Sashe 49
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Wani kallo ta dunga binsa da shi,ya d'aure fuskarsa yace "bar kallona ko na sauke ki nan yanzu" da sauri ta d'auke kanta hawaye har sun fara sakkowa fuskarta,tace "wallahi sai na daina zuwa skul d'in" ya d'age shoulder yace "ruwanki ne kiyi duk yadda kika ga dama" harararsa tayi za tayi magana yace "ina kallonki kici gaba" murgud'a masa baki tayi ta juyar da fuskarta tana kallon waje,har suka shiga Sardauna crescent bata sake masa magana ba shima bai ce mata ba,Ameerah kuwa tunda ta maida hankalinta kan wayarta ko sauraron abunda suke fad'a ma bata yi,ya tsaya get d'in gidan ya bud'e motar ya fita,Manar ta d'aure fuska ta k'i sauka har ya bud'e back seat ya d'auki ledar da ya ajiye ya rufe,Ameerah tace "Yaya mu jira ka a mota?" Ya kalleta yace "ku zan barma ajiyar motar?" Babu shiri taja bakinta tayi shiru ta bud'e ta sauka,ya kalli Manar da ta wani hard'e hannuwa a k'irji yace "get down my friend" sake kautar da kanta tayi tak'i kallonsa yace "idan kika bari na zo inda kike baza kiji dad'i ba" ta bud'e motar ta fito sai b'ata rai take,ya gyad'a kansa ya wuce forefront suka bisa a baya,ya tsaya bakin get yayi knocking,get keeper ya lek'o suka gaisa da Waleed yana kallonsu da rashin sani yace "wa kuke nema?" Waleed yace "arhmm! Gurin Hjy muka zo" mutumin yayi saurin bud'e musu k'ofar suka shiga,shi yayi musu jagora har entrance sai da yayi knocking maid ta bud'e k'ofar,get keeper d'in yace "bak'i ne sun ce gurin Hjy suka zo" da sauri tace su shiga,suka masa godiya suka wuce cikin parlon,Manar da Ameerah sai kalle² suke,saman lafiyayyun royals chairs d'in Waleed ya zauna Manar ta zauna kusa da shi Ameerah ta zauna one seater,maid tace "bari a fad'a mata" Waleed yace "alright" ta wuce sama da sauri,not too long suka fara jiyo maganar Hjyr cikin k'asaita tana tambayar maid "basu fad'a miki daga gidan da suke ba?" Tace "ehh Hjy" tab'e baki matar tayi ta sakko tana kallon su cike da rashin sani,garama Waleed ta nuna alamun kamar ta ganesa,suka gaisa da su Waleed yace "Hjy Asama'u ta aiko mu" sakin fuskarta tayi tana fad'ad'a fara'arta tace "kar dai kace min Waleed ne a gabana?" Yayi murmushi yace "ni ne Hjy" tace "ikon Allah.. Waleed k'ai ne ka zama haka? Yaushe rabona da ganinka?" Ya sosa backhead d'insa yana sakin murmushi,tace "masha Allah! Ya karatu fa ko aiki zance?" Yace "aiki ne Hjy" tace "da kyau! A ina kake aikin?" Yace "prime hospital" tace "maa sha Allah! Allah taimaka" yace "ameen" maid ta k'waloma kira,jikinta na b'ari ta zo tace "ga ni Hjy" cikin fad'a tace "wannan wane irin halin banza ne? Na yi bak'i baki kawo musu ko ruwa ba,kina aikin me?" Tace "kiyi hak'uri Hjy ina had'a musu abun motsa baki kika kira ni" wani tsawa Hjyr ta mata da sai da Manar ta tsorata ta rik'e hannun Waleed,tace "c'mon dallah kar ki b'atan rai,kun san aikinku amma kullum sai an koya muku,sai kace baku san dalilin da yasa mutum ya d'auke ku ba" da sauri ta bar gurin tana ba-ta hakuri,Hjyr tayi murmushi ganin Waleed ya sunkuyar da kansa tace "kuyi hak'uri fa wallahi halin maids d'in kenan dole sai sun sa mutum jin kunya" Waleed yayi murmushi yace "babu komai Hjy,dama sak'o ta bayar tace a kawo miki,sauran bayanin za ta miki a waya" tace "to babu laifi" ya mik'a mata ledar da Mama ta bayar a kawo mata,ta bud'e tana dubawa,Manar dai sai kallon parlon take sai da Waleed ya tab'ata yace "ke meye haka?" Ta waiga ta kallesa,ya d'auke kansa kad'an a hankali yace "sai ance miki y'ar k'auye za ki nutsu?" Ta d'auke kanta bata sake yarda ta kalli komai ba ta basar sai dai fa ba wai ta hak'ura da kalla ba ta wutsiyar idonta take kallon da dabara,bayan ta gama duba kayan ta ajiyesu gefe tace "aikam kaya sunyi kyau" shi dai Waleed bai ce komai ba sai mik'ewan da yake k'ok'arin yi yace "Hjy za mu koma" tace "da wuri haka,ko ruwa fa baku sha ba" yayi murmushi yace "za mu sha wani lokacin" tace "a'a Waleed idan kai ba ka sha su ai za su sha ko y'an mata?" Da sauri Manar tace "ehh za mu sha" wani kallo ya mata ta wutsiyar idonsa,Ameerah dai bata ce komai