Sashe 63
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Since Mama taga Manar akan stage d'in suna magana da Waleed,da wani kallon da Waleed d'in yake mata wani tuk'uk'in bak'in ciki duk ya lullub'e zuciyarta,dai² da second d'aya bata tab'a jin son Manar a ranta ba,haka nan ta tsani ganin wani abu ya had'ata da Waleed,cikin bak'in ciki da b'acin rai ta dunga kallonsu tana k'issima abubuwa da yawa a ranta,sanda ta ga Azaan kuwa a kusa da Manar da irin kirarin da MC ya dunga masa gaba d'aya taji akalar lissafinta da kwakwalwarta sun sauya,and idan har ba idanunta ne suka mata k'arya ba ko suke yaudararta tabbas ta so ganin kamar duk samarin gurin idanunsu na kan Manar,ga wanda baza su iya had'iye maganarsu ba kuwa,jin kunnenta suka dunga zuzuta kyaun da Allah ya mata,at last kam ko tashi bata iya tsayawa anyi daga dinner ba ta tafi gida zuciyarta sai azalzalarta take,tun tana kan hanyarta na tafiya ta fara k'ok'arin kiran Hjy Izzatu saboda a yadda take jin zuciyarta ta yi mata duhu baza ta iya bari har sai ta kai wayewar gari without sunyi communicating ba,ak'alla ta yi mata kira ya kusa biyar ba'a d'auka kafin ta hak'ura tana fitar da wani hucin b'acin rai ta tura mata text message "k'awata na kira ki ban same ki ba,ina cikin gagarumin matsala da tashin hankali,idan kin ga missed calls d'ina let me know please.." Har ta zo gidan ba ta da wani nutsuwa ta wuce d'akinta ta zauna ta rafka uban tagumi da duka hannuwa biyu tana tunani,wane irin al'amari ne yake shirin faruwa da ita haka,da farkon ta raba Manar da Waleed a tunaninta hakan zai sa ta samu kwanciyar hankali amma sai kuma taga abun yana neman rikid'e mata zuwa wani yanayin na daban,lallai idan har tayi sake ta bari al'amarin ya kasance kamar yadda take gani ita za ta tafka babban asara,dole ne ma ta tashi tsaye ta yiwa tufkar hanci dan baza ta iya zuba ido tana gani Manar taje inda za ta huta ba,yadda ta tsaneta tun farkon bata san ma wane sub'utar baki ya kaita tace ma bokan duk ma wanda zai aureta suje suyi tayi ba,ita fa akan ta bari Azaan ya aureta gara tayi duk wacce za tayi ta hana hakan faruwa,ko da ace za tayi yawo tsirara ne. A gefen Manar kuwa lokacin ko da ta fito daga d'akinta a parlor ta tarar da Daddy da mother suna hira k'asa² tayi sallama fuskarta a sake unlike before tana fad'in "Daddy barka da zuwa" ya kalleta yana sakin murmushi ya mik'a mata hannu yace "Mamana tun d'azu nake jiran fitowar ki" ta rik'e hannunsa a hankali ta zauna jikinsa tace "Daddy an zo lafiya,ya hanya?" Yace "alhamdulillah ya skul fa? Kina zuwa dai ko?" Wani murmushi tayi mai tafe da ajiyar zuciya tace "Daddy ina zuwa kullum,ka tambayi mother" mother dake gefe tana kallonsu tace "a'a kada ya tambayeni,ni me na sani,Hjy dai zai je ya tambaya tunda can kuke kwana kuke wuni" dariya Daddy yayi yace "alright! Kun kusa exam ko?" Ta gyad'a masa kai tace "ehh! Daddy me za ka ba-ni for gift idan naci JSCE?" Yace "idan kinyi k'ok'ari sosai duk abunda kike so i'll buy it for u" wani irin dad'i taji tace "da gaske Daddy?" Yace "sure! Yanzu ki ba ni labarin kina gane karatun ko kuwa? Ance min baki iya karatun hausa