← Book details Manar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 184

Sashe 93

Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da Azaan ta fara had'uwa a wajen apartment d'insu kafin ta k'arasa gidan Dadda,yana mata magana ko saurarensa bata tsaya yi ba ta shige tana kuka,ya bita da kallon mamaki har ta shige,then ya wuce yana sakin wani murmushi,tana shiga d'aki ta fad'a gado tana kuka,har Ameerah ta shigo bata sani ba sai da ta dafa ta a rikice take tambayarta "sis what happened?" Cikin kuka Manar ta d'ago idanunta da suka yi ja tace "Yaya ne" Ameeah tace "me ya had'a ku?" Tana share hawaye ta mata bayanin abunda Waleed yace mata,Ameerah ta sauke ajiyar zuciya tace "to ke mene ne yasa ki damuwa tunda ba kya sonsa?" Wani kukan ta fashe da shi tace "ai baza ki gane ba" Ameerah tace "mene bazan gane ba?" Ta mata banza bata k'ara kulata ba can ta d'auki wayarta ta dunga kiransa amma bai picking ba,dole ta hak'ura ta ajiye wayar tana sauke ajiyar zuciya. Washe gari da rana ta shiga part d'insu har lokacin she's not moody,ta tarar da mother tana jera abinci a kan rug,ta k'arasa ta gaisar da ita tana k'irk'irar murmushi,mother ta kalleta tace "ga abincinku nan ke da Daddy" ta k'arasa ta zauna kan carpet d'in tana bud'e warmers d'in tayi d'an murmushi,Daddy ya fito daga d'aki ya k'araso cikin parlon ya zauna saman lallausan carpet d'in shima yana kallonta yace "sweetheart!" Dariya tayi tace "Daddy good afternoon" yace "afternoon dear,how are u?" Tace "alhamdulillah!" Daddy yana kallonta yace "I'm proud of u sweetheart! Keep it up dear" tace "thank u Daddy,but ni ba ku bani gift ba,duka gidan nan Yaya kad'ai ne ya bani" murmushi yayi yace "let lunch first" ta d'auki plate ta zuba musu mother tana zaune a parlon har suka gama cin abincin,Daddy ya kalleta yace "hope u will also pass ur up coming exams!" Ta gyad'a kai tace "sure Daddy" Daddy yace "good sweetheart" d'an k'aramin box ya fito da shi daga pocket d'insa ya mik'a mata yana sakin murmushi yace "this is my gift" tayi dariya tana kallon mother tace "mother saura na ki" murmushi mother tayi tace "ki fara bud'a wannan muga abunda Daddy ya baki" ta mak'ale shoulder a shagwab'e tace "ni ki ba ni naki na had'a" mother tace "alright!" Ta shiga d'aki ta d'auko wani jaka mai kyau,Daddy yana kallonsu yana sakin murmushi,ta mik'a ma Manar jakar hannunta tace "my gift for u dear! Allah sa na tsoron Allah ne" tace "ameen!" Ta karb'a ta had'a su guri d'aya,tana sakin murmushi tace "Daddy ka ajiye min yanzu zan dawo" yace alright" ta fita da sauri ta nufi part d'in Dadda,jakar da Waleed ya ba ta jiya ta d'auko ta taho part d'in,tayi sallama ta shiga,Daddy yace "me kika samo mana?" Tayi dariya tace "kyautan da Yaya ya bani ne jiya" ta zauna jikin Daddy ta fara d'auko na Mother tana sakin murmushi ta bud'e ta d'auko madaidaicin Qur'an mai kyau sai littataffai k'ananu biyu,d'aya Azkhar ne,d'ayan kuma Addu'a'u min-kitaab was-sunnah,Manar tayi murmushi tana kallon Qur'an d'in tace "wow! Thank u Mother,i love it and i love u too" mother ta dunga kallonta ganin yanda tayi murna da gift d'in tayi murmushi itama tace "really?" Tace "sure mother" d'an k'aramin box da Daddy ya bata ta