Sashe 73
Manar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
'Dauke kanta tayi fuskarta a d'aure tace "ni dai ba za ni ba" yayi saurin kallonta yace "why?" Tana b'ata rai tace "haka kawai" yace "ban yarda ba" tace "ni fa ba na son ganinta ne that's why bazan je ba" wani kallo ya mata yace "what's ur problem?" Tace "Yaya i just told u ba na sonta,amma shi ne kaje ka aureta" kallonta ya dunga yi yace "are u jealous?" Ta girgiza masa Kai fuskarta a d'aure,yayi k'asa da muryarsa kamar mai rad'a yace "idan ba kishi na kike yi ba me kike?" Tace "ni dai ba na yin komai" wani murmushi yayi yace "alright! Ina gidan za kuje?" Ta fara girgiza masa kai,ya d'aure fuskarsa yace "wai mene ne natsalarki ne?" Kamar za tayi kuka tace "Yaya ni wallahi ba na son matarka" ya zaro ido yana kallonta,yace "to kuma gurinta za kije?" Tace "to ba itace matar gidan ba kuma ai za mu ganta" ya girgiza mata kansa yace "gurina za kije fa" tace "ni dai Yaya.." kafin ta kai k'arshe yace "alright! Baza kije ba ko?" Ta gyad'a masa kai yace "fine.. yanzu na fahimci abunda kike nufi,ba itace ba kya so ba kawai har da ni" muryarta yana cracking tace "Yaya.." ya d'aga mata hannu yace "babu wani Yaya da za kice,ai na gane abunda kika kasa fitowa ki fad'a,na gode.." kuka ta fashe da shi tana kallonsa tace "ni yaushe nace maka haka?" Yace "ko da baki ce ba ai abunda yake k'asan zuciyarki kenan" tace "ni wallahi ban ce maka ba" ya tab'e baki yace "ke kika sani.. Dama ni da kika ce ba kya so me zai kaiki gida na ko?" Ta dunga kallonsa hawaye cike a idanunta tace "shi kenan zan je" yace "no! K'i barshi kawai,ba sai kin je ba,saboda kada kiga wanda ba kya so.. babu damuwa kin ji" yana gama fad'a ya tashi yayi hanyar fita ta d'aga kanta ta bisa da kallo tace "Yaya." Yak'i tsayawa ya fice yana mata dariya. Washe gari da safe Dadda ta riga su shiryawa,ta shiga ta gansu kwance,ta kame baki tace "to ku kuma har yanzu baku farko ba,fisabilillahi sai rana ya kai tsakiyar duniya tukun za ku tashi mu tafi?" Ameerah ta bud'a idanunta tace "haba dan Allah Hjy ki bari har gari ya waye mana" cikin fad'a Dadda tace "wane gari kuma ake jira ya waye? Banda wannan? Ku dai kuna nan kuna ta baccin asara za kice na bari har gari ya waye" tana mitar nata ta fita,Ameerah ta tashi ta d'auki hijab d'inta tasa sai cika tace ta fice,Dadda dake parlor tace "iiiihhhh! Guduwa za ki yi?" Ameerah da ta fita balcony ta d'aga murya tace "ni wallahi bazanje ba,kuyi tafiyarku dama" Dadda ta tab'e baki cikin jin haushi tace "dama ni ban yi niyyar zuwa dake ba tun farko ban san wa ya gayyatomin ke ba,je ki dai Allah raka taki gona.." ameerah ta ji haushi tayi k'wafa ta wuce bata tsaya ba,Manar dake kwance tana jiyosu tayi tsaki ta sake juyawa,a k'alla sai da Dadda ta sake shigowa kusan uku kafin ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta shirya sai cika take,ta d'auki hijab tasa ta fita parlon,zaune taga Dadda ta rafka tagumi fuskarta kamar za tayi kuka,ta d'auke kanta tace "zanje na karya a gida sai mu tafi" da sauri Dadda ta tashi ta d'auki mayafinta ta