← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 184

Sashe 23

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a hankali ta sauke wani bayyanannen ajiyar zuciya jin ba abunda take tunani bane,but duk da haka bata fasa fad'in "ni dai na fad'a maka babu kai babu ita,kabi hanyarka itama tabi nata,bana son ko wane irin kusanci yana had'aku,kai idan da dama ma ko hanya ta bi kada ka kuskura ka bi,ka canja wani kawai shi ne abunda nake buk'ata,hakan shi zaisa nayi farin ciki kuma ya ba-ni nutsuwa" gyad'a mata kai yayi a hankali cike da wani irin mutuwar jiki yace "done!" Tayi masa murmushi tace "good" then ta juya za ta fita,da idanu ya bita yana jin gabansa yana tsananta fad'uwa saboda k'aryan da ya yanko mata,ya san halin fad'anta akan yar k'aramar magana sai ta masa babu dad'i,kome kuma zai fad'a mata ba yarda za tayi ba but yana had'awa da Abba sai gashi har ta fita,a hankali ya rufe idanunsa yana tunanin maganganunta,wani tambayar da yake yawan yiwa kansa game da alak'arsa da Manar da Mama ba-ta so,ba tun yanzun ba abun ya tsaya masa a rai,iya bincikensa kuma ya kasa gane gaskiyar dalilin Mama na son datse alak'ar nasu,shin me yasa yake hango tsana mai girma a idanunta duk lokacin da aka ce mata wani abu ya had'asa da Manar? Wannan amsar ita ne ta gagaresa samu har yau,ya rasa kuma wanda zai tambaya ya bashi amsa. Tana fita d'akin fakam² take tafiya,underneath ta fara zana munanan kud'urinta towards Manar,ta bud'e bedroom d'inta ta shiga lokacin duka yaran basa nan already sun fita,ta mayar da k'ofar ta kulle,bakin gadonta ta k'arasa ta zauna,wani tunani ne ya fad'o mata a rai,da sauri ta d'auki waya ta fara kiran line aminiyarta Hjy Izzatu,bugu d'aya a na biyu ta d'auka da fad'in rai ta furta "k'awata ya gari?" Hjy Asama'u tace "lafiya,ba lafiya ba" da sauri Hjy Izzatu tace "tofa! Wani matsalar ya faru?" Mama tace "ina gudun ace haka ya faru Hjy" Hjy Izzatu tace "me yake faruwa?" Mama tace "ina ga gobe zan shigo,maganar ya fi k'arfin muyi shi a waya" amsawa Hjy Izzatu tayi da "alright! Allah kawo ki lfy,sai kin shigo d'in" suka yi sallama,ajiyar zuciya Mama tayi tana gyad'a kai,a fili ta furta "dole ne na tsaya a kanka Waleed,idan ma akwai abunda yake tsakaninku kake b'oyemin,tabbas zan shiga na rabasa.." Da safe lokacin Waleed ya shiga apartment d'in gaida Dadda ya tarar bata nan,da murnanta Manar ta d'auko wayarta ta nufesa tace "Yaya ina kwana" bai kalleta ba ya amsa,ya nemi guri ya zauna,ta k'arasa kusa da shi ta zauna tace "Yaya ka ga wayana da.." Bata k'arasa ba taga ya wani irin juyo ya kalleta sai da ta tsorata tayi baya,ya zuba mata idanunsa yace "waye ya baki damar rik'e waya?" Rau² idanunta suka yi tace "Yaya Azaan ya aikomin da shi" d'aure fuskarsa yayi yace "Azaan?" Ta gyad'a masa kai,gyad'a kai yayi yace "ba ni na gani" girgiza masa kai tayi,ya kafeta da idanunsa ganin da gaske baza ta bashi ba ya mata tsawa yace "ba ni nace" jikinta har b'ari yake ta mayar da hannuwanta baya ta b'oye ta ci gaba da girgiza masa kai,yace "baza ki bayar ba?" Da sauri ta gyad'a masa kai,murmushi yayi yana lumshe idanunsa yace "kada ki bari na kamaki baza kiji dad'i ba" zumb'uro masa baki tayi tace "to ba k'wacewa