Sashe 10
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari Friday gaba d'aya yaran gidan basa nan sun tafi skul sai Manar kad'ai dake kwance a parlor kan kujera,sanye take da wani sleeveless mai net ta wajen boobs d'inta red colour,rigan ya zauna a jikinta sosai sai short d'in wando da iyakar tsayinsa k'asan buttock d'inta kanta ko d'ankwali babu ta kafe TV da kallo,a nutse ya tura k'ofar ya shiga sanye cikin k'ananun kaya black trouser da polo t-shirt yellow,a ciki² yayi sallama ganinta ita kad'ai ya k'arasa yana d'aure fuskarsa,ta d'ago ta amsa tana sakin masa murmushi tace "Yaya! Sabahal khair" had'e rai yayi bai amsa ba yana jifanta da wani dirty look yace "wane irin iskanci ne wannan?" Kallonsa ta dunga yi bata gane me yake nufi ba ta dai zuba masa idanunta,wani tsawa ya mata yace "ba dake nake ba kike kallona?" Zumb'uro masa baki tayi cike da shagwab'a tace "to ni me nayi kuma?" Ya fara takowa inda take yace "ni kike tambaya?" K'unk'uni ta fara masa "to ai ban san me nayi ba,daga zuwanka ka fara min fad'a" hannu ya kai zai kamota tayi saurin gocewa,bisa tsautsayi ta fad'o daga kan kujeran ta buge k'afarta,uban azabar da ya ratsa kwakwalwarta yasa ta fasa wani gigitaccen k'aran da yayi calling attention Dadda dake cikin d'aki tana gyaran kaya,ganinta kawai suka yi ta fito kamar an cillota a rikice ta k'arasa ta d'agota tana tambayarta "me ya faru?" Wani kallo Waleed ya dunga mata yana jira yaji me za tace,cikin kuka bata yarda ta kalleshi ba tace "to ba Yaya bane" da sauri Dadda ta katseta tace "me ya had'a ki da shi?" Tace "ni ban masa komai ba kawai zuwa yayi zai doke ni" tsuke fuska Dadda tayi ta kalli Waleed dake tsaye yana kallonsu cike da takaici tace "dan Allah Mamman zo ka fita kafin raina ya gama b'aci" yace "na je ina?" A fusace tace "duk ma inda za ka kaje mana,ko da ni kake tambaya idan za ka fita?" Tab'e baki yayi ya wuce zai zauna,tayi maza ta sha gabansa da sauri ta fara kakkare kujerunta,cikin masifa tace "idan ba sai ka fita ba kafura uwata ta haife ni,ni dai da girmanka ba za ka zo kana sani magana ba,ko yara basa zuwa su sani magana kamar haka,sai kai gaskiya bazai yiwu ba,maza ga hanya can fita ka ba-ni guri,ko yanzu nasa a kira min Yaro" had'e rai yayi yace "matsa na wuce" a fusace tace "ka wuce kaje ina?" Yace "ki matsa na wuce nace,babu inda zanje sai na gama uzurin da ya kawo ni" wani kallo ta dunga masa tace "idan na k'i na matsa fa?" Yace "zan janyeki na wuce" mitsi² tayi da ido ta kama waistband d'inta ta rik'e tace "to janye nin muga" bata gama rufe bakinta ba ya kama hannayenta duka kamar wata y'ar tsakuwa ya matsar da ita gefe ya nemi saman kujera ya zauna yana had'e rai,wani kallo ta dunga masa tana tsaye inda ya matsar da ita ta kasa magana,bai kalli inda Manar take ba fuskarsa babu fara'a yace "ke! Je ki had'a min breakfast" zare idanu ta fara yi da sauri ta kalli Dadda tana jira taji me za tace,Dadda tayi mitsi² da idanu a fusace tace "a ina za'a maka girkin?" Yace "a nan" wani kallo ta aika masa tace "ka kawo min kayan abinci dama da idan kaji yunwa za ka