Sashe 166
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
bata kwankwasa k'ofar ba ta fara rad'a sallama,kamar a mafarki Amaar da suke parlor dukansu su shida sun sa yaran a gaba suna lissafin yanda hidimar suna zai kasance ya kallesu yana bud'a idanu yace "kamar maganar Hjy Siyama naji" Azaan yayi wani dariya yace "haba malam ita da take naija d'in za kaji maganarta a nan? Kada fa kamanta nan India ne and a yankin Vishakpatnam kake kuma" Amaar yace "tou shi kenan bari na duba dai" ya tashi ya nufi k'ofa Azaan na masa tsiya,yana bud'e k'ofa kuwa yaci karo da fuskarta ya ware idanunsa yace "hajajju.." Sai kuma ya juya ya bata hanya yana kallon Azaan yace "hey buddy! Didn't i told u maganarta naji kake min musu?" Dadda dai tuni ta shige ta barshi tsaye a nan yana surutu,Azaan ya kallo Dadda dake shiga yana dariya yace "sannu da hanya Dadi.." Ta washe baki hak'orin makkanta hud'u suka bayyana tana kallonsa tace "sannunmu dai Mamman,na sameku lafiya?" Azaan yace "lafiya lao,ya mutanen Nigeria?" Tab'e baki tayi tace "yo suna can mana sai sanda suka ga dama su zo" Ameerah tace "kai Hjy maimakon ku taho tare" wani kallo Dadda ta mata tace "iiiihhh! A jakata zan zubosu mu taho,ko kuwa gammo zan nad'a na kawosu nan d'in dole?" Gaba d'aya parlon suka fashe da dariya,Manar tace "sannu da zuwa Hjyrmu" Dadda ta juya ta kalleta tana rik'e hab'a tace "o'o sannu y'ar nan,Allah dai ya rabaku lafiya kou?" Manar tayi murmushi bata ce komai ba,Dadda ta sauke mayafinta ta nemi guri ta zauna tace "tou Allah ya raya abunda aka samu" su Ameerah suka amsa da ameen,nan suka fara gaisawa,kafin kace me kayan arziki har sun fara biyo Dadda daga b'angaren Rani Naheed da gurin Mommella,ita kanta b'angaren Manar d'in haka hadimansu suka fara fito da kayan motsa baki,Dadda ta bud'a idanu tana kallon kayan da aka cika gabanta da su,tace "iiiihhh! Tou ina mutum zai kai wannan kuma fisabilillahi? Sai kace na koma mai cikin zani za'a kawo min wannan uban kayan duka?" Ameerah tace "kici iya cinki Hjy ki bari" Dadda tayi saurin kallonta tace "kamar ya inci iya cina in bari haka babu dad'in ji? Tsakani da Allah ku baku san almubazzaranci babu kyau ba? Kuyi ta dafa abinci ba iya cinyewa kuke ba,sai anyi magana kuce Allah ya hore muku ku da iyayenku" yanda take fad'a tsakaninta da Allah duk sai da ta basu dariya,da taji haushi tace "ai sai kuyi ta dariyan,gaskiya dai guda d'aya ce,in karasa wanda zai gaya maka dole kayi kuka.. Aaatoohh!" Azaan ya sauka kusa da ita ya zauna bil'hak'k'i yace "kiyi hak'uri Dadi baza a kuma ba,za'a d'auki maganarki" ta tab'e baki bata kulasa ba ta fara zurama cikinta abinci masu dad'in d'and'ano da gasassun y'an shila na dangin tsuntsaye daban² tana lumshe idanu,sanda ta gama tayi hamdala,da iska ya fara ratsata here ta fara hamma,jikokin suka fara mata dariya da tsiya,suna cewa "bayan ci,zama tsaigumi,tafiya rashin kunya,kwanciya lalaci,tsuguno neman dad'i" ita dai bata tanka su ba nan ta b'ingire sai bacci,ba ita ta farka ba sai guraren maghreb,bayan ta yi sallah ta yi addu'o'inta tace a kira mata Yaro su zanta,sanda ta sanar masa ta sauka lafiya,suka tab'a hira kafin suka yi sallama,lokacin kuma ta kalli Waleed ta mayar da hankalinta kansa,a nan ta fara rattabo masa jawabin za ta tafi da Manar da yaran masaukinta dan ta samu damar yi mata sahihi kuma ingantaccen wanka kamar yanda yake a al'ada..