yafa tace "iiiihhhh! Kuma zama kike so nayi jiranki? Gaskiya ba na iyawa muje can kya ci ai gidan Yayanki ne,matar tasa ba sai ta dafa maki duk abunda kika ce kina so ba" Manar ta kalleta d sauri tace "a can kuma zan ci?" tace "iiiihhhh! Gidan Mamman d'in ba'a cin abinci ne? Muje kin ji kada rana ya k'ara yi,gara muje yanzu ba muje musu da wannan ranar fatsar² ba" ta wuce gaba tana mita Manar ta bita a baya tana b'ata rai. Sanda suka sauka mota a bakin get driver ya tsaya Dadda ta fita tana kallon gidan,ta kalli Manar tana washe baki tace "nan shi ne gidan Mamman din?" Manar dake jin haushi tace "ni to ya za'ayi na sani" Dadda ta kalleta,ganin yadda fuskarta yake d'aure tace "to ko dai haushi na kike ji na hana ki tsaiwa kici abinci?" Manar tace "a'a" Dadda tace "iiiihhh! Me aka maki to?" Tace "babu komai" Dadda tace "babu komai kike b'ata rai?" Ta mata shiru bata amsa ba ta wuce gaban get d'in tayi knocking,get keeper ya bud'e yana kallonta yace "wa kike nema?" Ta d'aure fuska tace "gurin me gidan muka zo" a masife Dadda data tsaya baya ta lek'o tana kallonsa tace "Kai d'an nan gurin jika na muka zo,maza ka bud'e mana mu shiga" get keeper sai kallon Dadda yake ya k'i bud'e musu,Dadda dake jiran yace su shiga taga ba shi da niyyar bud'e musu,rai b'ace tace ma Manar "ke ina salularki?" Manar tace "na barta a gida" Dadda ta saki baki tana kallonta kamar za tayi kuka tace "yanzu fisabilillahi idan ba dama kin so a walak'anta mu ba,yaushe za ki bar wayar a gida?" Manar dai ta k'i kulata,cikin sanyin jiki da ba murya Dadda ta kalli mai gadin tace "yanzu kai d'an nan da gaske baza ka bud'e mana mu shiga ba?" Yace "baba ba nan gidan bane kuje gaba" Dadda ta bud'e baki tana kallonsa,cike da jin haushinsa tace "kai allan musuru ne da ka san ba nan muka zo ba?" Yace "ba shi bane,amma bazan bari ku shiga ba" Dadda ta ji haushi sosai tace "kada Allah yasa ka bari mu shiga d'in,idan ka barmu mun taka ciki ba ka k'aunar Allah da manzonsa" yace "sai dai ki fad'i koma mene,amma bazan bud'e muku ba" k'wafa tayi mai ciwo ta koma gefe tana mita,Manar dake kallonta ta ciro wayarta daga jaka ta fara kiran Waleed,bugu d'aya ya d'auka yace "what?" Ranta a bace tace "ga mu bakin get ka fito" yace "baza ku shigo ba?" Tace "to ba get keeper d'in ya hana mu ba" da sauri Waleed ya sauka d'aga kujeran da ya kwanta tun asuba da ya dawo daga masjeed yace "alright! I'm coming" ya katse kiran,a nutse yake tafiya ya bud'e get ya fito,Dadda sai mita take ma Manar tana fad'in "amma wallahi sai Allah ya saka min tsaiwan da kika ja min a rana,haka kawai dan k'aryan bala'i kice kin bar salular a gida.." Tana ganin Waleed ya fito ta nufesa kamar za tayi kuka tace "gaskiya Mamman ka yiwa Manar nasiha,wannan dai ba halin kwarai bane ta daddage tayi k'arya alhalin ta san ba haka bane.." Waleed dake kallon Manar tun fitowarsa yace "ku zo muje" suka bisa,Dadda ta waiga ta galla ma get keeper kallo tace "d'an bak'in ciki sai dai ya mutu,ko yanzu ma za ka hana mu shigar ne?" Murmushi yayi bai ce komai ba ya koma kan bench ya zauna,Dadda