Sashe 90
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
musu abunda ya faru,Nusy ta zaro idanu tana kallonta tace "really?" Ta gyad'a mata kai,dariya Ameerah ta fara tana k'unshe baki,Manar ta zuba mata ido cike da jin haushi tace "ni wallahi shi sa ba na son fad'a miki abu,sai ki kama yiwa mutum dariya" Ameerah ta tsagaita tana kallonsu tace "didn't i told u Yaya yana sonki kika ce ba haka ba? Idan babu k'ira mai zai ci gawayi dama?" Manar ta had'e rai tace "ni fa ba sona yake ba" Ameerah tace "really?" Ta gyad'a mata kai,Ameerah tayi shiru bata sake cewa komai ba,ta san Manar da kafiya akan abu,Nusy tayi wani murmushi cike da zolaya tace "friend! How do u feel the test of his salivas?" Kallonsu Manar ta dunga yi kawai ta fashe da kuka,da gudu ta bar gurin,Ameerah da Nusy suka kwashe da dariya,Ameerah tace "kyaleta gulma ce fa,wallahi itama ta san Yaya yana sonta,if not me zaisa shi sakar mata fuska? Duk fa gidan ita kad'ai yakewa wasa,ita kad'ai take ganin dariyarsa.." Nusy ta gyad'a kai tace "i can see.. Jiya kawai na gansa amma nima na yarda dake,Yaah Waleed na sonta fiye da tunani" har suka fito get basu daina maganar ba,tsaye suka ganta tana goge hawaye da yake har sannan driver bai k'araso ba,suka k'arasa gurinta suna kallonta,d'auke kai tayi kamar bata gansu ba,Nusy tace "friend ki fad'a min mana" wani kallo Manar ta mata tace "kije kice ma Yaa Abdoul ya miki sai kiji ko me na ji" ta k'are maganar tana murgud'a musu baki,suka dunga dariya duka sun mayar da abun wasa,suna tsayen driver ya tsaya kusa da inda suke,ta wuce ta bar su tsaye suna mata dariya,sanda suka shigo gida motar Daddy da ta gani a parking space yasa ta fitowa motar da sauri ta wuce part d'insu har ranta ta jin dad'i,da ta shiga bata samesa ba lokacin sun wuce masjeed,ta cire kayanta ta d'aura towel ta shige bathroom,haka kawai tun da ta kwab'e ta shiga tube take jin kamar hannun Waleed yana tab'ata,ta lumshe idanunta ta kai hannunta kan breast d'inta,taji babu komai a gurin tayi ajiyar zuciya,bayan ta gama wanka ta fito ta wuce ta bud'e press d'inta ta ciro wayarta,missed calls d'in Azaan ta gani har uku da text,bata tsaya dubawa ba ta ajiye ta gama shiryawa sannan ta fito parlor,taga Daddy a zaune tana sakin murmushi ta k'arasa ta zauna jikinsa ta gaida shi,Daddy ya kalleta yana shafa kanta yace "Mamana are u okay?" Ta wara idanunta tana sakin murmushi tace "sure Daddy,ya hanya?" Yace "Alhamdulillah,ya shirin grad?" Tayi y'ar dariya tace "Daddy ai mun gama komai" mother dake jera ma Daddy abinci a k'asan kan rug sai hararanta take,Daddy yace "u should tell me abunda kike so na siya miki as gift d'inki na grad" cike da jin dad'i tace "toh Daddy" tare suka ci abinci da Daddy bayan sun gama suka zauna suna hira,Waleed ya shigo ya samesu,tun da ya shigo idanunsa suke kan Manar,har ya zauna ta kallesa tana sakin murmushi tace "Yaya ina wuni?" Yayi ajiyar zuciya yace "lafiya lao,ya shirye²?" Tace "alhamdulillah" ya gyad'a kai suka gaisa da Daddy da mother,Daddy na kallonsa yace "ya iyali?" Waleed ya shafa kansa yace "alhamdulillah uncle" Daddy yace "maa sha Allah,how about work?" Ya amsa yana satar kallon Manar,wani kallo ta masa ta d'auke kanta,bata k'ara magana ba har Waleed suka fita da Daddy. Da yamma ta fita b'angaren Dadda,tayi sallama ta shiga parlon,Daddy ne zaune parlon sai Waleed,gefe kuma Amaar da Azaan suna hira tana ganin haka bata tsaya ba ta wuce d'aki tayi kwanciyarta kan gado,Waleed ya bita da kallo da yaga bata tsaya ba a parlon yayi wani ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa..