← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 184

Sashe 51

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikinsa har tsuma yake wajen tambayarta "Mama ita wannan d'in?" Tace "yes! Itafa!" Yace "Mama please.. Dan Allah ki bari na nemi type d'in da za tayi dai² da ni,wallahi Mama ni dai yarinyar nan sam bata min ba" wani kallo ta dunga binsa da shi,a wani iri tace "na barka ka nemi type d'in da za tai maka?" Yayi shiru bai yi magana ba,cikin hasala tace "Waleed! Wai ni sa'ar wasanka ce?" Yayi k'asa da kansa yace "i'm sorry Mama" taci gaba da fad'a "idan ba kana son mayar da ni sakarai ba,ni zan nema maka mata kace min bata maka ba? Yarinya y'ar gidan mutunci" ya d'ago a hankali ya d'an marairaice fuskarsa yace "i'm so sorry Mama,ni ina da dalilin da yasa nace miki haka" a fusace tace "dalilinka na banza da wofi? Wallahi Waleed ka mayar da hankalinka jikinka,kafin na sab'ar maka,ka san Allah da gaske idan ka turje zan gwada maka k'arfin ikona,anything can happen at anytime wallahi" numfashi ya sauke a hankali yace "Mama kina ganin yin haka shi ne dai²? Nifa na fad'a miki ina da personal problem da zaisa nak'i amincewa" Mama dai sai kallonsa take ranta a b'ace tace "Waleed ni kake fad'ima haka?" Ya girgiza mata kai yace "no! Mama ya kamata ki fahimce ni,idan kika ce sai na aureta zai iya kasancewa na cutar da ita,u know already i've my own problem,she's not my type and she can't take me at all.. Idan kun takura aka yi auren a haka za mu cutar da juna ne kawai.." Gaba d'aya idanun Mama suka rufe gani take kamar raina mata hankali yake son yi ta k'ara fututtuke fuska tace "na rantse da ubangijin sammai da k'assai bakwai idan ka ga an fasa abun nan sai dai in yarinyar ce tace ba ta so,amma dan kai baka isa bad'a min k'asa a idanu ba,wallahi baka isa ka kunyatar da ni a gurin aminiyata ba" shiru yayi kawai ya rasa abun da zai sake fad'a mata ta gane me yake nufi,though ya fad'a a yanayin da dole ma sai ta gane d'in,yadda ta rufe ido tana masa fad'a nan da nan yaji ransa ya b'aci a fusace ya juya ya bar mata gurin,tana masa magana ma ko saurarenta bai tsaya yi ba ya fice,gidan Dadda ya wuce sai huci yake kamar kububuwa ya shiga babu ko sallama,Dadda da su Manar sun baje suna kwasar garar arziki,sunyi dumu² da paper chicken da suka zo da shi,Manar ta d'aga kai tace "Hjy kuma fa har kud'in ma ita ta bamu" Dadda tace "dubu goma fa" Manar tace "ehh ai dan baki ga gidan ba,da ba za kiyi mamaki ba ma,ko Meerah?" Ameerah ta gyad'a kai dai² lokacin Waleed ya kwanta kan kujera ya dafe kansa da yake jin ya fara sara masa,Dadda ta d'auki wani k'aton tsoka ta kai baki tace "Iiiiiihhh kuma shi mutumin fa me yace?" Manar ta d'ago ta saci kallonsa,shigowarsa yasa ta fasa fad'awa Dadda abunda tayi niyya,da sauri ta d'auki nasa kason da Dadda ta ware masa ta matsa kusa da shi tace "Yaya" bai iya d'agowa ba yace "leave me alone please.. I'm not in the mode" sororo ta tsaya kansa tana kallonsa ta sake cewa "Yaya!" A fusace ya d'ago kamar zai bugeta yace "I said leave me alone" wani kuka ne ya kwace mata tsabar firgitar da yasa tayi