← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 184

Sashe 32

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da yamma lokacin Amaar ya dawo daga aiki ya shiga apartment d'in Dadda ya tararta ita kad'ai tana mitar b'ata mata d'aki da su Manar suka yi suka fita without sun gyara,yayi murmushi ya k'arasa shiga yayi sallama,bata amsa ba ta d'aga kai ta kallesa ta d'auke kai,murmushi yayi yace "Hjy Manar fa?" Wani kallo ta masa ta d'auke kai ta ci gaba da sakace hak'orinta,bai damu ba ya sake cewa "Hjy ko sun miki laifi ne kika k'i kulani?" Kamar ya tsokanota tayi k'wafa cikin jin haushi tace "idan ba ma sun raina ni ba dama su b'ata guri kuma su tafi su barshi haka kaca²,yanzu ni suke nufi zan sake gyara musu?" Amaar ya girgiza kai yace "a'a gaskiya basu kyauta ba" ta gyad'a kai tace "yara sai k'azantar tsiya malam,su dai babu daman suga guri tsaf² sai sun k'azancesa" Amaar kamar zai yi dariya saboda yadda take kambama maganar,ya juya da sauri yace "Hjy bari na turosa su gyara miki gidan" ta d'aga kai ta bisa da kallo,har ya kai bakin k'ofa ta tab'e baki ta d'aga murya tace "dama baka wahala ba,wad'annan sakarkarun babu abunda suka iya,sai shegen surutu malam kamar sun ci aku.." Dariya ce ta kwace masa yayi sauri ya k'arasa fita yace "bari dai naje na dawo Hjy" ba tare da ta tankasa ba ya fice,apartment d'in Mother ya tsaya yayi knocking Ameerah ta bud'e k'ofar,tana ganinsa tace "Yaah Amaar sannu da dawowa" ya gyad'a mata kai yace "Manar fa?" Juyawa tayi bata bashi amsa ba ta k'walama mata kira,Manar dake zaune tace "mene ne wai?" Tace "kizo inji Yaah Amaar" da murnanta ta taso ta k'araso gurin tana washe masa baki ta gaishesa,ya d'aure fuska yana kallonsu yace "maza ku wuce muje" kallon juna suka yi kafin Manar tace "ina za mu Yaya!" Ya juyo ya kalleta yace "cewa nayi ku wuce ko na ce wata tayi magana ne?" Sum² suka wuce forefront ya kallesu yace "kun san inda za ku da kuka wuce?" Suka tsaya suna kallonsa,ya maka musu harara ya fara wucewa forefront suka bisa a baya,suna shiga suka ga Dadda zaune a parlor sai kad'a k'afa take,Manar ta d'aure fuska itama Ameerah tayi kicin² tak'i kallonta,Amaar ya nemi guri ya zauna in a serious note yace "maza ku d'au tsintsiya ku gyara gidan kafin na b'ata muku rai" sum² suka yi suka wuce kitchen suna hararan Dadda da tak'i kallonsu,yana zaune suka gama sharar suka goge,duk da yana musu wasa amma idan ya had'e rai bala'in tsoronsa suke,suna gamawa ya mik'e zai fita yace "Hjy sai da safe" d'aga kai Dadda tayi ta kalli parlon da yayi k'al² sai k'amshin room freshener yake tayi wani murmushi tace "to d'an fodiyo,sannu kai dai ka ji,Allah maka albarka" ya amsa yana murmushi ya nufi k'ofa,har ya kusa fita ya kira Manar,she thought ko zai sake sa su wani aikin kuma bata iya amsawa ba kawai ta fashe da kuka tace "Allah Yaya na gaji" saurin juyawa yayi yana kallonta tana matsar idanu,sanda ya gama k'are mata kallo yace "dallah rufewa mutane baki,kin ji na ce kiyi min wani abu ne da za ki b'arewa mutane baki?" Da sauri Dadda ta kallesa fuskarta cike da damuwa tace "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Haba d'an fodiyo,me kuma tayi za ka kwad'a mata tsawa haka?" Ba Amaar kad'ai ba hatta Manar da Ameerah sai da suka kalleta,Amaar yayi squeezing fuskarsa yace "me ya faru kuma?" Cikin fad'a Dadda tace "yo wannan uban tsawan da kayi ko ni sai da y'ay'an cikina suka juya bare Manar da take k'aramar yarinya,irin haka ai babu dad'i,kuma ni sai naga jarumtarta da ta tsaya iya zubar da hawaye kad'ai" Amaar ya dunga kallonta mamaki ya hanasa sake mata magana,Dadda tace "ni dai idan ba abun arziki ya kawo ka ba dama ka fitar mun daga gida Allah tashe mu lafiya" gyad'a kai yayi ba tare da ya ce komai ba ya juya yana tafiya yace ma Manar "idan kin gama kukan ki zo ki karb'i