kwaso k'afafunka kazo a dafa maka?" Bai kalli inda take ba yace "sai na kawo za'a dafa min,think Abba yake siya ko?" Cikin fad'a tace "da Yaron ya siya ya aiko min yace ni da kai ya siyawa ne? Naga dai bai ce saboda kai ya aiko ba da za ka kwaso jiki kazo min,kuma dai tunda ka san baka tab'a kawo min ko k'wallin shinkafar ka ba,maza ka tattara tsumman rayuwarka ka tafi gurin uwarka da kake kaima albashinka kaci a can" wani kallo ya d'ago ya dunga mata fuskarsa a d'aure,for about 3 minutes ya kasa cewa komai,sai kuma ya mik'e da sauri ya nufi k'ofa,ta rakasa da mugun harara tace "Allah raka taki gona" yana jinta ya k'i tankata ya fita dan taji haushi sai ya bar mata k'ofar a bud'e ya san ta tsani a fita ak'i rufe mata k'ofa,ta saki baki cikin takaici tayi k'wafa tace "ke! Je ki rufe mana k'ofa maza kada k'ura ya cika mana gida" tashi Manar tayi ta nufi k'ofa ta rufe ta dawo ta kwanta ta ci gaba da kallonta. Around 12pm ta fito part d'in za ta je gurin Aunty,a hankali take tafiya kamar mai counting steps d'inta,har ta kusa k'ofar part d'in ta jiyo muryar Ameerah tana kwalo mata kira,tsayawa tayi a balcony tana kallon su har suka gama fitowa daga motan,Ameerah ce da wasu y'an mata biyu da baza su wuce sa'anninsu ba,suna mugun kama da Waleed kana kallonsu za kasan they're from one mother,har suka k'araso inda take Ameerah ta fara mik'a mata hannu tana sakin murmushi suka yi musabaha,Manar tace "har kun dawo?" Ameerah tayi murmushi tace "kai sis mun dad'e fa a skul d'in tun 7am muka fita,na san time d'in ma ko juyin farko baki yi ba" murmushi Manar tayi kafin tayi magana d'aya daga cikin y'an matan da suka zo tare da Ameerah ta tab'e baki tana musu wani kallo tace "ya ma za'ayi ta sani tunda babu fuss!" D'ayar dake gefe tayi saurin karb'an zancen "dama tunda an fi ganewa a tafi wani duniyar karuwanci a b'ige da karb'ar sabil ai baza'a san komai ba,haka za azo a koma cikin duhun jahilci" dariya suka fashe da shi d'ayar da ta fara magana tace "ai ko yanzu ma sis Diyanah kada ki fitar da tsammanin kamosu aka yi aka dawo da su,basu yi niyyar zuwa ba" wacce aka kira Diyanah ta fashe da wani dariya tana rik'e ciki tace "kina nufin dai sun zama *TAKARI* kenan?" Dariya suka sake sakawa suka tafa,Ameerah dake kallonsu ranta ya mugun b'aci da maganganunsu tace "haba guys wannan ai ba yi bane,me yasa za kuna fad'an irin maganganun nan?" Diyanah tana mata wani kallo a tsiwace tace "an fad'a d'in ko akwai abunda za kiiya yi?" Ameerah ta girgiza kai tace "babu abunda zanyi but zan fad'awa Abba muddin baku daina ba" Manar dai sai cika take kamar za ta fashe ta kasa magana tsabar yadda taji maganar ya daki zuciyarta sai hawaye take ta k'ok'arin mayarwa,d'ayar budurwar ta watsoma Ameerah wani mugun kallo tace "ai dama dole ki tare mata,tunda an tab'a k'anwar uwarki.." Saurin dakatar da ita ameerah tayi "A'a Deejah kada mu kai nan,duk abunda za ku fad'a ya tsaya iya kanmu,amma kada ki kuskura ki k'ara saka iyayen mu" a tsiwace Deejah tace "idan an tab'a me za ki iya yi?" Ameerah tace "sai kin gwada zan nuna miki abunda