d'auka tana cewa "saura na Daddy bari muga" ta bud'e box d'in key ya fad'o,ta bisa da kallo ta kai hannu ta d'auka,so excited tace "Daddy!" Tana d'aga key d'in motar da ta d'auko tana kallo tace "u brought me a car Daddy?" Mother sai kallonsu take cike da jin dad'i,Manar ta rungume Daddy tace "i love u Daddy,Allah ya k'ara girma" murmushi yayi yace "Ameen,za a kawo motar da yamma" Manar da ta rasa me za ta ce saboda murna tace "toh Daddy,Allah ya kai mu,thank u so much,Allah saka da alkhairi" yace "ameen" ta juya tana kallon mother dake sakin murmushi tace "mother kinga gift d'in Daddy na" mother ta gyad'a kai tace "yeah! Muna godiya yallab'ai Allah k'ara girma" Daddy dai bai ce musu komai ba sai murmushi yake,ta d'auki jakar gurin Waleed ta bud'e ta fito da manyan turaruka masu tsada da kwalin sabon waya k'iran iPhone 12,wani k'ara ta saki ta mik'awa mother key d'in da kwalin wayarta tsabar farin ciki ta rasa me za tayi kawai ta fara tattare warmers da plate d'in ta kai kitchen bata fito ba sai da ta wankesu,Daddy sai kallonta yake yana sakin murmushi mother ma tana mata dariya,Daddy ya tashi ya bar parlon yana cewa mother "yarinyar kin nan aka sake ba ta want gift d'in za ta iya tafiya zariya" daga haka ya shige bedroom d'insa,mother said dariya take musu. Da dare lokacin ta fito b'angaren Dadda suka had'u da waleed za shi gun Dadda,ta wara ido tace "Yaya baka tafi ba?" Ya kalleta bai ce komai ba and bai tsaya ba ya wuce,ta dunga kallonsa kamar za tayi kuka ta kasa tafiya,can dai ta bisa dai² lokacin ya gama yiwa Dadda sallama ta jiyo Dadda na fad'in "to kuma yanzu tsakani da Allah Mamman baza ka jira har ayi bikin Manar ba za kayi tafiya?" Wani murmushi yayi da ya tsaya iya lips d'insa cikin k'arfin hali yace "zan dawo kafin lokacin" ta washe baki tace "toh ko kai fa,ai hakan dai zai fi ayi bikin kana nan,sai ma ka kaita d'akinta kayi mata fad'a" saurin tashi yayi yana mata wani kallo ya nufi hanyar fita yace "sai da safe.." Tace "toh Allah ba mu alkhairi,sai na zo gidan mun k'ara yin sallama" bai tanka ta ba ya fita,Manar tana jinsu kafin su gama yin sallama tayi sauri ta tafi gurin motarsa ta tsaya tana share hawaye,ko minti uku ba'a yi ba ya fito tun daga nesa yake kallonta da mamaki bai ce mata komai ba ya k'arasa ya bud'e motarsa zai shiga kafin ya rufe ta rik'e murfin motar ta fad'a jikinsa ta saki kuka ta k'ank'amesa tightly,Waleed da ya ji gaba d'aya jijiyoyin jikinsa sun saki ya jingina da seat ya lumshe idanunsa and hold her closely to himself,a hankali ya kai hannunsa ya rufe motar jikinsa was vibrating lokacin ya daure muryarsa a sark'e yace "stop those tears Lilac" girgiza masa kai tayi ta d'ago idanunta da suka yi kaca² da hawaye tana masa wani kallo tace "ina za kaje ka barni?" Ya dunga kallonta idanunsa har sun fara k'ank'ancewa trying hard to control his feeling but he can't dole ya kai bakinsa yayi grabbing lips d'inta,abunda bai yi tunani ba da sauri ta tallafe backhead d'insa and give him all the support,suka lumshe idanunsu tare suna enjoying moment d'in,fuskar Waleed har wani murmushi yayi appear ya rik'eta sosai,almost ten minutes suka d'auka sune tsotse² kafin ya janye a hankali yana sauke wani