Sashe 46
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
ya kalleta yace "me fa?" Tace "dariyan da kake,dan baka ga yadda ya maka kyau ba" yayi murmushi yace "kina so nayi?" Ta gyad'a masa kai da sauri tace "sosai ma" yace "sai dai ki siya" zaro idanu tayi tace "ni to ina naga kud'in siya?" Yace "ba ki da su?" Ta gyada masa kai,yace "eyyahh! Shi kenan baki da rabon gani" sosai tayi fuskar kuka yayi murmushi yace "ko dai na ranta miki,idan Hjy ta dawo sai ki karb'a ki biyani?" Da sauri tace "eh! Zan karb'ar maka a gurinta" yace "no! Ban yarda ba,kada kiyi min irin nata kice kinci dubu sai ceto" dariya ta fashe masa da shi yace "ohh! Na fad'a dai² ko?" Ta girgiza masa kai tana tsayar da dariyarta tace "aaaaa.. Ni fa ba haka nake nufi ba" yace "ya ya kike nufi?" Tace "babu komai" yace "ban yarda ba" tace "da gaske zan karb'ar maka idan ta dawo" yace "um'um! Sai dai ki yimin labari mai dad'i" da sauri tace "shi kenan ba sai na biya ba?" Ya harareta yace "inji wa yace haka?" Tace "to ai idan nayi maka labari ka ga ba sai na biya ba" yace "a'a za ki biya" da sauri tace "tabbb' d'i ai sai dai idan kaima za ka biya ni shi kenan kaga na samu kud'in da zan biya ka" yace "da gaske?" Tace "ehh!" Yace "ke fa k'anwata ce,sai na biya za ki ba ni labari?" Tace "to ba kaima ka ce sai na biyaka ba?" Yace "shi kenan na yafe ba sai kin biya ba" da sauri itama tace "nima na yafe to" hira sosai suka dunga yi tana bashi labari,wani yayi murmushi wani kuma idan yaga ta yi wauta yayi dariya,sosai ranar ya ba-ta mamaki,ta dunga tuna lokacin baya da suke kamar haka,daga bayan tafiyarsu Saudiyya zuwa yanzun ne kad'ai aka samu canji,sai ga shi yau ya sake dawo mata kamar asalin Yayanta da ba ya kyararta,a hakan Dadda ta dawo ta samesu sai surutu suke,tayi tsaye bakin k'ofa tana kallonsu sanda mamaki ya isheta ta k'arasa shiga tana rik'e chin d'inta tace "me zan gani kuma yau ni jikar laraba?" Dukansu suka juya suka kalleta,Waleed ya d'auke kansa yace "sannu da zuwa" Manar ma tayi mata sannu da dawowa,babu wanda ta amsawa ta k'arasa shiga ta ajiye mayafinta saman kujera ta wuce d'aki tana fad'in "ai shi kenan,ni dai ban san lokacin da kuka shirya da mutumin ba" Manar ta bita da kallo bata kulata ba,tana shigewa tayi saurin rik'o hannunsa a hankali ta rad'a masa tace "Yaya tashi mu tafi" ya kalleta da sauri yace "ina za muje?" Tace "ni wallahi mitarta ne ba na so,ita kuma yanzu sai taita ma mutane fad'a ko basu yi komai ba" murmushi yayi yace "ke da Hjyn kuma zan ji kanku?" Tayi kicin² tace "ni dai idan baza kaje ba zan tafiyata" tashi yayi yace "ina kike so muje wai?" Tace "yawo" zaro idanunsa yayi yace "yawo zuwa ina?" Tace "ko ina ma,muje da sauri ni dai kafin ta fito" jin alamunta tahowarta ta turasa suka yi waje da sauri,suka tsaya balcony ya kalleta yace "Umhn! Ina jinki" tace "ina mukullinka?" Ya watsa mata hannuwansa yace "suna d'akin Mama namanta su" zaro idanu tayi tace "ya akayi ka barsu a can?" Yace "ohoo! Ko zaki ki d'auko mana?" Ta wani zaro idanu a tsorace tace "tabb' d'i wallahi bazan iya ba" yace "saboda me?" Tace "ina jin tsoro" yace "tsoron wa?" Tace "Mama mana" shiru yayi yana kallonta kafin yace "shi kenan sai dai mu hak'ura da fitan" da sauri tace "to Yaya kai kaje ka d'auko mana" ya zaro idanunsa yace "tsoro nake ji nima" tace "tsoron wa?" Yace "Mama" ta kallesa tace "to kai ba Mamar ka bace me yasa kake tsoronta?" Yace "munyi fad'a d'azu" dariya ta fara masa tace "kai Yaya da Mamar ta ka kuka yi fad'a?" Ya kalleta yace "ke ba Mamarki bace?" Ta tab'e baki tace "ni ba Mamata bace ita,mother da Aunty ne mamomina" wani kallo ya dunga yi mata yace "saboda me ita bata zama Mamanki ba?" Tace "to ba ita kullum sai dai tai ta min fad'a ba,kuma ko gaisheta nayi ba ta amsawa,shi yasa nima na daina gaisheta,kuma su Deejah ma ba sa gaida Mother da Dadda shi yasa ni kuma na fad'awa Dadda tace nima na daina gaisheta ai uwa bata fi uwa ba" still yayi yana kallonta kafin ya matso kusa da ita yace "me yasa kike k'in gaisheta?" Tace "to ba su Diyanah suma ba sa gaisar da Mamata ba" yace "amma ni ai ina yi" tace "to ai na ka daban suma nasu daban" a hankali ya rik'e hannunta yana kallon cikin idanunta yace "daga yau za kina gaisheta?" Tayi saurin kallonsa,ya d'aga mata kai yace "yessss! Suma zan samesu,za suna zuwa suna gaida mother" tace "to Hjy fa?" Yace "itama haka" ta tab'e baki tace "tabb'! Baza su zo ba fa" yace "saboda me?" Tace "har Abba fa sai da yace musu amma basa zuwa" yace "yeah! Ni zansa suyi" ta karkace kai tace "tabb' d'i ni dai gaskiya bazan yi ba" ya d'aure fuskarsa yace "ko saboda ni baza kiyi ba?" Ta girgiza masa kai tace "a'a zanyi saboda kai" yayi murmushi yace "thank u" daga haka suka koma parlon suka sake zaunawa suka ci gaba da hira,dukkan b'acin ransa lokaci d'aya ya nemesa ya rasa,tsaf ta goge masa komai daga ransa. Yana barin d'akin cikin tsananin tashin hankali Mama ta fizgo wayarta ta fara dannama Hjy Izzatu kira,bugu d'aya ta d'auka da fad'in "y'ar halak kink'i ambato.. Kin ganni gidan Sahiba" duk da tashin hankalin da take ciki bata fasa tambayarta ba tace "Hjy Baraka?" Hjy Izzatu tace "ehhh! Wallahi yanzun ma maganarki muke tace kwana biyu ai baku had'u ba" ajiyar zuciya Mama tayi tace "wallahi ki bari kawai ina cikin tashin hankali ne" Hjy Izzatu tace "tashin hankali akan me,me yake faruwa kuma?" Mama cikin dauriya tace "maganar ya fi k'arfin muyi shi a waya,ke dai kawai ki samu ki zo ko ni na zo" ajiyar zuciya Hjy Izzatu tayi tace "shi kenan idan na bar gidan Sahiba zan b'illo" Mama tace "da kin taimake ni wallahi,dan yau duka ba na cikin nutsuwa ta" Hjy Izzatu tace "shi kenan sai na shigo d'in,dama akwai maganar da nake son muyi dake ma,kuma sai kika katse min hanzari da wannan maganar,but babu matsala duka idan na zo sai mu tattauna" Mama ta amsa suka yi sallama,tana sauke wayar daga kunnenta ta rushe da kuka tana fad'in "Allah ya isa tsakanina dake Maryam da dukkan zuri'ar ki,in Allah ya yarda bazan tab'a ganin wannan bak'in cikin ba" ana cikin haka Hjy Izzatu ta k'araso gidan,tunda ta shigo suka k'ule cikin d'aki Mama take ba-ta labarin duk abubuwan da suka faru,Hjy Izzatu ta rik'e baki tana jinjina maganar tace "dank'ari! Yanzu shi Waleed d'in ne ya iya kallonki ya fad'a miki wannan maganar?" Mama cikin kuka tace "wallahi Hjy ni kaina sai da naji mamaki" Hjy Izzatu ta girgiza kai tace "a'a wannan dai wallahi kema daga ji akwai makirci ciki,Waleed da ko mai kika ce masa obeying yake bai tab'a miki gardama ba,shi ne har kuna musayar yawu da shi?" Mama tace "ki gane min hanya dai,ni kaina na kasa believing" Hjy Izzatu tace "wallahi da sake.. Wai an bawa mai kaza kai,kin san Allah ba yin kansa bane,dole akwai wata a k'asa" da sauri Mama tace "ko?" Hjy Izzatu cikin tabbatar mata da zancenta tace "ahaafff! Ke dai ki bari kawai amma sha Allahu muka je gurin malam d'an juma abunda zai tabbatar mana kenan" Mama cikin tashin hankali tace "to yanzu ya kike ganin za ayi?" Hjy Izzatu tace "ai yadda za'ayi ki shirya kawai gobe muje" Mama tace "amma ba kya ganin gobe ya yi wuri na sake requesting fita gurin Alh?" Hjy Izzatu tace "a'a wane irin wuri kuma? Ai da zafi² ake bugun k'arfe,ko kuwa dai kin fi so muyi sanya muna ji muna gani a sabautamu?" Mama ta girgiza kai tace "ina fa zan so haka ya faru da raina" Hjy Izzatu tace "atoohh! Idan ba haka kike so ayi ba kuwa ai ya zana dole mu fita goben" da sauri Mama ta jinjina kai tace "an gama ai ko Alh bai yarda bama zan saci hanya na zo" Hjy Izzatu tayi dariya tace "yawwa y'ar gari.. Ni kuwa kin ma katse min hanzari fa!" Mama tace "hanzarin me kuma?" Hjy Izzatu tace "maganar auren da boka yace ki yiwa Waleed nake son tuna miki" wani ajiyar zuciya Mama tayi tace "ki bari kawai sai na nutsu zan waiwayo kan wannan batun" Hjy Izzatu tace "a'ahh! Nima ba nufina kenan ba,na dai gano miki suruka ne a gidan da ya dace" kallonta Mama ta dunga yi bata gane me take nufi ba,tace "fahimtar da ni" Hjy Izzatu tace "y'ar Sahiba na gano yau,kin san ta gama karatun ta dawo k'asar,ni dai wallahi na yi masa sha'awarta,baki ga yanda ta sake yi ba,yarinya jajir da ita kamar tsada,abun dai sai kin gani.."