suka shiga gidan tana ma Waleed mitar "gaskiya Mamman wannan mutumi baida kirki ko d'is.." Waleed dake gaba yace "me ya maki?" Tace "shi haka ake yi sai yace mutane baza su shiga gidan ba.. To ko dai baka fad'a masa muna zuwa ba?" Yace "nace masa me?" Tace "kai kuwa ai da sai ka ce masa kakarka da k'anwarka suna zuwa ya bud'e musu k'ofa" yayi murmushi suna zuwa balcony Dadda har lokacin tana masa mita,ya bud'e musu k'ofar suka shiga parlon,Dadda ta washe baki tana kallon lafiyayyun leather chairs d'in parlon,Manar tana biye da ita,da k'arfi bayan ta gama shiga tace "salamu alaikum" da taji shiru ta sake maimaitawa,wani kallo Manar tayi mata cikin jin haushi tace "kai Hjy kiyi a hankali mana.." Matsawa Dadda tayi ta bud'e baki tana kallonta,Manar ta turo baki ta d'auke kanta tace "kawai sai kiyi ta maimaitawa da k'arfi kamar ba safiya ba kuma ce miki aka yi ba'a ji ba?" Dadda za ta yi magana Waleed dake bayansu ya yima Manar wani kallo yace "kyaleta Hjy kada ki kulata" Dadda ta washe baki tana kallonsa tace "ai dama ko baka fad'a ba bazan kulata ba,yo ce mata aka yi nima irinta ce?" Kallonsu kawai Manar tayi fuskarta a d'aure,can ta juya a hankali,kallonta taga Waleed yana yi,ta sunkuyar da kai tace "ina kwana Yaya?" Kafin ya amsa suka ji muryar Dadda tace "ina amaryar taka kuma Mamman?" Waleed ya juya ya kalleta yace "tana sama" zaunawa suka yi Waleed yana kallon Dadda yace "ina kwana?" Ta washe baki tace "Lafiya lao Mamman tun asuba da na tashi nayi wanka wallahi,banda su da suka b'ata min lokaci da tun gari bai gama wayewa ba za ku ganmu" shafa beard d'insa yayi yana sakin lallausan murmushinsa,Dadda tana kallon pillow da aka ajiye kan lallausan sabon rug d'in parlon tace "wai ita amaryar taka baza ta sakko ba ne kuma Mamman?" Waleed yace "tana sama fa think bata tashi ba.." Yana fad'in haka ya tashi ya wuce sama,Dadda ta k'ara kallon pillow dake parlon murya can k'asa tace "Manar waye kuma ya kwana a parlor?" Manar tayi murmushi tace "kai Hjy me ya ruwan ki kuma?" Dadda ta tab'e baki tace "iiiihhh! Ba ruwana kuwa" ta rik'e bakinta tana sake k'arema parlon kallo,can ta cire mayafinta ta nad'e tana kallon ko ina tana murmushi tace "sabon gida ba dai kyau ba" ta mik'e ta nufi wani k'ofa ta bud'e tana lek'a ciki ta k'arasa shiga sai kalle² take yi kafin ta fito ta rufe tace "to shi kuma Mamman duk shi ya zuba lafiyayyun kayan nan ko iyayen zabiyar ne suka mata?" Ta tab'e baki ta tafi ta bud'e kofar kitchen tana lek'en ciki ta zaro ido tace "Waiii.. Ai kitchen d'in ma ba masaka tsinke,shak'e yake shima da kaya,ashe dai ba gwalagwalan k'arya aka dunga fantamawa da shi ranan bikin ba" Manar dai ta had'e rai sai kallonta take ta k'i ce mata komai,Waleed yana haurawa sama ya bud'e d'akin Afiyah,bacci ya sameta tana yi ta you d'ai² a gadon,ya shiga ya kulle k'ofar ya k'arasa kan gadon ya d'an bugi pillow d'in yana kallonta,sai da ya sake bugawa da k'arfi for the second time sannan ta bud'e ido,tana ganinsa tayi sauri ta mik'e zaune tana kallonsa da wani expression,yace "kin ma yi sallah kuwa?" D'auke