heavy ajiyar zuciya,Manar ta k'ara fashewa da kuka tana lalubensa,ya bud'a idanunsa da kyar yana kallon fuskarta cike da dauriya ya d'ago fuskarta yace "what happened?" Kasa amsawa tayi ta kai lips d'inta kan nasa za tayi grabbing da sauri yasa index finger d'insa ya raba su,ta bud'e idanunta tana kallonsa,hawaye kwance cikin idanunsa yace "stop lilac" sheshshek'a ta fara yi,ya had'e rai yace "baza ki daina kukan ba?" Ta fara goge idonta,ya sa hannunsa yana share mata idanuwanta,yayi murmushi muryasa a can k'asa yace "i'm going to travel" kukan ta fara k'ok'arin ci gaba da yi,ya girgiza mata kansa yace "don't cry.. I'll be back as soon as possible" turo baki tayi,hakan da tayi sai ta basa dariya yayi kissing tip of her noise a hankali yace "za ki biyo Hjy kuzo gidana gobe?" Saurin kallonsa tayi,sai kuma ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba,yace "idan kun zo sai ki raka ni airport ko?" Mak'e kafad'a tayi tana turo baki,yace "baza ki zo ba?" Ta gyad'a masa kai,yace "why?" Fuskarta a d'aure tace "i just don't like ur wife" kasa cewa komai yayi yana kallonta,can a hankali yace "but it's also ur home,me kike tunani?" Tace "toh ai ita bata san haka ba,ko baka gaya mata matsayina bane?" Dariya sosai ta basa and he couldn't help it sai da yayi,ta tab'e baki tace "ni dai bazan zo ba,ba na sonta" ya sauke ajiyar zuciya yace "toh ni zan zo mu d'auke ku sai mu wuce ta nan,haka ya maki?" Ta gyad'a masa kai da sauri tace "toh! Umm kasan me Yaa Azaan ya bani gift?" Shiru yayi yana kallonta,lokaci d'aya mood d'insa ya canza,fuskarsa a d'aure bai ce komai ba ya bud'e motar ba tare da ya kalleta ba yace "jeki maza za muyi waya idan na je gida" tace "toh" fuskarta da murmushi ta sauka daga jikinsa,yayi ajiyar zuciya ya rufe motar,yana kallonta ta juya ta tafi b'angaren Dadda,then ya yima motar key ya bar gidan. Sanda ta k'arasa balcony tana sakin murmushi ta ga Azaan tsaye gurin yana waya sai kallonta yake,ta wara ido tace "lahh Yaya!" Ya dunga kallonta and he can't take off his eyes on her,ta tab'e baki tace "Yaya sai da safe" daga haka ta wuce da sauri tana murmushi ya bi ta da ido. Da safe tana gyaran d'akinta around 11am bayan ta gama shiryawa mother ta lek'o d'akin tana kallonta tace "Manar kin san dai ke Hjy take jira ko? Tun d'azun sai aike take,idan baza kiba dan Allah ki wuce ki sanar mata ta nemi wani ya rakata" dariya Manar ta fara yi tace "yanzu fa zan fito" mother ta fita daga d'akin,Manar ta gama ta bi bayanta,dai² lokacin Dadda ta shigo parlon tana kallon Manar dake saka hijab fuskarta a d'aure ta k'i kallonta ta tab'e baki tace "ke dai wallahi baki da kirki,tun jiya ince maki zamu je ki raka ni gidan Mamman amma dan walak'anci ki bari inta maki aike tun safe sai da kika bari rana ya game gari kin zaunar da ni ina ta jiran ki.." Manar tace "toh! Ki jira na karya mu tafi,ni bazan biki ban ci abinci ba,ke sai ki sa mu dunga zuwa gidan mutane ko tashi basu yi ba ana walak'anta mu" Dadda ta zaro ido tace "yanzun kuma jiranki zanyi fisabilillahi,kin ma kanki da ni adalci kenan?" Manar dai bata tanka ta ba ta wuce kitchen ta had'o breakfast d'inta ta zauna dining sai da ta k'oshi sannan ta
Chapter 93 · 0% Book details