Sashe 14
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
bata k'i zuwa duk safiyar Allah ta gaishe ni ba,kana ganinta nan dai a haka kamar mutuniyar kirki,amma ni ban isa taje ta tsuguna ta gaishe ni ba,ko da muka zo garin kaf gidan nan babu mahalukin da baije yayi min sannu da zuwa,ya tambaye ni mun zo lafiya ba,amma ita da y'ay'anta kaf ni banga k'eyarsu ba,shi isa nima ko da na tashi rabo na ban babu su ko abun share hanci ba.. Aaahhh tooooh! Maganar gaskiya fa kenan,wanda yayi da kai ai kaima sai kayi da shi,wanda kuwa yace baya yi da kai sai kaima kak'i yi da shi,amma dai maganar gaskiya ka ja mata kunne,idan ta hana wad'annan gantalallun zuwa su gaishe ni sun bi maganarta,bata isa hana Mamman zuwa inda nake ba saboda ni naci wahalarsa,komansa ni ce dan me kuwa za ta dunga k'ok'arin shiga tsakanin mu?" Wani kallo Abba ya dunga jifan Mama da shi har Dadda ta dasa aya,Abba cikin tsananin b'acin rai yace "Asama'u! Maganar da Hjy ta fad'a akanki da yaranki haka yake bakwa zuwa gaisheta?" A fusace Dadda tace "o'o! Ban gane haka maganar da na fad'a yake ba? Kana nufin da girma na zan yiwa matarka k'arya?" Saurin girgiza kai Abba yayi yace "a'a Hjy ko kad'an ba abunda nake nufi ba kenan,ina dai son ta tabbatar min ne da bakinta,saboda na san irin hukuncin da zan d'auka kansu" Dadda ta gyad'a kai da sauri tana washe hakor'in makkanta tace "Uhumn! Ko da na ji,na san dama baza ka bari a wulak'anta ni ba.. Kai dai Yaro Allah maka albarka ya kyauta bayanka" Abba yace "ameen" kafin ya juya ya sake kallon Mama yace "Hjy Asama'u dake nake baki ba-ni amsa ba?" Mama cikin had'e rai tace "haka ne" Abba ya dunga kallonta yana gyad'a kai cikin tsananin b'acin rai yace "ita uwar tawa ce baki ga damar zuwa ki gaisar ba kenan?" Mama dai ta yi shiru sai b'ab'b'ata rai take,a fusace Abba yace "da kika ki zuwa su kuma yaran fa? Wane dalilin yasa kika hana su zuwa?" Nan ma dai tayi shiru,cikin fushi Abba yace "Tambayarki nake?" D'auke kai tayi tak'i cewa komai,yana gyad'a kai ya kalli Deejah dake rab'e gefen k'afar Mama yace "je ki kiramin y'an uwanki duka yanzu kuzo ku same ni" tashi Deejah tayi da sauri jikinta yana b'ari tayi sama,ba'a jima ba suka dawo tare da su Ameerah da Diyana,suka nemi guri suka zauna kawunansu a k'asa Abba ya fara fad'a yace "wane iskanci yasa bakwa zuwa gaisar da Hjy?" Ameerah ta d'ago da sauri tace "Abba wallahi ni dai ina zuwa" Abba ya mata tsawa yace "rufe min bakinki a nan" da sauri Dadda tace "a'a Yaro banda takwarata cikin marasa zuwan,ita kam kullum sai taje gaishe ni safe da dare,wani lokaci ma can take wunarmin idan ba su da makaranta" Abba ya kalleta yace "su waye basa zuwa gaishe ki?" Da baki Dadda ta nuna su Deejah tace "ga su nan zaune gabanka gantalallu masu kamar an tada akuya tsaye" Abba ya kallesu yace "ashe ba-ku da mutunci? Ita Hjyr sa'ar ku ce?" Suka yi shiru,tsawa ya musu yace "sa'ar ku ce nace?" Da sauri suka girgiza kai,Abba yace "mutanen banza mutanen wofi,ni za ku gaishe ni uwata ce baza ku gaisar ba?" Suka yi shiru,fad'a sosai ya dunga yi daga k'arshen yace "duk ranar da ta sake kawo k'orafin kunyi wani abu na rashin da'a ranku sai ya yi mummunan b'aci zan sab'a muku sosai a gidan" a fusace yace "baza ku iya bada hak'uri ba?" Da sauri suna had'a baki suka ce "kiyi hak'uri" Dadda ta kau da kai tana tsuke fuska tace "shi kenan Yaro ya wuce,ni dama buri na har kullum bai wuce ace zuri'arka sun samu shaidar k'warai ba kamar yadda ka samu" Abba ya gyad'a kai ransa a b'ace yace "kiyi hak'uri Hjy in sha Allah haka bazai kuma faruwa ba" Dadda ta washe baki tace "to shi kenan,ai ya wuce ma" ta mik'e tsaye tana karkad'e jiki Abba ya bita da kallo,tace "to ni dai na tafi tunda wanda na zo neman baya nan" da sauri Abba yace "waye kike nema?" Tace "Mamman nazo nema,shima yau sati guda kenan ban sashi a idanuna ba,daga yin y'ar magana ya d'auke