← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 184

Sashe 134

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fa Dadda tace ai sai su tafi su barta ta kwana da ita tunda dai bata farko ba har lokacin bare su san a want hali take,Abba yace "Hjy ai su nan hospital d'in masu jinya basa kwanar musu sai dai ka wuni ka tafi da safe ka sake dawowa" Dadda ta dage ita wallahi sai a tafi a barta ko ba'a kwana ita dai yau sai ta kwana gurin jikarta har da kukanta,da kyar dai Aunty da Amaar suka lallab'ata ta yarda za ta tafi bayan ta gama mitar wannan dai ba tsari bane ace za'a bar mutumin da yake jinya shi kad'ai kamar ya rasa dangi,Waleed yace zai zauna tare da ita babu matsala suje sai da safen,haka suka fito suka wuce a motar ma sai mita take har dai suka k'arasa gida. A b'angaren Mama kuwa sanda Waleed ya bar gidan hannu biyu ta d'ora a ka kukan ma ta rasa ta inda zai zo mata saboda tsananin tashin hankali da rud'anin data tsinci kanta a ciki,abu na farko dake sawa zuciyarta rauni shi ne furucin Waleed,na biyu kuma dai ta san duk bala'i tunda Waleed ya ganta red-handed dole ma ko ya rufa mata asiri idan Manar ta farfad'o ta tona,tou wai ita yanzu ta ma fara bin hanyar gidan? Idan taje tace musu me? Ta kalli Afiyah dake kuka wiwi tana sak'e² a zuciyarta dan dole ma ya zamar mata ta koma gidan ta san matsayin aurenta duk da dai ta san zai wahala Abba bai rabu da ita ba a lokacin,bata iya cewa Afiyah komai ba ta zare jikinta ta lallab'a ta bar gidan ko noticing Afiyah bata yi ba,sai da ta gama koke²n ta d'ago da niyyar mata magana taga wayam,duk inda take tsammanin ganinta sanda ta duba bata ganta ba ta gyad'a kai ta kirata a waya,Mama tana ganin kiran lokacin ta gama waya da wani cikin malamanta yace kada ta damu zai mata aiki ya rufe bakin su ko tambayarsu akayi baza su fad'i gaskiya ba,ta masa godiya kafin ta hau napep ko ta kan kiran driver bata bi ba ta nufo gidan da kwarin guiwarta,sanda taga kiran Afiyah kasa d'auka tayi saboda bata san me za tace mata ba tunda dai ita shaida ce akan Waleed ya saketa saki uku,ba ta da damar sake tursasa sa sai ya mayar da ita gidansa kuma,ko ba ma wannan ba ita kanta ta kanta take yi da igiyar aurenta biyu da suka yi saura a yanzun,saboda haka sanda wayar ya katse ta turama Afiyah sak'on ban hak'uri sai kuma kalmar ta na k'arshe wanda ya masifar k'onawa Afiyan rai shi ne da Mama tace "kowa yayi ta kansa" Afiyah ta share hawaye tana k'ara jinjina kalmar kowa yayi ta kansa a ranta,tace "za ki san ni kika cewa kowa yayi ta kansa" ta wuce bedroom d'inta fuskarta ya yi jaa ya kumbura ta d'auka mayafinta ta had'a kayanta cikin trolley ta fita daga gidan tana waiwayensa tana sake share fuskarta. Around 2:00am Manar ta farka da matsanancin ciwon ciki,kukan da take k'asa² tana rik'e cikinta ya dawo da Waleed daga duniyar tunanin da ya tafi,da sauri ya matsa kusa da ita ya kamo hannunta yana mata sannu,yana kallonta yake tambayarta ina yake mata ciwo,ta kasa magana sai nuna masa cikinta take,da kyar ya lallab'ata ta kwanta ya matsa inda ya ajiye magungunanta da ya siyo a pharmacy d'azun sanda ya fita,ya had'a mata tea sai