sak'onki da Azaan ya bayar a kawo miki" ya k'arasa maganar yana ficewa daga apartment d'in,tana jin ya ambaci Azaan da sauri ta biyosa ko jira bata yi taji abunda Dadda za ta ce ba Ameerah ta rufa mata baya,a parking space suka gansa yana bud'e motarsa,suka k'arasa suka tsaya ya d'auko ledan dake ajiye d'aya kujeran yana mik'a mata ya rufe motarsa ya bar gurin,Ameerah ta karb'a ta bud'e taga sak irin wancan da Waleed ya k'wace colour d'in ne da bambanci,cikin tsananin murna suka juya zuwa part d'in Dadda,suna shiga cikin karad'i Manar tace "Dadi kinga sabon wayana da Yaa Azaan ya sa a k'ara.." Bata k'arasa ba suka yi ido hud'u da Waleed dake zaune,babu shiri ta had'iye sauran maganarta,Waleed ya zuba mata ido yana kallon yadda take tafiya hannunta a b'oye a bayanta tana zumb'uro masa baki,Ameerah ma tana ganinsa ta juya za ta fita ya mata tsawa yace "idan kika sake k'afar ki ya fita daga gidan nan ni da ke ne" babu yadda za tayi ta dawo ta tsaya,Manar za ta shiga d'aki ta b'oye wayar kafin ta kai k'ofar bedroom yace "kema idan kika bari k'afar ki ya taka cikin d'akin nan jikinki zai fad'a miki" saurin juyowa tayi ta kallesa ta kalli Dadda da tak'i musu magana,bai kalli inda take ba yace "me Azaan d'in ya bayar aka kawo miki?" Tayi shiru tak'i cewa komai,ya mata tsawa yace "ba dake nake ba kika min shiru?" Kuka ta fashe da shi ta juya da gudu ta shige d'akin,ya gyad'a kai ba tare da ya kalli direction d'in Ameerah ba yace "mene ne take fad'a?" Ameerah cikin tsoro tace "Yaya nima ban sani ba fa" yace "k'arya kike" da sauri tace "believe me yaya ban san komai ba" wani kallo ya d'ago ya mata yace "ba tare na ganku yanzu a parking space ba?" Tayi tsuru² tana in'ina,ya sake mata tsawa yace "za ki fad'a min abunda ya faru ko sai na zaneki?" Hawaye suna zubowa idanunta tace "waya ya bayar a kawo mata" still Waleed yayi yana kallonta kafin ya maimaita "waya?" Tace "ehh" ya gyad'a kai yace "je ki karb'o ki kawo min" bata masa musu ba ta wuce tana shiga ta samu Manar tana rusa kuka,kaf maganar da Waleed yayi babu wanda bata ji ba,cikin kuka tace "ni to me na masa da zai na kwace min waya?" Ameerah tana share hawaye tace "kiyi hak'uri Sis kawo na kai masa in yaso sai na baki na wajena kiyi amfani da shi" Manar ta girgiza kai tace "ni dai bazan bada wannan ba" Ameerah tace "please ki kawo zan d'auko miki wancan d'in na wajena kinji?" Manar tace "ni wallahi bazan basa ba" yana jiyo rigimar su ya taso da kansa ya bud'e k'ofar yana kallonsu ya tsaya bakin k'ofa bai k'arasa shiga ba,fuskarsa a d'aure yace "d'auko ki kawo min" da farko k'in kai masa tayi sanda taji ya ce "idan kika bari na tako nan na sameki jikinki zai fad'a miki" babu yadda za tayi ta d'auka tana zuwa ta tsuguna ta ajiye masa a k'asa,ya mata tsawa yace "nan nace ki ajiye?" Ta zumb'uro baki ta d'auka ta mik'a masa,ya zuba mata idanu yace "daga yau duk wanda ya kuskura cikin ku na k'ara ganin waya a hannunsa.." Bai k'arasa ba ya gyad'a kai ya juya,kai tsaye ya wuce zai fita daga apartment d'in Dadda da tun d'azu ta zuba masa idanu tak'i ce masa komai ta kada baki tace "Afff! Ka mance baka karb'e na gurin Ameerah ba ai" wani juyowa yayi yana kallonta ta tsuke fuska tace "meye kake kallona ai tuna maka nayi ni" wani murmushi yayi bai ce komai ba ya juya ya fita daga gidan,tun da Manar ta tabbatar ya tafi mata da wayarta take kuka,ko cikin dare ta farka tana tunawa sai ta fashe da kuka,ranar gaba d'aya ta hana Dadda da Ameerah sukuni,kafin safiya ciwon kai mai tsanani da zazzab'i mai shegen zafi ya rufeta..

#Share pls.
#Asli Smasher.
💠💠💠💠💠
©®2021.

*♡MANAR¸.•💥*

*WATTPAD:REAL-SMASHER898.*
https://t.me/joinchat/VHlmxxheyxG6m9VoUJZbZA

_Devoted to My Mamma Hjy Maryam Alhassan (Jikar Kulu)._

_Bestowed to Fateema Abdulmajid._

11.

#Forbidden..
Chapter 32 · 0% Book details