Sashe 24
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
zuciya yace "na'am baby" kuka ta fashe da shi,a rikice yace "Subhanallah! What happened? Waye ya tab'a min ke?" Toshe bakinta tayi saurin yi,hawaye wani na bin wani,Azaan sai magana yake mata ta kasa amsawa,da sauri ya katse kiran hankalinsa a mugun tashe ya kirata video,tana ganin kiran ta kasa d'auka,shi kuma ya kasa hak'ura sai kiranta yake sake yi,Ameerah dake kwance ta zubawa sarautar Allah ido ganin Manar ba ta da niyyar d'auka ta fizge wayar tayi answering,da wani breaking voice yana ganin an d'auka ko gama tantance fuskar waye akan wayar baiba ya fara tambayar "Baby tell me what happened,me aka miki,ke da waye?" Ameerah tace "Yaa Azaan ita da Yaya ne fa" da sauri Azaan yace "Ameerah! Ita da wane Yayan ne?" Tace "Yaya Waleed" idanu ya zuba mata yana maimaita "Waleed! Me ta masa? Can u explain me ya had'a su?" Ta gyad'a masa kai tace "wayarta ya kwace mata" Azaan yace "ya kwace,for what reason?" Girgiza kai tayi tace "nima ban sani ba,na dawo skul yanzun take fad'a min" gyad'a kai yayi yace "tun yaushe ya karb'a?" Tace "i don't know,amma ina jin tun safe ne" lumshe idanunsa yayi yace "alright! Ba ni ita muyi magana" mik'awa Manar wayar tayi,ta kasa karb'a sai kuka take,Ameerah tace "Yaa Azaan tak'i karb'a fa" da sauri Azaan yace "Baby!" Kina jina?" Ta gyad'a kai bata d'ago ba,yace "kukan ya isa haka,dan ya karb'i wayan kike damuwa?" Tayi sauri ta d'ago kanta wasu hawayen suna sauka cheeks d'inta tace "ni ba a kansa bane" yace "Uhn! Tell me akan mene ne to?" Da muryar kuka tace "kana ta kira ban d'auka ba,na san ka yi fushi" wani beautiful smirk ya sakar mata yace "banyi fushi ba dear,yanzun ba gashi na san dalilin k'in d'aukan kiran ba" saurin karb'ar wayar tayi daga hannun Ameerah tace "da gaske?" Ya gyad'a mata kai yace "absolutely sure dear" tayi murmushi ta share hawayen,ya sake yi mata murmushin da yake k'ara masa kyau,a hankali yace "ki daina kukan haka nan,anjima za'a kawo miki wani kinji?" Gyad'a masa kai tayi,ya sake yin murmushi yace "shi kenan?" Tace "Ehh!" Yace "ina Dadi?" A shagwab'e tace "bata nan" yace "ina ta tafi?" Tace "ta je gidan k'awarta" gyad'a kai yayi yace "sai ku kad'ai ta bari?" Tace "ehh!" Ya gyad'a kai yana lumshe idanunsa yace "alright! Later za muyi waya idan na k'arasa gida ina hanya kika kira" ajiyar zuciya tayi tace "to! Allah tsare hanya" yayi mata murmushi yace "ameen.. Thank u" tace "ina gaisar da Momellah" ya amsa mata,ita ta fara katse kiran,tana d'agowa ta saki ihu,da wani muryar shagwab'a tace "sai yayi ta karb'ewa,ai dai ga shi za'a k'ara kawo min wani" Ameerah tayi dariya tace "Iyeeeee! Y'ar gatan Yaa Azaan" Manar tayi murmushi had'e da yin fari da idanunta tace "ya son ranki?" Ameerah tace "Aahhh! Normal" saurin tashi manar tayi tace "ke ni banyi sallah ba" tayi sauri ta dira daga gadon,bayan ta idar hira sosai suka yi kafin yunwa tasa su tashi suka fita zuwa gidan mother..