dai bai cika sugar ba a ciki ya bata,shi kad'ai ta iya sha kafin ya had'a allurai ya mata ya zauna gefenta ya rungumeta yana shafa bayanta yana hura mata iska a kunne,tun tana kukan kad'an² sanda ciwon ya fara mata sauk'i tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya,wani wahalallen bacci ya sake d'aukarta,kusan a haka suka zauna sai da aka fara kiran assalat kafin ya gyara mata kwanciya ya fita ya nufi masallaci,after ya fito guraren 6am ya dawo d'akin ya zauna yana gadinta,idanunsa tar a kanta yanda yaga rana haka darenma ya gansa,sai guraren 7am ta sake farkawa,but wannan karon alhamdulillah jikin da sauk'i sosai sai d'an abunda baza'a rasa ba,ya tambayeta or did she feels pain anywhere kuma? Tace a'a ba ta ji,yace idan ta ji canji ko ya ya ne ta sanar masa ta amsa shi,shi ya mata wanka saboda yanda jikinta yake ba wani kwari ya shiryata,da yake tun a jiyan ya taho mata da kayanta daga can ya biya gida ya karb'an musu abinci gurin Mother,sanda ya kwantar da ita kan gado yace "ki huta kafin su Hjy su k'araso" zai bar kusa da ita ta rik'o hannunsa tana kallonsa da pale idanunta tace "Yaya ina za kaje kai?" Ya d'an girgiza mata kai da wani cool voice yace "i'm not going anywhere Lilac,ina tare dake" d'an gyad'a masa kai tayi ta matsa masa kusa da ita tace "tou kazo mu kwanta tare,kaima ai baka huta ba" da sauri yace "no kiyi baccin ki,ba na son takura miki" b'ata rai tayi tana kallonsa hawaye cike a idonta tace "ni dai sai ka zo mun kwanta a nan" yaga rigima take nema dole ya rab'a ya kwanta kan gadon though ya musu kad'an ta wani shige jikinsa tana sauke ajiyar zuciya suka yi shiru,can da aka jima he thought ko ta yi bacci,sai ji yayi ta kira sunansa da muryar kuka,ya lumshe idanuwansa a hankali yana jin damuwa duk ta masa yawa,bai iya amsawa ba sai da yaji tana shafo fuskarsa tace "Yaya!" Ya daure duk da hawayen da suke neman zubo masa yace "uhn!" Bud'ar bakinta tace "Yaya mun yi asaran baby'nmu kou?" Kasa magana yayi saboda zuciyarsa yayi mugun karyewa,idan yace zai yi magana kuma kuka zai iya kwace masa a ko wane irin lokaci,but the way ya sake k'ank'ameta a cikin jikinsa har tsoro ya bata,nan da nan ta fashe masa da kuka sosai,da sauri ya d'ago fuskarta yace "shhhhiiii! Don't cry" ta kasa yin shiru sai sheshshek'ar kuka take,ya kai hannu yana goge mata fuska yace "i said ya isa,kou kina so ki sani kuka ne ehh?" Ta girgiza masa kai da sauri,yace "it's okay tou,ki bar kukan haka,okay?" Ta gyad'a masa kai,ya d'an zubawa lips d'inta da suka yi wani pinkish kaman na jarirai idanuwansa,so yake yayi kissing d'insu but yana gudun abunda zai iya faruwa,yana can duniyar tunani sai jin saukar warmth lips d'inta yayi akan nasa tana tsotsa,yayi saurin kallonta yana k'ok'arin raba bakinsa da nata,da kyar ya iya b'amb'areta yana kallonta yace "me kike yi haka? Baki san ba ki da lafiya ba?" Ta fashe da kuka sosai tace "tou ba kaima kana so ba?" Ya zaro idanuwansa yace "kika ji na fad'a miki haka?" Tace "ai tou ba sai ka fad'a zan sani ba" ya d'an lumshe idanuwansa a hankali yace "kiyi bacci nace,ina jiran Hjy suzo naje gida na dawo" kallonsa ta dunga yi kafin