za kayi ba?" Yace "haka kika ji na ce miki?" Ta girgiza masa kai tace "to ai na san haka ne" gyad'a kai yayi bai sake mata magana ba ya kawar da kansa daga kanta,jan jikinta ta fara yi tana matsawa,ba tare da ya kalleta ba yace "ina za kije?" Da sauri ta mik'e hannayenta a bayanta tana b'oye su ta juya za ta gudu,yana sane yasa mata k'afa,saura kad'an ta fad'i k'asa yayi sauri ya fizgota ta fad'a jikinsa,a tare suka saki wani marayan ihu,k'amshin scent's d'insa da suka kaiwa hancinta ziyara da fad'uwan da tayi ba a k'asa ba yasa tayi saurin bud'e idanunta,idanunsa a kulle yana sauke numfashi a hankali,Manar dake jikinsa yadda taji yana kara cuddling d'inta yana wani k'ara kulle idanu yasa ta fara mutsu² tana son tashi,a hankali ya bud'e lumsassun idanunsa ya saukesu kan kyakykyawar fuskarta,tura baki tayi a shagwab'e idanunta suna tara hawaye tace "Yaya ka sake ni" d'aure fuskarsa yayi yace "ni zan sake ki ko ke za ki d'aga ni?" A shagwab'e tace "to ba kai ka rik'e ni ba" wani kallo ya mata kafin yayi saurin janye hannayensa da ya zagayeta da su yana aika mata harara yace "sai ki tashi ai" da sauri ta mik'e daga jikinsa tana zumb'uro masa baki ta juya bayanta,ya harareta maimakon ya tashi kawai sai ya sake gyara kwanciyarsa ya lumshe idanunsa,juyawa tayi za ta bar gurin ta jiyo maganarsa "kuna da ruwan zafi?" Tace "ehh akwai a flask" ya gyad'a kai daga kwancen da yake yace "je ki had'a min tea" saurin juyawa tayi ta kallesa tace "Yaya yau alhamis fa" idanunsa a rufe yace "I knew" tayi still tana kallonsa tace "Yaya ba kana azumi ba yau?" Bai bud'e idanunsa ba yace "ina ruwanki?" Ta zumb'uro masa baki tace "to ba gani nayi duk litinin da alhamis kana yin azumi ba?" Yace "za kije kiyi abunda na saki ko sai jikinki yayi tsami?" Da sauri ta juya tace "Allah baka hak'uri" bai kulata ba ta juya ta shiga kitchen ko minti uku ba'a yi ba ta fito da mug cike da ruwan zafi,tana k'arasowa inda yake tace "Yaya" bud'e idanunsa da suka d'an birkice yayi ya kalleta,tace "ga shi" ya kalleta yana d'aure fuskarsa yace "mene ne wannan?" Tace "ruwan zafin daka tambaya" yace "haka nace kiyi min?" Ta tsaya kallonsa,ya sake d'aure fuskarsa yace "ba dake nake ba kika kafe ni da idanu?" Juyawa tayi tana k'unk'uni ya gyad'a kai yace "ina jinki ki gama zagina" saurin juyowa tayi tana kallonsa,fuskarta kamar za ta fasa kuka tace "nifa bance komai ba,yace "nayi miki k'arya" ta girgiza kanta da sauri tace "a'a.." Wani kallo yayi mata yace "me kika ce?" Kamar za tayi kuka tace "nifa ban ce komai ba" ya gyad'a kai yace "k'aryar dai kike nufin na yi miki,right" kafin ya sake magana tuni hawaye har sun wanke mata fuska,ya sake gyara zama ya zuba mata sexy idanunsa,cikin matuk'ar d'aure fuska yace "idan kika bari ruwan nan yayi sanyi za ki ji jiki" share hawayen tayi saurin yi ta koma kitchen sai b'ata rai take ta had'a masa lafiyayyen tea thick one,ta dawo ta kawo masa,ya karb'a yana kallon spoon data sa yace "waye yace miki ina shan tea da spoon" ba tare da ta ce komai ba ta d'auke,ta juya ta koma kitchen ta ajiye,tana fitowa ta tarar ya ajiye mug d'in yana danne² a wayarta data ajiye,ta dunga kallonsa gabanta sai fad'uwa yake,tana kallon mug d'in ta