Sashe 6
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani shegen kallo Mama ta dunga aikawa Aunty fuskarta a d'aure tace "me kike nufi Bebie?" Dariya Aunty tayi tace "ya za ki tambayeni bayan kinfi kowa sanin abunda nake nufi?" Mama ta dunga gyad'a kai tana kallonta kafin tace "okay! Ta nan kika b'illo?" Aunty tayi dariya ba tare da ta sake cewa komai ba ta wuce za ta koma sama,Mama ta d'aga murya tace "da kin zauna ai munyi.. In banda shishshigi ma har akwai wata uwar mijin da zan dunga ma rawar jiki? In ba neman wurin zama da son a sani ba" juyowa Aunty tayi saurin yi ta kalleta tace "kin ji ai inda aka samu matsalar,da kin san darajar mahaifiya tabbas baza ki k'i nunama uwar mijinki so ba,sannan baza ki k'i yi mata kallon mahaifiya ba" cikin sauri Mama tace "me kike nufi?" Aunty tace "ohoo! Dubawa za kiyi" ta wuce ta barta nan kamar za ta fashe tsabar b'acin rai. Suna fita Manar ta kalli Ameerah tace "wai ina su wad'ancan suke?" Ameerah tace "su wa kike nufi?" Tana squeezing fuskarta tace "ya-ma sunan su?" Dariya Ameerah ta fara yi kafin tace "wai kina nufin kin manta sunan su?" Seriously ta gyad'a mata kai,Ameerah tace "lallai Manar d'an tafiyar nan shekara hud'u har yasa kin fara manta mutanen gidan nan?" Kicin² Manar tayi tace "to ki tuna min mana kuma" Ameerah tace "Deejah da Diyanah" kyab'e baki tayi tana gyad'a kai tace "Mmm!" Daga haka bata sake cewa komai ba suka k'arasa apartment d'in,suna tsaye balcony ta hango fitowarsa daga part d'in da suka baro,ta zuba masa idanu tana kallonsa sanye yake da k'ananun kaya sai sauri yake ya nufi parking space,Ameerah tayi knocking k'ofar tana yiwa Manar tambayar "Sis! Wai kuma za ku sake komawa Saudi?" Manar bata kalleta ba tace "Ehh!" Ameerah tace "when?" Juyowa tayi saurin yi lokacin da taga fitarsa daga gidan tana squeezing fuskarta tace "ni ki min da hausa ban gane ba" Ameerah tayi murmushi tace "sai yaushe?" Hannuwa ta watsa tace "ohoo! Nima ban sani ba,sai lokacin da Dadda tace" Ameerah ta gyad'a kai tace "alright!" Sake knocking tayi ganin ba'a bud'e musu ba har lokacin,daga ciki akace "ana zuwa.." D'an yaro ne k'arami bazai wuce 5yrs ba ya bud'e k'ofar,Manar ta kallesa tayi masa murmushi,tace "marhaba akhul'sagir" wani gwalo ido yaron yayi da gudu ya koma cikin karad'i yana fad'in "Mother ga aunty ta zo" kyakykyawar matar dake fitowa daga bedroom wadda baza ta wuce 47yrs ba d'auke da yarinya a kafad'arta kana kallonta za ka hango kamar da suke da yaranta dake nan a parlon suna faman TV game,tana kallon yaron tace "wace Aunty'n?" Yace "Auntyn mu ta saudiyya ce suka zo" juyawa tayi saurin yi tana amsa sallamarsu,idanunta akan Manar tace "yaushe kuka zo?" K'arasawa tayi ta karb'i baby girl dake hannun mother tace "ba'a dad'e ba" mother ta gyad'a kai tace "sannu ya hanya?" Gaisar da ita Manar ta fara yi,ta amsa sai kallon yadda ta k'ara girma take,Ameerah ma ta gaisheta ta amsa,mother ta juya tana kallon yaran y'an matasa su kusan biyar da suka cika parlon da ihu tace "Mu'awiyah! Maza ku kashe game d'in nan haka" saurin kashewa suka yi suka taso suna yiwa Manar sannu da zuwa,sai murmushi take yi tana kallonsu,mother ta mik'e tayi