ni da gaba ya daina zuwa gaishe ni,ni dai ban san wane irin laifi nayiwa matarka ba da ta k'ullace ni take min haka" ran Abba ya kuma b'aci ya dunga kallon Mama ya kasa yi mata magana,Dadda tayi masa sallama ta juya ta nufi hanyar fita tana mita,tana bud'e k'ofa suka kusa yin karo da Manar dake tsaye jikin k'ofa ta kasa kunne tana sauraren abunda suke cewa,da sauri Dadda tayi baya kad'an ya rage bata zura da gudu ba,Manar ta fara b'ab'b'aka dariya tana rik'e ciki,wani irin kallo Dadda ta dunga binta da shi kamar za tayi kuka,can kuma sai ta d'auke kai tana tsuke fuska tace "ke kuma me kike yi a nan?" Manar ta juya tana dariya tace "biyo ki fa nayi na ga kina jin tsoro" wani kallo Dadda ta maka mata,cikin jin haushi tace "kin fad'awa uwarki Maryam haka" da sauri Manar ta b'ata rai tace "ke wai daga an miki wasa sai ki fara zagin mutane" a fusace Dadda tace "to ko za ki rama?" Harararta Manar tayi tayi k'wafa,Dadda ta wuce fuuu ta barta a gurin kamar za ta tashi sama,Manar ta zumb'ura baki tak'i binta ta wuce apartment d'in mother. Tun da Dadda ta tafi Abba yakewa Mama fad'a ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba sai da ya mata tass²,Mama dai tak'i cewa komai,yanda tayi masa ya sake k'ona masa rai ya dunga kallonta bai dai ce mata komai ba,ya d'auki waya ya fara kiran Waleed,Waleed dake driven ya d'auka yayi sallama,Abba ya amsa kadaram kadahan,kafin yayi wani magana Abba yace "where are u Muh'd?" Waleed yace "i'm on my way back home" Abba ya gyad'a kai yace "alright! Idan ka dawo ka same ni ina son ganinka" amsawa yayi yana duk'ar da kai kamar yana gaban Abban,in less than five minutes ya k'araso,yayi parking ya fito ya rufe motar gabansa sai fad'uwa yake ya bud'e k'ofar ya shiga da sallama,d'ago kai Mama tayi ta bisa da kallo tana had'e rai,and ta k'i amsa sallamar da yayi,sure ba don Abba dake zaune ba baza ta tab'a bari ya zo ba,tun yana hanya za ta masa waya ta hanasa k'arasowa,da kallo ya dunga bin occupants d'in parlon,Abba ya kallesa fuskarsa babu fara'a in a serious note yace "get seated my friend" guri ya samu ya zauna kansa a k'asa ya gaisar da Abba then Mama da take aika masa mugun harara,Aunty kam da fara'a sosai a fuskarta ta amsa masa har tana tambayarsa aiki,da yake kansa na k'asa bai san ma abunda Mama take yi ba kasancewar tun shigowarsa bai yarda ya kalleta ba,Abba yana kallonsa yace "Muh'd! Me ya had'a ka da grandma d'inku?" K'asa ya sake yi da kansa ya kasa magana,Abba yace "am i not talking to u Mr man?" Wani ajiyar numfashi yayi kafin yace "nothing Abba" tsabar mamaki yasa Abba couldn't stop looking at him,then ya maimaita "babu komai kace?" Yayi shiru ya kasa amsawa,gyad'a kai Abba yayi yace "this will be the last time da za'a kawo min k'aran ka,kai ne babba duka gidan amma kuma da kai ake complaints,wane irin shirme ne wannan?" Shi dai bai iya cewa komai ba har Abba ya gama fad'an yace ya tashi ya bashi guri,hak'uri ya fara bawa Abban kafin ya mik'e zai bar gurin,Abba ya bisa da kallo yace "make sure ka je ka bata hak'uri kafin safiya if not kuma ranka zai b'aci" shiru yayi ya juya ya nufi hanyar fita,kusa da apartment d'in su mother yana k'ok'arin wucewa aka bud'e k'ofa,ya waiga a hankali ya kalli gurin suka yi ido biyu da Manar dake fitowa,d'auke kai yayi ya ci gaba da tafiya,Manar tana hangosa ta kwalo masa kira "Yaya" bai tsaya ba ya ci gaba da tafiya,ta biyosa da sauri tana zumb'ura baki tace "shi ne baza ka kula ni ba ina maka magana?" Still ya k'i tanka ta,haushin yadda yayi mata yasa ta sha gabansa ta koma tafiya da baya²,ganin fuskarsa babu alamun wasa tace "Yaya me aka maka?" Wani kallo yayi mata a fusace yace "kauce ki ba-ni hanya kafin na mare ki" nok'e kafad'a tayi a shagwab'e tace "ni dai sai ka fad'a min abunda aka maka" wani kallo ya maka mata bai ce da ita komai ba ya ratseta zai wuce tayi saurin rik'o hannunsa.