fara tunanin masa magana,a hankali tace "Yaya shayin zai huce baka sha ba fa" bai d'ago ba yace "wani yace miki ina shan abu da zafi?" Tayi still tana kallonsa,mamakinsa yasa ta kasa sake cewa komai,kusan mintuna biyar ya d'auka kafin ya kai hannu ya d'auki mug d'in ya kai bakinsa,idanunsa har lokacin akan wayar yace "me kike kallo?" Tayi saurin girgiza masa kai tace "babu komai" yace "idan akwai dai ki fad'a" sake girgiza masa kai tayi,daga haka bai sake tambayarta ba parlon yayi shiru,sanda ya kusa shanye tea d'in tace "na d'auko maka bread?" Ya girgiza mata kai alamun baya so,ta juya tayi shiru tana tunanin wayarta da ya d'auka,ba tare da ya kalleta ba yace "je ki kunna min TV" tashi tayi ta kunna,ta dawo ta zauna hankalinta akan TV amma zuciyarta ta yi nisa gurin tunani,tsaf ya gama dube²n da zaiyi ya ajiye wayar kusa da nasa,ko cikakken minti biyu ba'ayi ba aka fara kiranta,ya kalli screen d'in sunan wanda ya gani yana kira yasa shi d'aure fuskarsa,har kiran ya katse aka sake kira bai ce mata komai ba,ring d'in da taji yana sake tashi yasa ta d'aga idanunta ta kalleshi tana jira taji ko zai ce tazo ta karb'a but har kiran ya sake katsewa ko tari yak'i yi,for the third time ana sake kira yayi tsaki ya mayar da wayar silent,Manar da taji bai ce mata komai ba ta sunkuyar da kanta tana matsa fingers d'inta,ya jima sosai a gidan kafin ya tattara belonging d'insa ya nufi hanyar fita,ta d'aga kai ta bisa da kallo sanda ya kai k'ofa kamar ance ya juya,yana waigawa yaga shi take kallo ya tab'e baki ya k'arasa ficewa,kuka ne ya kwace mata da gudu ta tashi ta shige d'aki ta fad'a saman gado,bayan ta yi mai isarta bacci ya d'auke ta sai da Ameerah suka dawo skul ta shigo ta tasheta,tana bud'e idonta ta fara jan zuciya Ameerah ta zuba mata ido tace "me ya faru sis?" Wani kukan ta fashe da shi,hankalin Ameerah a tashe tace "tell me please! What happened? Me aka miki?" Da muryar kuka tace "ya k'wace min wayana" Ameerah ta zaro ido tace "waye?" Tace "Yaya" still tayi tana kallonta kafin tace "ya akayi yaga wayar?" Manar cikin kuka tace "nice na nuna masa" dafe forehead Ameerah tayi saurin yi tace "kema fa sai da nace miki kada ki bari ya gani zai kwace,shi ne baki jiba kika kai masa,ai ga shi nan kin janyo ya kwace" tana share hawaye tace "ara min naki na kira Yaa Azaan" Ameerah tayi shiru da farko then tace "sai dai idan baza ki fad'a masa ba" Manar tayi saurin kallonta tace "wa zan fad'awa?" Ameerah tace "shi Yayan" gyad'a mata kai tayi tace "bazan fad'a masa ba" Ameerah tace "promise?" Manar dake kallonta tayi squeezing fuskarta tace "me?" Ameerah tace "kinyi alk'awari?" Da sauri ta gyad'a mata kai tace "ana bu'udak" murmushi Ameerah tayi then ta mik'a mata wayar,da sauri ta karb'a da yake ta haddace number Azaan a kanta nan da nan tayi saurin sakawa ta fara kiransa,lokacin Azaan yana driven kamar bazai d'auka ba da farko ganin da number Nigeria ake kiransa yayi shiru yana tunani kafin yayi parking gefen hanya,ya d'auka yasa wayar hands free,muryar Manar ya ji ta ce "hello! Yaya" da sauri ya katse ya kirata back,hannunta har rawa yake ta d'auka da muryar kuka² tace "Yaa Azaan" tana jinsa yayi ajiyar
Chapter 23 · 0% Book details