← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 184

Sashe 97

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

wahale suke dawowa gida,duk ranar da suke da paper kuwa da kyar suke tsinana wani abun,yayin da har lokacin babu labarin Waleed bare asa ran zai dawo,sanda Mama ta masa waya take tambayarsa yaushe zai dawo cewa yayi ba yanzu ba,babu yanda bata yi da shi ba amma fir ya nuna shi fa bai jin zai dawo ma sai an gama azumi kaf,dole ta hak'ura ta kyalesa,ranar ana sallah saura kwana uku aka kawo lefen Manar,fad'an irin kayan da aka zuba mata kamar b'ata baki ne,tunda Mama ta samu labarin shigowar y'an kawo lefe though maza suka kawo ta kasa zaune waje d'aya ta dunga safa da marwa daga d'aki zuwa parlor,haka ko su Deejah ma taita sawa su gano mata idan yan kawo kayan sun tafi,can dai ta gaji ta kira Hjy Izatu duk ta sanar mata abunda ake ciki,Hjy Izzatu tace "toh meye abun d'aga hankali kuma Allah na tuba,ke da aka gama baki tabbataci akan yarinyar nan sai ta yi auren nan babu fashi,kin san fa abune da ba zai tab'a yiwuwa ace an fasa ba,to meye abun damuwa kamar baki yarda da bawan Allan nan ba.. Tunda yace ki jira ayi auren akwai yanda zai yi ya raba,ki bari dai har yayi abunda zai iya muga,idan babu nasara ne sai mu nemi wani ko kuwa?" Hankalin Mama a tashe tace "na sani Hjy ba wai ban yarda bane,ni kawai burina bai wuce naga yarinyar da uwarta sun ji kunya ba,kuma dai kin san yanda muka yi da Waleed akan yarinyar ko ba haka ba? Ga shi ma ya yi tafiyarsa ya zauna wata k'asa duk akan maganar auren yarinyar ya gujewa zama a nan,ni dai idan da taimakon da za'ayi ina son ayi ya dawo ayi bikin a kan idanunsa dan ya tabbatar bazai samu yarinyar ba.. Banda ma abu ai wallahi ko shi yaron dake nemantan ban so aka ce lallai saii ya aureta ba,so nayi ace lalata ta yayi ko wani jigataccen almajiri ya fito zai aure shegiyar yarinyar.." Dariya Hjy Izzatu ta fara tace "kai k'awata ba ki da dama wallahi" Mama dai ta yi kicin²,Hjy Izzatu tace "babu damuwa za mu san yanda muka yi da Waleed ya dawo" Mama tace "yawwa dan Allah ayi duk yadda za'ayi asa shi ya dawo gida" Hjy Izzatu tace "an gama fa kada kiji komai,kamar ya dawo ma an gama" lokacin suna cikin maganar kamar ance ta d'aga kanta taga Azaan da Amaar suna shigowa,yanayin kallon da suke mata yasa ta sha jinin jikinta da sauri ta yiwa Hjy Izzatu sallama ta katse wayar,fuskarta a d'aure tana aika musu mugun kallo,su dai suka wuce sama babu wanda yace mata k'ala,jin an sake bud'e k'ofa da sauri ta d'aga kai she thought su Deejah da ta aika su mata investigation ne,Aunty ta shigo da farin ciki sosai tace "Hjy an kawo kayan Manar,kaya na gani a fad'a wallahi son kowa k'in wanda bai samu ba,akwatuna sha biyu..." Mama ta d'auke kai tana tab'e baki da kyar ta iya cewa "toh Allah dai yasa ba yaudara bane,wannan kayan kamar za'a siyar da yarinya.." Juyawa Aunty tayi ta nufi sama tana cewa "ai da yake itama iyayenta ba fatararru bane,in dai arziki ne gadonsa tayi,dan an kawo mata kaya irin wannan ba komai bane da arzikinta ta zo" tai wucewarta sama ta bar Mama da sakakken baki,y'an kawo kaya suna barin gidan aka kwashi kayan aka kai part d'in Dadda,Dadda ta saki baki tana kallon maids da suke shigo da kayan tace "wannan kuma fa daga ina? Meye wannan d'in a ciki?" Ruqayya na murmushi tace "kayan takwararki ne" Dadda ta mik'e da sauri tace "wa ya kawo?" Ruqayya tace "iyayen wanda ke sonta ne suka kawo,Alh yace a shigo da su nan" Dadda ta saki wani kabbara sai kuma ta fara gud'a tana rawa,can dai ta dakata tace "yaushe suka zo?" Ruqayya tace "basu jima da tafiya ba" zaunawa Dadda tayi ta fashe da kuka tace "Allah sarki takwarata,shi kenan haka za ta tafi ta barni ni ni kad'ai raina.." Shigowar su Dadday tare da Abba yasa tayi shiru tana share hawayen idonta,suka zauna suna gaisheta,ta amsa cikin rawar murya tace "kuma har lokacin aurar da Manar d'in ya yi ne?" Daddy dai bai bata amsa ba sai kallonta yake,Abba ne ya mata bayanin komai da lokacin da aka tsayar sallah da sati biyu,Dadda ta sake rangad'a gud'a tace "Alhamdulillah! Takwarata ta yi goshi,Allah na gode maka,Allah ka ara min rai da lafiyar ganin y'ay'anta,na rainesu kamar yadda na raineta in sa masu albarka" sai kuma ta fashe da kuka,Ameerah da ta shigo ganin kayan tana ganin Dadda na kuka ta fashe ba dariya,su Daddy dai suna gama magana suka fita,Dadda ta kalli Ameerah tace "maza janyo su mu gani y'ar nan" suka dunga d'aga kayan suna kallo...
Chapter 97 · 0% Book details