← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 184

Sashe 100

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Afiyah tayi tace "ai kuwa idan haka ne ya zama dole na kirasa na lallab'asa har ya dawo" Mama cikin zumud'i tace "yawwa yar gari, idan ya tambayeki kice masa kin koma gidan tuni saboda gudun b'acin ransa" Afiyah ta gyad'a kai tace "yeah! That's why nake k'ara sonki my in-law" Mama tayi wani murmushi tace "to ya za'ayi,ai dole ya zame min na soki Afiyah saboda ke yar Sahibata ce" Afiyah tayi dariya tace "let me call him muji ya ake ciki" Mama tace "maza yi hanzari ki kirasa" sai da Afiyah ta yima Waleed kusan kira biyar bai d'auka ba har ta ji haushi za ta ajiye ta fasa dai ta k'ara kiransa,Waleed da duk kiran da ake masa yana kallo ganin daman d'auka ne baiba,sanda ya gaji da ganin kira daga number da bai san na waye ba ya d'auka cikin hasala yace "who's this fool da yake kira,ba ku san kuyi hak'uri ba idan kun kira sau d'aya ba'a d'auka ba?" Afiyah da taji wani b'acin rai kan maganar da Waleed ya fad'a ta daure tace "it's me Afiyah" saurin daga wayar yayi yana kallon number kafin ya mayar da ita kunnensa yace "ohh! How are u and what's up kike kira na by this time around?" D'an shiru tayi tana had'iye b'acin ranta tace "dama na kira ka ne tunda kai baka kira ba since ka tafi" ya tab'e baki yace "okay thanks zan kashe ina wani uzuri yanzun" Afiyah tace "alright but ai ya kamata ka saurareni da uzurin da yasa na kiraka ko?" Waleed cikin hasala yace "don't tell me that rubbish.. think munyi magana dake kika rantse sai kin rafi gidan ku?" Afiyah cikin kwantar da murya tace "but after then ai na koma gidanka ko?" Waleed yace "kada kimin k'arya" Afiyah tace "da gaske nake maka fa na koma,ka tambayi mahaifiyarka kaji" yayi wani murmushi yace "okay let me call u" bai jira cewarta ba yana sakin wani murmushi ya katse ya kirata video dan ya tabbar da gaske tana gidan nasa ko a'a,sanda Afiyah taga kiransa wani zaro idanu tayi tana nunawa Mama call d'in tace "me zan ce masa yanzu idan ya ganni a nan?" Mama tayi shiru tana tunani har sai da kiran ya katse,Hjy Izzatu tace "think he calls don ya tabbatar da maganarki na cewa kina gidansa,and if muna son ya yarda yabi all maganar mu ya zama dole mu koma gidan yanzun" Afiyah tace "but i think.." Da sauri Hjy Izzatu tace "don't say anything! Kawai ku tashi mu tafi aiwatar da abunda zai fiye mana,idan mun gama sai mu dawo" here suka yi shirin tafiya,sanda suka isa gidan get keeper ya bud'e musu yana masu barka da zuwa,suka shige compound d'in babu wanda ta damu ta amsa masa gaisuwarsa,Afiyah tayi parking suka fito suka wuce cikin gidan da sauri,mugun k'ura suka tarar gidan ya yi,Mama da Hjy Izzatu suka shiga suka d'auko tsintsiya suka fara karkad'e chairs,sanda suka share parlon tsaf suka goge,suka haura sama shima suka gyara,d'akin Afiyah kam sanda suka bud'e kallon² Mama suka yi ganin yanda Afiyah ta cika gadonta da kaya duk kuma sun yi k'ura,but haka suka shiga suka gyarasa suka kwashe kayan suka wanke suka shaya mata,kafin suka koma k'asan suka tarar da Afiyah zaune tana danne² a wayarta,dai² lokacin Mama tace "ki k'ara kiransa muji" Afiyah ta gyad'a kai tace "okay!" Then ta kira Waleed,kamar ba zai d'auka ba da farkon ya daure dai ya yi answering call d'in,Afiyah cike da kissa tace "D ka kira ni ina bathroom" Waleed yace "okay! We will talk later" ya katse wayar ba don ya yarda da abunda tace ba. Almost two days ranar da za'a fara biki ya shirya dawowa without ya sanarma kowa yana tafe,ko da yama driver waya yaje ya d'aukosa sai da ya masa warning kada ya sanarma kowa yana hanya,daga airport kai tsaye yace ma driver ya wuce da shi gidansa idan ya huta zai je su gaisa,driver yana saukesa gidan bayan sun gaisa da get keeper ya wuce ciki,gently yake tafiya yana k'arema ko ina kallo,sanda ya tsaya balcony ya danna bell,shiru d'in da yaji yasa shi cire keys d'insa ya bud'e,tun daga saka k'afarsa cikin parlon ya fahimci Afiyah ba ta nan kamar yadda ta sha masa k'aryan tana nan,ya gyad'a kai ya k'arasa shiga a nutse ya haura sama ya shigar da trolley d'insa bedroom then ya zaro wayarsa ya kirata,tana d'auka yace "where have u been?" Tace "ina gida fa" yace "wane gidan?" Tace "gidan mu mana" d'an shiru yayi then yace "gidan ku kika tafi?" Da sauri tace "a'a ina fa gidan mu ni da kai" wani gyad'a kai yayi yace "but i didn't see u.. Kin shiga wani guri kin b'oye kanki ne?" Afiyah ta zabura ta mik'e zaune tace "ban gane ba? Ina zanje ni kuma?" Kai tsaye yace "okay! Fito ga ni cikin gidan ina jiranki" wani zaro idanu tayi kafin tace k'ala ya katse wayarsa ya juya ya fita daga d'akin...
Chapter 100 · 0% Book details