← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 184

Sashe 103

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

da kallo har ta k'arasa shigowa ta ajiye,tace "Yaya ga abincin" ya gyad'a mata kai yace "thank u" ta fita tace "Yaya sai mun dawo" bai ce mata komai ba ya bita da kallo zuciyarsa a cunkushe,ko minti goma ba'ayi da fitar Manar ba Afiyah ta shigo gidan,ta mata kallon banza itama ta mata,ta wuce ciki ta samu Mama da Hjy Izzatu can k'arshen d'aki suna k'us²,suka gaisa Mama tace "to kin kirasa ne?" Afiyah ta gyad'a mata kai tace "ehh! Ya ce min zai yi wanka" Mama tace "alright! Let me call him muji yana ina yanzu" ta d'auki wayarta ta fara kiran line Waleed,Waleed dake tsaye gaban mirror ya kalli wayar ya sauke numfashi ya d'auke kai,sanda aka sake kira ya kai hannunsa yayi answering yasa wayar a handsfree,Mama ta fara cewa "Waleed kana ina?" Yace "ina bedroom" tace "ka tafi gida ne?" Yace "a'a ina nan" tace "alright!" Ta katse wayarta da sauri tana kallon Afiyah tace "maza tashi kije yana d'akinsa ki samesa daga nan ki sanar masa za muje unguwa" Afiyah ta amsa ta tashi ta fita,bedroom d'insa ta bud'e ta shiga,ya waigo da sauri jin an bud'e k'ofar idanunsa suka sauka kan Afiyah dake shigowa,ta k'arasa kusa da shi tana kallonsa tace "sannu da dawowa D" bai tanka ta ba ya wuce ya ajiye towel d'in hannunsa,Afiyah ta k'arasa a hankali ta zauna bakin gadon tana sake kallonsa,ya gama duk abunda zaiyi ya zauna yana cin abincin da Manar ta kawo masa,seeing that bai da niyyar mata magana tace "D za mu d'an fita da Mama" bai d'ago ba yace "baza kije ba" ta masa wani kallo tace "kamar ya bazan je ba?" D'ago idanunsa yayi yana kallonta yace "kamar dai yadda kika ji na fad'a" a tsiwace tace "wallahi baka isa ba Waleed,tun yaushe ka hanani fita,kai kayi tafiyarka ni ka hanani,akan me za ka nemi kulleni ni ba matar limami ba" bud'a idanuwa Waleed yayi yana kallonta yace "really?" Ta gyad'a masa kai tace "tabbas" ya gyad'a kai yace "okay! U can go,but let me tell u this,billah idan kika sake k'afarki ya taka wani waje without na amince daga can inda kika je ki wuce gidanku and don't even think zan biyo ki.." Saurin kallonsa tayi tace "me kake nufi?" A fusace yace "abunda duk kwakwalwarki ya fahimtar dake" Afiyah ta mik'e tsaye cike da tsageranci tace "wallahi baka isa ka hanani zuwa inda nake so ba" ya gyad'a kai fuskarsa a d'aure yace "okay! Let's see.. Tsakanin ni ko ke muga wanda ya isa" da sauri ta fice a fusace ta nufi d'akin Mama kamar za ta tashi,ta tura k'ofar da k'arfi ta tsaya door way sai huci take,a tare Hjy Izzatu da Mama suka kalleta suna had'a baki suka ce "lafiya?" Afiya ta fashe da wani kuka kamar dama jira take wani ya tanka mata tace "ki kirasa ki masa magana don idan har ban fita ba yau shirin da muke yi ne zai ruguje" Mama ta zaro idanu tace "wani abu yace?" Afiyah ta sanar mata yadda suka yi da shi,cikin b'acin rai Mama ta gyad'a kai tace "kyaleni da shi kawai,na san yanda zan masa,dan na ga take²nsa halinsa na da yake k'ok'arin dawowa da shi" daga haka ta tashi ta fita d'akin,Afiya tana ta zaune har bayan minti talatin ganin Mama bata dawo ba har sannan ta mik'e ta bi bayanta,ta samesu Mama sai balbalin fad'a take masa,Afiyah na shigowa ya d'ago fuskarsa d'aure zai yi magana Mama ta hanasa,dole yayi shiru har dai ta gama ta fita,ya dunga mata wani kallo yace "kina tunanin fad'an da kika sa mahaifiyata tayi min zai sa na barki ki fita?" Ta nufesa tace "wai me ke damun ka ne Waleed,ni dai na san lafiyar ka k'alau ka tafi.." Ko kallonta bai yi ba ya tattara kan phones d'insa zai fita,da sauri ta fad'a jikinsa ta baya tana shafa chest d'insa cike da shagwab'a tace "ni dai wallahi ka gaya min meye laifina,kawai daga zuwanka ka fara min hayaniya" bata jira cewarsa ba ta juyo da shi ta rungumesa gam tana k'ara shige masa,lokaci d'aya tayi turning him on. Sanda yayi mata laga² ya huce haushinsa a kanta,ya sauka gadon ya wuce bathroom ya tsarkake kansa,ya fito ya sameta tana waya tana jin motsinsa tace "I'm coming fa yanzun bari nayi wanka na zo" tayi saurin ajiye wayar ta wuce bathroom,yana kwance idanunsa a rufe ta fito ta gama shiryawa,ta k'arasa kusa da shi ta zauna gefensa tana tab'asa a hankali tace "Dear zanje Mama suna jirana za mu wuce" calmly ba tare da ya bud'e idanunsa ba yace "i said u are going no where ko?" Ta zaro ido tana kallonsa da mamaki don duk tunaninta ya hak'ura,ta d'an marairaice tace "haba dear,ba fa dad'ewa za.." Da sauri ya katse ta ya mik'e zaune fuska a d'aure yace "i'm telling u this wallahi idan kika fita gidan nan yau za kiga the other side of me" yana fad'in haka ya mik'e ya fice,ta bisa da kallo zuciyarta sai tafarfasa take,can ta mik'e ta fice daga d'akin ranta a mugun b'ace taje ta sanar da Mama tace "ya fa k'i bari na biku Hjy,taurin kan Waleed da kafewan da yake kan abu wallahi ni dai tsoro yake bani" da mamaki Mama tace "ya k'i bari ki kifita kuma?" Afiyah tace "ehh" Mama ta gyad'a kai tace "yana ina?" Afiyah tace "ya fita fa" Mama ta gyad'a kai ta fara kiransa a waya,cikin takaici ta sauke wayar tana kallonsu tace "toh ai wayar tasa a kashe yake" Afiyah tace "yanzu ya za muyi to?" Mama tace "ina ga mu bari anjima idan an fara tafiya gurin bikin sai mu fita" Afiyah ta tab'e baki bata ce komai ba..
Chapter 103 · 0% Book details