ba,Hjy Sahiba tace "kuma ko gaisawa da *AFIYAH* ma baku yi ba kake cewa za ku tafi" yayi d'an murmushi yace "da yake ba gida za mu koma ba,akwai aiken da za mu kai kuma shi yasa" tace "okay! Bari nasa a kirata ku gaisa ko a tsaitsaye gudun wata rana kada ku had'u a hanya baku san juna ba" yace "haka ne" wata maid d'in daban ta k'waloma kira tace "ki kira min Afiyah su gaisa" ta haura sama da sauri,ba'a jima ba ta dawo tace "Mummy ta ce kada a dameta tana da uzuri" Hjy Sahiba cikin fad'a tace "zancen banza ma kenan,baki ce ni nake kiranta ba hala?" Maid tayi shiru sanin halin fad'an Hjyr,a tsawace tace "kije kici ni nake kiranta ba-na son shirme" komawa tayi ko minti biyu ba'a yiba,sai ga wata matashiya zabiya (albino) tana sakkowa cikin shagwab'a da wani siririn murya tace "Mummy wai ke kike kira na?" Hjy Sahiba ta kalli yarta dake sanye da crazy jean da wani gantalallen riga mai off shoulder tana washe baki tace "yeah! Ga Waleed nan ku gaisa" ta mata maganar tana nuna mata inda suke,gaba d'aya bata kula da mutum ba sai da Mummy'nta tace mata ta ko waiga suka had'a ido da Manar,suka kalli juna suka d'auke kai,Waleed da tun sakkowarta bai d'aga kansa ba yayi busy wajen danna wayarsa,sai da yaji muryarta tana gaisar da shi ya d'ago ya tura wayar aljihunsa,without looking at her ya amsa,ita kam sai kallonsa take da idanunta da take kuma k'ank'antarwa saboda hasken da ya mata yawa ta zauna wing d'in chair da mahaifiyarta take tana sake binsa da kallo,maid ta kawo musu snacks and drinks ta ajiye,Manar ta d'auki maltina ta bud'e ta sha,Ameerah dai ta k'i tab'a komai sai kallonsa take sai da Hjy Sahiba tace "Ameerah ke baki sha ko drink ba" Ameerah tayi murmushi tace "am ok ni dai" Hjyr tayi dariya tace "ko dai kina tsoron Waleed ya miki fad'a?" Da sauri Ameerah ta girgiza kanta tana yin murmushi tace "a'a na k'oshi ne" Hjy Sahiba tace "a'a ban yarda ba.. Bari ayi muku take away sai ku tafi da shi ko?" Manar dai sai cin cake take da paper chicken da aka kawo musu" Waleed couldn't not stop looking at her ta wutsiyar idonsa ji yake kamar ya maketa sai dai babu hali,Hjyr tasa maid ta had'a musu kayan suka mata sallama za su tafi ta d'auko 10k ta bawa su Manar tace su sha ice cream,murna sosai Manar tayi ita ta karb'a ko d'an irin a barshin nan,maids suka biyo su da kayan har waje inda yayi parking suka sa musu cartons d'in lemo da ruwa a booth sauran kuma Ameerah ta karb'a ta ajiye gefenta suka yi musu sallama Waleed ya ja motar suka tafi,ko line basu gama bari ba Waleed ya fara yiwa Manar fad'a kamar zai cinyeta d'anya,ta had'e rai tace "to Yaya an bamu abu kuma sai muce a barshi?" Yace "idan baza kuce ba sai aka ce ana cewa ga shi ku karb'a? Jira kuke a baku kenan?" Tayi shiru,ya mata tsawa yace "ba dake nake ba?" Ta zumb'uro baki tak'i cewa komai,yayi k'wafa yace "gobe zabga wanda za ku sake bi" tace "kai za mu bi" da sauri ya taka brake ya kalleta a hasale yace "ni kika ce?" Ta girgiza masa kai da sauri tace "nifa bance komai ba" yayi k'wafa yaci gaba da driven,har suka je gida bai sake mata magana ba,yana yin parking ya bud'e ya fito musu da kayan yace "maza ku d'auka ku b'ace min d'aga gani" kafin ma ya k'arasa ta fizgi carton d'in malt d'in ta yi gaba,ya bita da kallo bai ce mata komai ba,Ameerah ta fito ta d'auki na ruwan da ledar da aka basu tabi bayan Manar,sai da yaga shigarsu gidan ya juya ya shiga na su gidan,a bedroom ya tarar da Mama yayi sallama,ta d'ago tana masa murmushi tace "Waleed! Har ka dawo?" Yace "ehh! Ta ce a gaishe ki" tace "muna amsawa,oa same su lafiya?" Yace "lafiya lao" shiru ya d'anyi then ya tashi yace "sai an jima" sanda yaje bakin k'ofa ta kirasa,ya tsaya a gurin ya waiga,tace "kun had'u da Afiyah?" Shi dai so yake kawai ya bar d'akin yace "ehh mun had'u" tayi wani murmushi tace "good.. Ya ka ganta,i mean ta yi maka matsayin matar aure?" Wani zaro ido yayi yace "zabiya ce fa" tace "zabiya ba mutum bace?" Ya girgiza kai yace "no! I just mean ni gaskiya ba irinta nake son.." Bai karsa ba tace "ni kuma itace tayi min,and ita na zab'ar maka matsayin matar aure.."