zanyi" dariya suka sa su biyun Diyanah dake jifansu da mugun kallo tace "kin ji fa sis kamar za ta iya mana wani abu,duk fa kwad'ayi ne yasa ta shiga maganar ma" Deejah tace "ke rabu da su kwad'iyi ai mabud'in wahala,idan ma za ku hak'ura da abunda kuke da shi ku zauna ku rungumi rayuwarku zai fi muku,amma kuna biyewa waccan tsohuwar tana d'ora ku turba mara kyau,duk sai kun yi dana sani a lokacin da bazai muku amfani b.." Bata k'arasa fad'an abunda yazo bakinta ba Manar da zuciya ta zo mata iya wuya ta cakumota a masife tace "wa kike kira waccan tsohuwar?" Diyanah tana k'ok'arin matsowa ta rik'e Manar da suka fara kokawa da Deejah Ameerah ta tareta da sauri tace "dakata malama baza ku mata taron dangi ba ehee,itama tana da wanda za su shigar mata" wani kallo Diyanah ta watsa mata tace "matsa kafin na bigeki" Ameerah ta fashe da dariya tace "wa za ki bige? Ai sai dai mu buge juna" Diyanah tace "dallah malama matsa!" Da karfi ta tura Ameerah saura k'iris ta fad'i tayi sauri ta rik'e pillar,ranta a mugun b'ace tana d'agowa ta fizgo Diyanah,a fusace Diyanah ta kaiwa ameerah mari tayi sauri ta goce bata sameta ba,kafin ta sauke hannunta k'asa Ameerah ta kai mata nata marin ji kake tass,gaba d'aya suka tsaya kamar wad'anda aka dannama pause har su Manar da suke kokawa,a fusace Diyanah ta k'unduma zagi "kan uba! Ni kika mara?" Ameerah tace "an mareki d'in ko an fad'a miki tsoronki ake ji?" Gadan² Diyanah tayi kanta za ta cakumota,Deejah ma ta yo kanta ita mai y'ar uwa za su mata taron dangi,Manar ta fizgota tana haki tace "ina za ki ai bamu gama ba" tana fad'a tana kai mata duka,nan kokawa ya kacame tsakaninsu,Deejah da Diyanah sai zage² suke su kuma su Manar sai jibgarsu suke suna haki. Cikin shirin tafiya masjeed Waleed ya bud'e k'ofar zai fito,kokawan da yaga suna yi yasa shi tsayawa ya zuba musu ido yak'i cewa komai,babu wanda ta kula da tsaiwarsa sai nishi suke suna dukan juna,can da yaga abun nasu ba mai k'arewa bane ya musu tsawa,gaba d'aya suka saki juna kowacce ta koma gefe suna mayar da numfashi,ya dunga binsu da mugun kallo kafin yace "ku mahaukatan ina ne daga dawowarku za ku fara ma mutane dambe a gida? Filin wrestling kuka samu?" Kawunansu Deejah a k'asa suka fara bashi hak'uri,wani tsawa ya watsa musu yace "be quite! Did i insist anyone to talk?" Manar ta tab'e baki ta d'auke kai,Waleed dake kallonsu fuskarsa babu wadataccen fara'a yace "i just gave u an hour kuje duk abunda za kuyi ku gama before,idan na dawo ban tarar da ku a nan ba jikinku duk sai ya gaya muku.." Yana fad'a ya wuce zai bar gurin,da sauri Manar ta juya za ta taci itama,Ameerah tayi saurin rik'o hannunta tace "don't go Sis! Allah Yaya zai miki babu dad'i" fizge hnnunta tayi tace "ku dai da kuke jin tsoro sai ku tsaya" wani juyowa yayi ya kalleta ba tare da ya ce mata k'ala ba ya gyad'a kai ya wuce parking space,Ameerah ta sake rik'ota tace "kinga kallon da ya mana ko? Let's go" Deejah da ba da ita Ameerah take ba a fusace tace "ke ma ki rabu da ita taje mana idan tana ganin zai kyaleta" wani kallo Manar ta mata tace "hala dukan da na