ba ma" zaro ido tayi tace "Daddy who say so?" Wani zaro ido yayi shima yana kallonta yana dariya yace "iyyee! Har turanci kin iya ashe?" Kunya yasa ta b'oye fuskarta a jikinsa tace "Daddy ai wannan da ne ban iya ba,amma yanzu har turanci na iya fa" yace "good! Ki k'ara k'ok'ari kinji Mamana,idan na ga result d'inki ya yi kyau zan miki kyauta" murmushinta ta sake fad'ad'awa tace "to Daddy zanyi" ya shafa kanta yace "Allah maki albarka" ta amsa da "ameen" d'an kallon idonta yayi da suka sauya yace "me ya samu idonki?" Wani rass taji gabanta ya fad'i ta fara kame² tace "Umm! Dama.." Yace "dama what? Kinyi kukan naki ko?" Girgiza masa kai tayi tace "no Daddy! Ina jin maskaran da aka sa mana ne gurin make-up shi ne idona ya canja" yayi ajiyar zuciya yace "alright! Thought kinyi kuka na sanki abu kad'an yake sa ki zubar da hawaye" ta girgiza kai tana murmushi tace "no Daddy ban yi ba" yace "alright! Idan kina kuka zai sa ki samu matsala a idanunki" da sauri tace "na dena" murmushi yayi yace "ban ce ki daina ba,yin kuka rahama ne,amma kina yin kad'an" ta gyad'a masa kai tace "to Daddy" hira sosai ta sake suka yi har tana kyalkyala dariya,cikin k'ank'anin lokaci ta manta da abunda ya faru tsakaninta da Waleed ta dawo kamar ma wani abu bai damu ranta ba,sanda taje kwanciya bacci nan labarin ya canja,ta dunga juye² ta kasa baccin,motsi kad'an ta shafa lips d'inta taji babu komai jikinsu,dan wani ji take kamar Waleed na sake kissing d'inta har lokacin,k'amshinsa kuwa duk da ta yi wanka ta fesa turarukanta bata daina jinsa a jikinta ba,haka ta raba dare tana fama kafin bacci ya d'auketa cike da mafarkin al'amarin da ya wanzu tsakaninta da Yayan nata. Washe gari Saturday akayi mother's eve,shima dai an b'arnatar da dukiya,ranar Sunday 11am aka d'aura aure,after weeding fatiha Daddy suka yi reception,da yamma sanda ake k'ok'arin tafiya d'aukan amarya sama ko k'asa Dadda ta nemi Manar ta rasa a gidan,tasa Ameerah taje ta dubo mata ita kafin motoci su fara wucewa,can daga apartment d'in Dadda sanda Ameerah ta koma tace bata ganta ba Dadda tana ta fad'an ina ta shige,Ameerah dai ta yi shiru tace "nima fa Hjy ban sani ba" Dadda tace "to wai motocin sun fara tashi ne?" Ameerah ta gwalo ido tace "tabb' d'i Hjy ai saura kad'an ma a gama tafiya" Dadda ta fara salati tace "na shiga uku ni jikar laraba,yanzu dan munafurci amma a rasa wanda zai lek'o ya sanarmin ni da k'awayena?" Nan suka fita ita da Tasallah da wasu tsofaffin k'awayenta da akayi zaman mutunci da jimawa,Dadda ta hango cincirindon wasu manyan mata k'awayen Mama suna shiga motoci tace "to me zan gani kuma haka?" Ta kame baki suna tafiya tana yima Tasallah mitar "to kuma haka ake fisabilillahi ita Asama'u baza ta aika a kira mu ba muje d'aukan amaryar,kawai sai ta saka wannan lafta²n matan,ko dai Mamman bai da dangi ai bai ci ayi masa haka ba,ina kakarsa ace banje d'aukan amaryarsa ba,ai sai Allah ma ya tambaye ni" Tasallah tace "duk fa kalen rashin mutunci ne da son kar a zauna lafiya,idan ba haka ba,me akayi² wasu k'awaye tunda dai ga mu danginsa muna raye har sai dai muji zance wai an tafi d'aukan amarya" motoci