hanyar kitchen ta barsu a parlor,abinci ta fito musu da shi dining,tana kallon su tace "kuzo kuci abinci" Ameerah tace "ni dai mother i'm full" saurin tashi Manar tayi ta nufi dining d'in bata yi magana ba,Ameerah da ta karb'i baby a hannunta ta bita da kallo baki sake tace "kai Sis! Yanzu fa Aunty tace kici abincin kika k'i" wani kallo ta juyo ta mata tace "to ina ruwanki da ni?" Ameerah tayi dariya tace "Allah baki hak'uri amma dai ki dunga fad'ar gaskiya" b'ata rai Manar tayi tace "to baki ga wancan matar tana gurin ba" Ameerah ta bud'a idanu tace "wace ce matar da take gurin?" Manar ta zumb'uro baki tace "Mamar su Yaya mana" tsawa mother tayi mata tace "iskancin da kika koyo kenan? Hjy Asama'un kike cema haka?" Manar ta d'ago tana kallon mother kamar za tayi kuka ta kasa magana,mother tace "dake nake kika tsare ni da kallo" sunkuyar da kai tayi ta zumb'uro baki,mother ta fara mata fad'an ba ta son rashin kunya,Manar ta fashe da kuka ta tashi da gudu ta fita,Ameerah tana kwalo mata kira bata tsaya ba ta tashi da sauri za ta bita mother tace "d'auki abincin ki kai musu daughter,kice ina gaida Hjy,ina mata barka da zuwa kafin na shigo" Ameerah ta amsa ta d'auki warmers d'in dake cikin wani folded basket ta fita da sauri,a parlor ta tarar da Manar kwance kan kujera tana kuka,ta kalleta ta ajiye basket d'in,Dadda ta fito daga d'aki tana fad'in "waye yake kuka kuma a nan ni Azumi?" Ameerah ta juya tace "Manar ce" saurin k'arasowa Dadda tayi har kamar za ta fad'i tsabar sauri tana sakin salati tace "me aka mata kuma?" Ameerah tace "ita da mother ne" wani kallo Dadda tayi mata tace "wace ce haka kuma?" Ameerah tace "Aunty Mammy" mitsi² Dadda tayi da idanu,bata tsaya sauraren abunda take fad'a ba tayi waje,kamar za ta b'alle k'ofar take bubbugawa,mother dake zaune tana bawa jaririyarta nono ta jiyo bugun ta kwalo ma Mahmoud kira,ya fito daga d'akinsu yace "here i'm mother" tace "je kaga waye yake bugun k'ofa" amsawa yayi ya wuce,yana bud'ewa Dadda ta kalleshi fuskarta a tsuke bata ko amsa gaisuwar da yake mata ba ta fara tambayarsa "Ina ita uwar taku take?" Yace "tana ciki" wucesa tayi ta shigo,mother dake zaune ta d'ago kai tace "sannu da zuwa Hjy" kicin² tayi tace "ba sannu da zuwanki nake buk'ata ba,zuwa nayi naji me yarinya tayi miki daga zuwa za ki sa ta kuka?" Mother ta saki baki tana kallon Dadda tace "wani abu taje tace na yi mata?" Dadda ta tsuke fuska tana mata wani kallo tace "ni ya za'ayi na sani? Zuwa nayi dai naji dalilin kukan nata" a hankali mother ta sauke ajiyar zuciya tace "babu abunda aka mata" wani kallo Dadda ta dunga aika mata tace "ba'a mata komai ba za taje min tana kuka? Wallahi ahir d'inki Maryam,ki fita idanuna na rufe,akan yarinyar nan zan iya sab'awa ko waye,ni ba na son haka daga zuwanmu dan neman rashin son zaman lafiya za ku fara sa yarinya kuka,ni sai na hanata zuwa gurin ki idan abunda za ki na mata kenan,ko nasa ta a gaba mu koma inda muka fito" fad'a sosai Dadda ta dunga yi kamar za ta aro baki,mother ta sauke numfashi tace "kiyi hak'uri Hjy in sha Allah baza'a kuma ba" Dadda ta juya a fusace tace "zai fi miki dai" tana fita mother ta rufe idanunta cike da