ta juya da sauri za ta wuce d'aki ya rik'o hannunta,cikin kuka tace "ni ka kyale ni" ya furzar da wani zazzafan numfashi yace "zo ki zauna muyi magana" ta girgiza masa kai tace "ni bazan zauna ba" ya mata wani kallo yace "sit please" sai da ta kalleshi kafin ta zauna,ya kalli Dadda da ta kafesa da idanu hannunta rik'e da namanta kamar wadda akayi pausing ko irin a shirin film d'innan,shi kansa da baya cikin yanayi mai dad'i sai da tasa ya murmusa ya juya ya kalli Manar a hankali ya rad'a mata "ko dai muje backyard muyi hira?" Da sauri ta kalleshi ya d'aga mata girorinsa,tace "toh" ta tashi shima ya mik'e,Dadda da ta bisu da kallo baki sake tace "ikon Allah.. Ni dai ban gane wannan k'us² da kuke yi ba,ko kuma dai wani sabon gulma da kinibibi ne hakan?" Waleed da ya kai k'ofa ya waiga yace "sai dai ki biyo mu kiji" ta saki baki har ya fita bata kuma cewa komai ba,sai kwafar da tayi tace "y'an banten uba,da ni kuke zance har gadon barci na za ku same ni" shi dai tuni suka yi gaba suka barta tana mita,a bayan ya ganta ta zauna kan wani dakali ya k'arasa yana kallonta ya zauna kusa da ita,gaba d'aya suka yi shiru ita tana kallon shuke² da bishiyun da suke kad'awa suna k'ara wadata gurin da yalwatacciyar iska,tayi ajiyar zuciya a hankali tace "Yaya na fara jin bacci" ya kalleta da kyau yace "really?" Ta waigo ta kalleshi,yayi murmushi yace "mu bar maganar ba yanzu ba?" Tace "a'a ka fad'a kawai" sai da ya ja fasali kafin yace mata "Mama ta nema min matar aure" zabura tayi bata san daga ina ba taji maganarsa ya sa ta k'warewa,da sauri ya matsa ya rik'eta sosai a jikinsa yana shafa bayanta,sai da ta koma normal ya janye hannunsa yayi shiru yana tunani damuwa k'arara a fuskarsa,wani dariya Manar tayi cikin murna tace "Yaya yaushe ne auren?" Ya zuba mata idanunsa yana kallon yadda take murna yace "kina farin ciki da auren?" Tace "sosai ma ni fa Yaya ban tab'a ganin anyi biki ba a gidan nan" ya maka mata harara yace "wai ke baki ji komai ba ma?" Tace "me zan ji?" Haushi ne yasa shi cewa "ban sani ba" tayi dariya tace "Yaya Allah ni dai murna nake yi za kayi aure,ka ga zan samu gidan da zan dunga zuwa ina yin hutu ko?" Kallonta ya dunga yi da mamaki ita matsalarta kenan,yace "wait.. Kin san wacce zan aura ma?" Ta girgiza masa kai,yace "wannan yarinyar" squeezing fuskarta tayi tace "wacce?" Yace "ta gidan da muka kaje.." Idanunta ta zaro tace "Yaya wannan zabiyar?" Ya gyad'a mata kai ransa yana kuma b'aci,wani dariya ta fashe da shi cike da wauta tace "shi kenan Yaya sai kuyi ta haifar k'warori" ya d'aure fuskarsa yace "waye ya fad'a miki haka?" Tana dariya tace "to ba ita zabiya bace" yace "dan tana zabiya ni kuma fa?" Kallonsa ta tsaya yi,ya d'aga mata gira ganinin kallon da take masa yace "what?" Tace "Yaya kuma kana sonta?" Gab'a d'aya ya d'auke wuta ya rasa wane irin amsa zai ba-ta,ta kai hannu ta tab'asa tace "Yaya!" Ya d'an dawo nutsuwarsa fuskarsa tana bayyanar da damuwa yace "ba na jin sonta at all" k'uri ta masa da ido tace "to Yaya itafa tana sonka?" Ya tab'e baki yace "ban sani ba" shiru tayi tana kallonsa fuskarta babu