← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 184

Sashe 30

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

tsaya kallon ruwa kuma kwad'o zai iya yi miki k'afa ba" Rabi tace "wane irin kwad'o ne wannan? Ai wallahi duk abunda zai shiga tsakanina da shi zan iya kawar da shi daga duniyar" wani dariya Asama'u tayi tace "anzo gurin!" A nan ta fara kyankyasa mata batun su Maryam da yanda za tayi har dai ta janyo ra'ayinsa kanta.. Alhamdulillah an gama biki lafiya amarya ta tare a katafaren gidanta da Raj Maqbool yasa aka gina musu cikin wata guda saboda makarantarta za su fara zama a nan idan sunyi hutu kuma su wuce India har zuwa lokacin da za ta kammala karatunta,bayan y'an rakiyar amarya sun tafi gida ya rage amarya da k'awayenta su Fatima,suka yi mata sallama za su koma gida sai washe gari su tafi gidajensu,Hafsah tana kuka suma suna yi ga shi sun rungume juna da kyar Muh'd ya rik'o hannun Maryam yayi waje da ita,ya sata motarsa ya shiga ya fara bata baki yana cewa "ai ba shi kenan kun rabu ba,za kuzo ku ganta itama za taje inda kuke,mene abun kuka kuma?" Sanda ya samu tayi shiru ya wuce da su gida shi ya rakasu har b'angaren Mama azumi,washe gari ko da za su tafi bayan sun yi sallama da Mama ta had'a su da kayan gara da abun arziki tayi musu addu'ar suma Allah kawo musu mazajen suma,suka fita suna k'walla saboda cikin y'an kwanaki suka yi saboda kowa na gidan banda Asama'u,bayan fitarsu Muh'd ya fara kaisu gidan Hafsah a can suka wuni daga can ya mayar da su gidajensu bayan ya musu siyayyar arziki da yake Maryam da Fatima unguwarsu d'aya line su ne dai ba d'aya ba,da zai tafi ya karb'i digit d'in Maryam suka yi sallama. Tun daga ranar yake kiranta suke gaisawa a haka mutunci ya shiga tsakaninsu,a hankali² alak'arsun ya fara rikid'ewa ya koma wata irin shak'uwa mai k'arfin gaske,haka kawai idan yana gari ma sai yace zai zo su gaisa,a zuwan da yake gurinta ya cusa mata ra'ayinsa,ba tare da jinkiri ba lokacin da yake sanar masa yana sobta itama ta karb'a,ko da ya kaiwa Mama azumi maganar ya samu matar aure tace "a ina take?" Kai tsaye ya sanar mata k'awar Hafsah ce k'anwarsu,Mama ta yi farin ciki sosai tayi addu'ar fatan alkhairi tace za ta fad'awa Malam,ko da Malam ya dawo ta sanar masa ya kira Ibrahim ya fad'a masa maganar,Abba yana sosa backhead yace "Baba nima ai fad'a muku ne banyi ba ya riga ni,amma nima ina da burin k'ara aure,harka na samu mata" Mama tace "da wuri haka Yaro?" Malam dai yace "maa sha Allah,a ina ita kuma take?" Yayi k'asa da kansa yace "ai itama k'awar Hafsah ce" Mama tace "ko dai Fatima kake nufi?" Cikin jin kunya yace "Ehh! Itace" Mama tace "ikon Allah! Ashe ni duk surukaina ne suka zo min har gida ban sani ba,ai kam na yi farin ciki wallahi,idan wannan abu ya tabbata Hafsah ita za ta fi kowa murna yayyenta sun aure k'awayenta.."
Chapter 30 · 0% Book details