Sashe 66
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Part d'insu ta shiga,cikin sand'a ta wuce kitchen ta had'o masa abinci da tea d'in da yace mata,ta had'a komai cikin basket ta d'auka ta fita,tana tsintar kanta balcony da ta tabbatar babu wanda ya ganta tayi ajiyar zuciya ta kulle k'ofar a hankali,ta juya za ta tafi kenan taga Azaan tsaye yana kallonta,tsabar tsoron da taji sai da zuciyarta ya bada wani rass ta daure tana masa murmushi tace "Yaya! Barka da dare" ya amsa yana kallon hannunta da take b'oyewa cikin hijab yace "Guddi what are u hidden?" Ta sake yin baya da hannunta tace "ni ban b'oye komai ba" yace "really?" Ta gyad'a masa kai,yace "mmm! Fito dashi muga" girgiza masa kai tayi da sauri bata tsaya ba tayi gaba tana zumb'uro baki tace "i said babu komai fa" tsabar mamakinta yasa shi kasa tafiya sai da yaga shigarta gidan Dadda then ya juya yana tafiya a hankali cikin compound d'in,ta tura k'ofar parlon a hankali ta rufe tana satar kallon k'ofar Dadda ta shige,a zaunen da ta barsa a haka ta tarar da shi k'afafunsa a k'asa ya rik'e kansa da hannu biyu,ta k'arasa ta ajiye basket d'in tace "Yaya.." Bai iya amsawa ba sai da ta zuba masa black tea d'in a cup tace "ga shi Yaya" a hankali yace "ajiye zan d'auka" ta dunga kallonsa kafin tace "zai yi sanyi ai" yace "ina kayan da nace ki kawo min?" Tace "yanzu zanje na d'auko" ya bud'a idanunsa kad'an ya d'ago ya kalleta,yadda tayi da fuskarta kamar kana mata magana za ta kece da kuka,ya d'auke kansa ya zuba idanunsa akan cup d'in tea data ajiye masa,sympathetically take kallonsa tace "sannu.." Ya d'an gyad'a mata kai kad'an yace "thank u" then ya d'auki cup d'in ya rik'e a hannunsa,Manar dai sai kallonsa take tana jera masa sannu,yace "je ki kawo min kayan please" tashi tayi za ta fita,har ta je k'ofa ta waiga tace "wanne zan kawo maka?" Yace "anyone ki kawo min" ta juya ta fita da sauri,har ta shiga gidan babu wanda suka had'u da shi,ta bud'e d'akinsa ta shiga,though ba yau ne karo na farko da ta fara shiga d'akin ba haka nan ta tsaya k'arema d'akin kallo kafin ta d'aga k'afarta ta nufi press d'insa ta bud'e ta ciro masa wani milk d'in yadi sai hula da takalmi,ta tsaya kad'an tana tunani kafin ta juya ta bud'e k'ofar ta fita,dai² lokacin Azaan yana bud'e k'ofar d'akin Amaar zai shiga,suka had'u a corridor d'in ya kalleta ta kallesa,bai dai ce mata komai ba ta wucesa ta sauka k'asa tana zumb'uro baki ya bita da kallo,sanda ta kai masa ya d'ago ya kalleta yace "ina singlet da gajeren wando?" Ta kalleshi da sauri tace "Yaya ba akwai wasu a jikinka ba?" Ya girgiza mata kai yace "ki kawo min wasu" haka ta koma duk a sad'ad'e saboda tsoron gamonta da Mama ta d'auko masa ta had'o masa da magani,bayan ta kawo ta fita parlor ya gama shiryawa yana fitowa ta d'aga kanta ta kallesa duk yayi wani iri,bai kalleta ba yace "good night Baby!" Da wani sanyayyan murya kamar wanda dai yake jira ta bashi umarnin kada yaje ko ina,kanta a k'asa tana wasa da fingers d'inta tace "baza ka ci komai bane?" Yace "no i'm ok" da kyar ta iya gyad'a masa kai tace "Allah tsare hanya.." Ya kalleta kad'an kafin ya amsa ya nufi hanyar fita zuciyarsa