ma tayi magana aka yi knocking k'ofar,suka kalli k'ofar a tare kafin ya fara k'ok'arin sauka daga gadon ya kwantar da ita saboda tun da ya dawo ya kulle,ya k'arasa ya bud'e,da Dadda ya fara yin ido biyu fuskarta a tamke tana mitan tun asuba ya kamata ace an kawota taga jikin Manar d'in amma dan walak'anci ba'a tashi kawota ba,sai da rana ta gama zagaye duniya,ya matsa ya bata hanya yana mata sannu da zuwa,ta amsa ta wuce ciki,ganin Manar d'in ma idanunta a bud'e Dadda ta wani washe baki tace "kaiii! Barka da nazo dai yau na ga idanuwanki biyu ba kamar jiya ba har muka tafi kina kwance kamar gawa" ta k'arasa gaban gadon tana d'an murmushi,Aunty ta shigo d'auke da basket da ledoji a hannunta,Waleed yayi saurin karb'an kayan idanuwansa akan Manar ya ajiye,suka gaisa da Dadda then Aunty,suka masa ya mai jiki ya amsa,sun jima da shigowa kafin yace zai je gida ya dawo,suka masa Allah tsare,ya d'an kalli Manar a hankali yace "bari naje na dawo" ta d'an langab'ar da kai,yace "me zan kawo miki?" Instead of ta masa magana sai ta girgiza masa kai kafin tace "babu komai" ya musu sallama ya fita. Ak'alla sai da Manar ta samu kwanaki biyar a hospital d'in,lokacin su Ameerah har sun zo sun koma,Mommella kawai suka bari,kullum da ita ake wuni a hospital d'in,since that day da incidence d'in ya faru Waleed ya rok'i Dadda akan duk hukuncin da za'a yanke suyi hak'uri har ranar da za'a sallami Manar d'in,da farko Dadda bata fahimcesa ba tace saboda uwarsa ce shi yasa zai ce a bari ba yanzu ba? Sanda ya mata bayani sosai yace shi fa ba yana nufin kada a hukunta Mama bane,jikin Manar d'in yake so yayi sauk'i sosai idan suka daso gida duk za sufi samun nutsuwar fuskarta case d'in yanda ya kamata. Ranan Sunday da yamma suka dawo gidan,motocinsu suna yin parking Mama ta lek'o ta window tana kallonsu saboda har ranar babu wanda ya tayar mata maganar,a tunaninta ma aikin bokanta ne yaci su shisa taji shiru babu wanda yace mata k'ala,tana tsaye tana kallonsu tana tab'e baki suka wuce part d'in Dadda,tana hango sanda Deejah ta fita taje part d'in,sanda take dawowa ta shigo d'akin ta samu Mama tsaye wajen window har lokacin ta kasa zama,ta shigo tace "Mama! Ya kamata ki shiga kiga jikin Manar,ance ta samu miscarriage ki mata jaje" wani uban kallo Mama ta juya ta maka mata tace "to uwar iya,bazan je ba,idan sai na je za ta samu sauk'i daga can ta mutu" Deejah ta dunga kallon Mama ta kasa magana tsabar mamaki,sanda Mama ta mata wani tsawa tace "c'mon get out please idan kin gama kinibibin" jiki a sanyaye Deejah ta fita tana waigen Mama,ita dai duk ta rasa wannan dalilin k'iyayyan na Mama akan Manar,shisa fa ita tun sanda Mama tayi rashin lafiyar nan ta dunga surutai jikinta duk yayi sanyi tun daga nan ta sakko ta daina ma Manar d'in mugun tsanar da Mama ta cusa musu a kanta,lokacin da Deejah take fita ya yi dai² da shigowar Aunty,ta gaisheta kafin ta wuce,Aunty ta tsaya daga door way tana kallon Mama tace "Alh yana son ganinki a can b'angaren Hjy yanzu" sanda Aunty take fad'ar sak'on Abba though cikin Mama yayi mugun juyawa but da yake she's wicked haka ta daure
Chapter 134 · 0% Book details