiri ko ba haka ba?" Daddy ya gyad'a kai yace "yanzu kazo da magana,amma bari na fad'a maka ka ga yanzu about 6pm,nima zan zartar da nawa hukuncin,nan da maghreb nake lokacin auren kada ya wuce nan" Alh Baffanyo yace "in sha Allah yanda kace haka za ayi,nima ba na so ya wuce haka" Daddy ya gyad'a kai ya mik'e tsaye yace ma su Abba "brother mu tafi" suka tashi suka ma Alh Baffanyo sallama,sai godiya yake musu suka karb'i yaron suka tafi,har bakin get ya musu rakiya gurin mota sanda yaga tafiyarsu kafin ya koma ciki hankalinsa a tashe. Sanda su Daddy suka koma gida babu wanda suka ma bayani,har after maghreb,sai da suka tabbatar an d'aura auren kafin suka shigo gidan,kai tsaye suka wuce b'angaren Dadda..
Chapter 153 · 0% Book details