duk a cunkushe yana jin babu dad'i,bai iya jira ya yiwa kowa sallama ba ya bar gidan,da kyar bayan tafiyarsa ta iya tashi daga gurin ta shiga d'akin,ta tarar da kayansa da ya cire a kan gadon,ta k'arasa ta d'auke ta nad'e su taje ta saka cikin kayanta,tunda ta koma d'akin ta kasa zaune ta kasa tsaye,ta kalli k'ofa ya fi a k'irga,ta tsaya jikin window ta fara kukan da ita ma bata san dalilinsa ba,wani tuk'uk'i taji zuciyarta na mata,tana ta tsaye har bayan kusan minti goma then ta dawo ta haye gadon ta kwanta tayi shiru tana ajiyar zuciya,gaba d'aya ta rasa tunanin da za tayi. Tun daga ranar gaba d'aya gidan suka dena ganin dariyarsa,duk mutum idan yayi aure ana ganinsa cikin farin ciki shi kam sab'anin haka ya kasance,kullum fuskarsa a d'aure babu alamun dariya,ko gidan ya zo ma ba ya wani jimawa yake tafiya,ko daga gurin aikinsa ma idan ya tashi wucewa kawai yake saboda Mama ta kafa masa sharud'anta na babu gaira bare dalili,idan ka ga ya shigo gidan ya jima sai dai idan b'angaren Dadda yaje ta rik'esa da surutu. Cikin haka lokacin JSCE d'in su Manar ya gabato,ranar da suka fara exam sosai yazo musu da sauk'i saboda lesson teacher d'insu kusan duk ya koya musu abubuwan da za su fito exam din,so shi yasa duka lokacin suka mayar da hankalinsu kan karatu ita da Ameerah dan ko wayoyinsu ma Dadda suka bawa ajiya suka ce sai sun gama exam ta basu,a hakan suka gama,bayan fitowar exam suka wuce S.S 1,inda aka kai su science class ita da Ameerah,su Deejah kuma commerce,wata ranar Friday sun taso skul lokacin da yake ana kwad'a rana suna shigowa gidan around 12am sai ga motar Waleed ta shigo a bayansu,driver ya yi parking suka fito ita da Ameerah za su wuce gidan Dadda,Waleed ya fito motar,Manar ta kalleshi idanunsa a kanta ta sunkuyar da kanta a hankali tace "ina wuni?" Ya amsa fuskarsa a d'an sake unlike before,daga d'aya gefen Afiyah ta fito cikin tsadadden lace d'inta sea green ta yafa red d'in mayafi da takalminta mai tsini da jakarta duk kalar mayafinta,kallo d'aya Manar ta mata suna had'a ido ta d'auke kanta tak'i gaisheta,Ameerah ta gaida ta kafin suka wuce abunsu tana k'ara kallon Manar,su Deejah suka tsaya suna ihun murna suna fad'in "ga in-law²" shi kam Waleed tuni yayi cikin gidansu ya barsu tsaye a compound,Afiyah da tsaf ta gane su Manar da suka wuce,ta kalli Deejah tace "wai wancan ma k'annen D ne?" Diyanah tace "wa kike nufi Aunty'n mu?" Afiyah tace "su duka'' Diyanah tace "Ameerah dai step sister mu ce,ita kuma wancan d'ayar cousin d'inmu ce,Daddy'nta ne k'anin Abbanmu" wani damm k'irjin Afiyah ya bada saboda bata manta kallon da Manar ta mata ba kafin ta wuce,tace "dama ba Mamar ku d'aya ba duka?" Deejah ta girgiza kai tace "haba dai su uku fa duka sa'anni ne da Diyanah,ni ce na girme su da 2 yrs" Afiyah tace "really?" Deejah tace "yeah! Da yake ni lokacin da Mama ta haife ni ba ni da lafiya sosai,shisa sai ba'a kaini makaranta ba da wuri sai da za'a sa su,kuma ko lokacin ma Abba cewa yayi a barni har na k'ara samun sauk'i Mama tace a'a,shi ne aka had'a mu duka aka kaimu class d'aya,so bayan mun gama primary kuma shi ne ita sai bata ci gaba ba,grandma d'inmu