Sashe 120
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
sanar musu sun fita,suka musu fatan dawowa lafiya,babu wanda ta bari aka ga kanta a waje sai da suka fito suna dariya suka gyara yafen mayafin,a mota suka tarar da su Azaan,Waleed da Amaar kowa a mota daban,Manar ta wuce ta shiga gurin Waleed,Ameerah ma ta wuce a hankali kanta a k'asa ta shiga motar da Azaan yake,Rania tayi murmushi taje wanda Amaar yake,tana shiga ta masa murmushi tace "hi!" Ya d'an kalleta yace "hello" hannu ta mik'a masa tana fad'a masa sunanta,yayi d'an murmushi ya mik'a mata hannu sukai shaking hands,Rania dake da d'an banzan surutu nan da nan ta fara masa hira,shi dai murmushi kawai yake mata yana gyad'a kai,har suka kai wani gurin koyar da rawa,Waleed yayi parking yana kallon Manar da kanta ke bud'e yace "waye yace ki fito haka kanki a bud'e?" B'ata rai tayi tace "Yaya ban yi kyau ba?" Yace "not at all.. kawai ba na so ne" kamar za tayi kuka tace "Yaya so kake amin kallon bak'auyiya kuma?" Ya dunga kallonta,a hankali ta kwantar da kanta jikinsa ta sak'alo hannunsa tace "to ba Hjy tace idan mutum yaje gari yaga mutane da jela shima ya ara yasa ba" dariya sosai ta bashi da tace haka,ya kai hannu ya d'ago fuskarta yana kallonta yace "ohh! Kema jelar kika ara kika sa kenan?" Ta gyad'a masa kai tana tura masa baki,d'an murmushi yayi yana kallon lips d'inta da suka sha wani chapstick mai masifar kyau,hancin nan da ring shapped d'inta da ya hanata sawa,wani murmushin ya sake yi a hankali ya kai harshensa kan lips d'in yana licking,idanunsa cikin nata yace "ba kya jin magana kou?" Rau² idanunta suka yi tace "ni me nayi?" Idanunsa akan lips d'inta yace "baki sani ba?" Da sauri ta gyad'a masa kai,d'an dariya yayi yace "okay" daga haka ya had'e bakinsu,sanda ya shanye janbakin ya saketa. Azaan ya shiga gurin ya musu register kafin ya fito ya kirasu suka shiga su shida,abun dariya sanda ake training d'insu rawa,Rania duk ta fisu iyawa,da kyar suka maida hankali suka koya fiye da rabin rawan nasu romancing juna suke su dai,ai kuwa ranar haka suka dawo gida jiki na ciwo,still washe gari suka sake komawa,sai da suka yi kwana uku suna zuwa kafin suka gama,ranar laraba akayi kamu na kurkum da suke yi,Azaan da Ameerah,Waleed da Manar duk sun ci fararen kaya irin na India,Dadda an sha Pakistan riga da wando dan rantsewa tayi tace "idan kaje gari kaga mutane da jela kaima ara kake kasa" har da mayafinta,sanda ta fito gurin kamun Manar tana hangota ta fara tuntsira dariya,Waleed ya kalleta yayi k'asa da murya yace "what?" Da kyar ta bar dariyan tace "Yaya" yace "uhn!" Tace "kalli Hjy Siyama kaga" Waleed yana kallon inda take nuna masa ya fara sakin murmushi ya kasa dena kallon Dadda,Manar ta fashe da dariya ta fad'a jikin Waleed tana cewa "Yaya wallahi kace ta cire bai mata kyau ba" Ameerah tana jinsu ta waiga,gano Dadda da riga da wando na Pakistan ta tuntsire da dariya tana b'oye fuskarta,Amaar yaga abun nasu ya zama wani iri ya waiga a hankali,zaro idanuwa yayi sai kuma ya juya yana dariya,jikokin duka suka dunga dariya,har aka tashi daga kamun idan suka kalleta sai sun dara,washe gari henna day,ranan ma haka aka sha dariya Dadda ta shiga cikin wanda akama k'unshi,ranan jumu'a sukai dinner iya familyn kad'ai,sai abun nasu ya zama kamar wani reunion,ba k'aramin kyau yayi ba ranan dai sari ne duka suka sa color d'aya,mazan suka sa suit color d'in sarin matan,ranan jumu'a aka sake jaddada aurensu aka musu marriage certificate,sai dare aka raka amare sabon apartment biyu da Raj Jarood yasa aka yi kusa da juna duk a cikin gidan..