takaici,tayi shiru tana tunanin anya idan tayi shiru ta zuba ido akan tarbiyyar Manar ta yi dai²? Abun yana damunta ba tun yanzu ba,kawai kara take yi ta zuba musu idanu,ba komai take iya d'aga ido ta kalla ba musamman idan ya shafi Manar. A parlor Dadda ta samesu Amaar ya shigo suna hira,ta kalli Manar dake b'ab'b'aka dariya ta washe baki hakor'in makkan ta suka fito tace "yawwa! Saki ranki takwara,yanzu na je na samu Maryam d'in na mata tatas,baza ta sake miki abunda za kiyi kuka ba har mu koma" sakin baki Manar tayi tana kallonta gabanta sai fad'uwa yake a tsorace tace "me kika je kika ce mata?" Dadda ta fara rattabo mata jawabin duk abunda tace,Manar ta dunga kallonta kamar za tayi kuka,da sauri ta tashi ta fita daga part d'in,karo suka kusa yi da Waleed a balcony yana k'ok'arin shigowa ya rik'eta da sauri yana mata wani kallo yace "ba kya kula idan kina tafiya ne?" Idanunta sunyi rau² ta rik'e masa hannu a tsorace tace "Yaya dan Allah muje ka rakani" kallonta yayi fuskarsa a d'aure yace "ina zan raka ki?" Hawaye suna sakkowa fuskarta tace "zan je na bawa mother hak'uri" wani kallo yayi mata yace "laifin me kika yi?" Tana share hawayen fuskarta a shagwab'e tace "to ba Dadda bace dan ta ga ina kuka taje.." Wani kallo ya dunga mata fuskarsa a d'aure ya mata tsawa "kauce ki ba-ni guri kafin na mareki" wani irin kuka ta fashe da shi da sauri ta fizge hannunta ta wuce da gudu ta nufi part d'in,ya juya yana kallonta sanda ta kusa shigewa ya sauke ajiyar zuciya then ya biyo bayanta,gently kamar mai counting steps d'insa yake tafiya ya bud'e k'ofar ya shiga da sallama,fad'a sosai ya tarar mother tana mata,ya samu guri ya zauna mother ta dakata suka gaisa,a hankali yana kallon Manar dake kuka yace "kiyi hak'uri mother in sha Allah baza ta kuma ba" girgiza kai mother tayi cike da takaici tace "Waleed al'amarin Manar da grandma d'inku ya fara damuna,ban san yaya zanyi ba,duk sanda yarinyar nan za tayi laifi ayi mata fad'a kakar ku tana jin labari za tazo ta maka tatas,akan yarinyar nan wane irin cin mutunci ne bama gani,yarinya sai kace ita kad'ai aka haifa,fisabilillah yanzu shi kenan duk abunda za tayi sai dai a sa mata ido,babu wanda ya isa ya mata gyara idan tayi ba dai² ba?" Waleed yace "kiyi hak'uri in sha Allah za a san yadda za'ayi" mother cikin takaici tana kallon Manar dake matsar idanu tace "itama kuma da yake makira ce kana mata fad'an abunda take yi sai ta b'are baki ta kwasa taje ta fad'a mata.. Gaskiya na gaji da abubuwan da suke faruwa akanta,duk ranar da naga babu haza billah za'a neme ni a rasa cikin gidan nan,bazan iya ci gaba da zaunawa ina kallon b'acin rai ba" hak'uri Waleed ya dunga ba-ta sanda yaga ta d'an sakko kafin ya kalli Manar dake zumb'uro baki a tsawace yace "baki iya bada hak'uri ba ne?" D'agowa tayi tana kallonsa tak'i cewa komai,ya zuba mata ido yana kallonta,ta d'auke kai kamar ba da ita yake ba tana hararan wani guri,bata yi zaton ya ga abunda tayi ba sai ji tayi ya ba-ta rankwashi,ta dafe gurin da sauri a gigice tace "kiyi hak'uri mother" mother ta dunga mata wani kallo cike da takaici ta kasa mata magana,ran Waleed ya b'aci sosai but haka yayi k'ok'ari ya danne