tasa rigimar sai su Abba sun biya mata kujeran Saudiyya,tana so taje neman kud'i kamar yadda k'awarta ta tafi,shi ne da za ta tafi sai ta tafi da ita,da Mama tana ba mu labari lokacin ta ce ba k'aramin rigima aka yi ba,Dadda ta dage sai ta tafi da ita,k'arshen da kyar su Abba suka hak'ura suka barta ta tafi da ita.." Gyad'a kai Afiyah tayi tace "okay!" Suka wuce tare cikin gidan,a parlor suka tarar da Mama ta sakko tana ganin Afiyah ta tafi hannuwanta a bud'e tana fad'in "oyoyo daughter-in-law" Afiyah ta k'arasa suka rungume juna da Mama,Waleed dake sakkowa lokacin tare da Aunty ya d'auke kansa yace "Mama na je gurin Dadda daga can zan wuce masjeed" Mama tace "alright! Za ka dawo da wuri ne?" Ya girgiza kansa yana kallon agogon wrist d'insa yace "a'a zan lek'a hospital daga can" ta amsa tace "to a dawo lafiya.." Ya amsa yayi hanyar fita without ya kalli direction d'in da Afiyah take yace mata "sai na dawo" a k'arshen throat,saurin tashi Afiyah tayi tana kallon Mama tace "Mama bari na bisa mu gaisa da kaka" Mama ta wani washe baki tace "to sai kun dawo" Waleed da har ya saka k'afarsa waje ya juya ya mata wani kallo yace "da baki yi niyyar zuwa ba sai da zan fita?" Bata kulasa ba ta wucesa ta fita,yayi k'wafa ya juya ya fita,yana kallonta tayi gaba yak'i ce mata komai sai da ya kai apartment d'in mother ya k'arasa balcony ya tsaya,Afiyah da tayi gaba ta waigo ta hangosa balcony d'aya gidan,da mamaki sosai a fuskarta tace "lallaima mutumin nan.." Ta tsaya compound d'in tana kallonsa,sanda yake knocking she thought nan ne apartment d'in grandma d'in nasu ta dawo lokacin shi kam har ya shige,ta murd'a k'ofar ta shiga parlon,a zaune ta tarar da shi suna gaisawa da mother,su Mu'awiyah,Mahmoud,Khaleel,Asad da Mus'ab sai surutu suke suna musun game,mother ta kalli Afiyah dake shigowa tana fad'ad'a fara'ar fuskarta tace "ashe tare kuke?" Yayi d'an murmushi yace "ehh!" Afiyah ta zauna kusa da shi tana kallon mother,ko ba'a fad'a mata ba ta ga kamannin Manar a fuskarta nan ta d'auke kanta tak'i gaisheta,Waleed ya d'ago ya zuba mata ido tsabar takaici ya kasa mata magana,mother tayi murmushi tace "amarya ya gida?" Afiyah dai sai kallon yaran dake gurin take suna gaida Waleed tace "lafiya" duka yaran suka gaisheta ta amsa sai yatsina take ta tashi tana k'arema parlon kallo tace "D na yi gaba ni,ka san ba na son hayaniya" mother ta bita da kallo tana jinjina k'arfin halinta,ta daure dai tace "to amarya ku gaida gida ko ruwa ma baku sha ba?" Afiyah da har ta je k'ofa tace "to zai ji" ta fita,Waleed ya rasa me zaice ma mother,jikinsa a sanyaye ya mik'e yace "mother bari na k'arasa gurin Hjy" tace "to shi kenan Waleed,na gode da ziyara" yayi murmushi yace "haba mother what a compliment here?" Tace "a'a ni da ka kawo min amarya,ai na yi godiya though bata tsaya ba" Waleed yace "bari dai naje zanje masjeed" tace "to sai ka dawo" ya kalli yaran yace "Asad ain't u go to masjeed? Kun zauna gida kuna game ko?" Asad ya juya yace "za muje Yaya!" Yace "sai yause?" Asad yace "yanzu za mu shirya" Waleed yace "ina ga imam d'in zai jira ku ko?" Dariya yayi yace "a'a Yaya" Waleed dake tsaye yace "to ya ya