isashshen walwala tace "to Yaya kai me yasa ba ka sonta?" Ya d'aga kansa looking to the sky kamar yana counting stars a hankali yace "there's some special,wanda aka halicceta daga jikina,aka halicceni da komai nawa saboda ita,ita kad'ai nake muradin aure,itace kadai zuciyata ta aminta da ita,nake kuma fatan mu rayu k'ark'ashin roof d'aya" dariyar da ta kyalkyale da shi ne yasa shi kallonta yace "me ya baki dariya?" Ta tsagaita tace "kai ne mana Yaya na ji sai magana kake kamar malamin soyayya" ya lumshe idanunsa kad'an yace "baza ki gane irin son da nake mata ba" gyara zamanta tayi tana kallonsa tace "Yaya to kai me yasa baka fad'a mata kana sonta ba?" Yace "there's someone da yayi intervening tsakanina da ita,and abunda yasa ban fada mata,but i just don't know ko itama tana sona kamar haka? Ko kuma dai ni kad'ai nake haukan sonta" Manar tace "kaiiii! Yaya son maso wani fa kenan kake yi" yayi murmushi mai ciwo yak'i cewa komai,ganin yayi shiru ta d'ora hannunta kan kafad'arsa tace "Yaya me yasa to baza ka fad'awa Mama kana da wacce kake so ba ta kyaleka?" Ya girgiza mata kai cike da jimantawa kansa yace "ta ruga da ta yanke hukunci tun farko" wani zaro ido ta sake yi jin ya ambaci sunan Mama a karo na biyu ta san ma ba abun arziki zai biyo baya ba tace "to Yaya auren dole Mama za ta maka ne?" Ya gyad'a kansa yace "kusan haka ne" wani tausayinsa taji da taga fuskarsa ta sauya,ta kwantar da kanta jikin kafad'arsa,a hankali tace "ni dai Yaya idan ba ka son auren ka fad'awa Abba to ko Dadda mana,su ai Mama za taji maganar su" ya girgiza mata kai yana jin wani tuk'uk'in bak'in cikin da ya tokare masa wuya yace "no way Baby,dole ne nayi hak'uri na karb'i auren" tace "saboda me?" Ji yayi idanunsa sun cika da kwalla ya daure yace "she said idan ban amince ba za ta tsine min" wani irin tausayi taji ya ba ta tayi shiru ta d'auke wuta,gaba d'aya ta shiga damuwa,almost 2 hours suna zaune babu wanda ya sake magana sai tunanin da zuciyoyinsu suke,ganin dare ya fara yi sosai ya sauke numfashi yace "ta shi muje na raka ki gida" ta d'ago kanta daga jikinsa jikinta duk a mace ta mik'e a hankali,ya tashi shima suka jera babu mai iya cewa komai suka zagaya,sai da yaga shigarta kafin ya lumshe idanunsa a hankali ya bud'e yana shak'ar numfashi then ya juya ya fara tafiya cikin nutsuwa. A yadda Waleed ya wuce ya barta tsaye a gurin ganin tana masa magana bai kula ba,hakan yasa ta sake shak'a,it was there ta yanke shawaran kiran Hjy Sahiba a waya,bayan sun gaisa Hjy Sahiba tace "na ga aikenki,but Waleed ya ce za kiyi min bayani ko?" Mama ta sauke wani numfashi tace "yeah! Later my friend,yanzun dai akwai maganar da na kira muyi" Hjy Sahiba tasa serious tace "wane magana ne?" Mama tace "a zahirin gaskiya yau na turo Waleed gidan ki ne for nothing other than suga juna da Afiyah,idan zai yuwu mu had'a su aure.." Hjy Sahiba ta gyad'a kai tace "wow that's very good.. Amma gaskita aminiya kinyi tunani mai kyau" Hjy Asama'u tace "fatan dai baku mata miji ba" da sauri Hjy Sahiba tace "ko anyi mata ma ai sai mu fasa tunda
Chapter 51 · 0% Book details