uku da suka yi ragowa basu k'arasa tafiya ba,Dadda ta hango wasu mata suna shiga da sauri har tana had'awa da gudu ta isa gurin tana bud'a hannu kamar yellow fifa tace "tsaya² direba" matuk'in motar farko ya lek'o yace "Baba lafiya?" Ta wani kallesa tace "ina fa lafiya,su wad'annan matan da suka cika mota ina za su?" Driver yace "Hjy tace a kaisu su d'auko amarya" Dadda tace "wace ce haka? Maza² dama ka sauke su ka kwasar min k'awayena ka kaisu gidan su gano! Fisabilillahi fa duk motocin gidan nan sun kwashe mutane sai k'awayena kad'ai za'a barmin dan cin fuska" wata mata cikin k'awayen Mama dake gaba ta lek'o tace "Haba Hjy wane irin zance kike? Mu da saboda bikin muka zo kice a zube mu" Dadda tace "to ke kuma a su wa za ki ja da magana ta?" Matar tace "ni a k'awar uwar ango" Dadda ta kalli Tasallah tace "Tasallah kiji min dai wannan mata da wani magana,ke k'awar uwarsa kike da lasisin zuwa bare ni da na haifi ubansa? Ko kuwa Asama'un bata fad'i muku ba?" Kallon Dadda matar ta dunga yi saboda bata santa ba,tayi wani dariya tace "Hjy Laura kuji dai wannan tsohuwar da wani magana ku nan kun mata kallon wadda ta haifi ubansa?" Wata dake baya ta lek'o ta k'arewa Dadda kallo,ta kalli super jikinta tana yatsina fuska tace "kai ina? Wannan da mai wanke²nsu tayi kama" salati duka tsoffin gurin suka d'auka,Dadda cikin fusata tace "kin gayawa uwarki mai wanke² shegiya mai bak'in ido.. Dama daga ganinku duk ba tarbiyya gareku ba,kuma wallahi tunda kuka fad'a min haka duk sai dai ku nemi motar da zai kaiku amma ba a motocin Y'ay'ana ba,matsiyata daga ganinku baku gaji arziki ba" tana yi Tasallah na tayata,babu yadda matan suka iya da masifar ta dole suka fito daga motocin suka yi cirko²,Manar dake d'aki ta jiyo fad'an Dadda ta tashi ta tsaya jikin window rik'e da labulen sai dariya take b'ab'b'akawa,wata cikin matan da Dadda ta sauke daga mota cikin jin haushin tijaran Dadda ta kira Mama a waya tace "to Hjy Asama'u mu dai gamu compound d'inku wata tsohuwa ta sa an sauke mu daga mota" Dadda cikin d'aga murya tace "ehh fad'a mata,ta zo nice nan,me za ta iya yi min? Allah na tuba uban wa ya haifar min yaran da za'a min gadara da dukiyarsu? Wani ya sha min wahalarsu?" Mama tace "ban gane ta sa a sauke ku ba?" Matar tace "to ni dai ki fito ki ganta,ta ce kakar Waleed ce" cikin sauri Mama tace "ga ni nan zuwa please" ta katse kiran da sauri ta fita,a compound tun kafin ta k'arasa inda suke take jin masifar Dadda da tsofaffi,ta k'araso tana kallonta tace "Hjy me yake faruwa?" Dadda ta wurga mata wani kallo tace "idan ba kinibibi irin na ki ba Asama'u har kamar ni za'a munafurtar a gidan nan" Mama tace "munafircin me aka maki kuma Hjy?" Dadda tace "yo kamar dai ba'a san na yi gayyar k'awayena ba,kawai sai mu fito za mu d'aukan amarya mu tarar an gama cika motoci da gird'ima²n mata,ko tsoron Allah ma babu mu an barmu can shanye da bakuna" Mama tace "to Hjy ki bari a fara kai su,sai a dawo a d'auke ku" Dadda tace "ban gane a fara kaisu ba?" Mama tace "su kad'ai ne basu tafi ba yanzun,idan an kaisu sai drivers d'in su dawo su kaiku daga baya" wani kallo Dadda ta dunga yiwa